Dangote zai sayar da kaso 10 na hannun jarin matatar man shi
Published: 23rd, October 2025 GMT
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ce matatar man shi na shirin sayar da tsakanin kashi 5 zuwa 10 cikin 100 na hannun jarinta a kasuwar hannun jari ta Najeriya.
Ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da S&P Global, inda ya ce ana sa ran sayar da hannun jarin a cikin shekara mai zuwa.
Dangote ya ce wannan mataki kwatankwacin irin yadda aka gudanar sayar da hannun jarin kamfanononin siminta da suga na Dangote ne.
“Ba ma son mu riƙe fiye da kashi 65 zuwa 70 cikin 100,” in ji Dangote.
Ya ƙara da cewa za a sayar da hannun jarin a hankali, gwargwadon sha’awar masu zuba jari da ƙarfin kasuwa.
Ƙwararren ɗan kasuwar ya ce kamfanin na duba yiwuwar haɗin gwiwa da kamfanonin Gabas ta Tsakiya domin tallafa wa faɗaɗa matatar da kuma haɓaka sabon aikin sinadarai a ƙasar China.
“Tsarin kasuwancinmu zai canza. Yanzu maimakon Dangote ya mallaki kaso 100, za mu samu abokan haɗin gwiwa,” in ji shi.
Dangote ya ce Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC) Limited na iya ƙara hannun jarinsa a matatar bayan rage shi zuwa kashi 7.2%, amma ba sai an kammala matakin ci gaban aikin gaba ba.
“Ina son in nuna abin da wannan matata za ta iya yi, sannan mu zauna mu tattauna,” in ji shugaban kamfanin.
Haka kuma, attajirin y ace matatar ta sanar da shirin ƙara yawan man fetur din da take tacewa zuwa ganga miliyan 1.4 a rana, wanda zai zarce mafi girman matatar man a duniya da ke Jamnagar, India, wadda ke samar da ganga miliyan 1.36 a rana.
“A watan Yuli, Dangote ya bayyana shirin faɗaɗa matatar daga ganga 650,000 a rana zuwa 700,000 kafin ƙarshen shekara,” in ji S&P Global.
“Yanzu, burin shi ne a kai ganga miliyan 1.4 a rana, ba tare da ranar da aka ƙayyade ba, wanda zai zarce matatar Jamnagar da ke India.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: hannun jari Matatar mai hannun jarin
এছাড়াও পড়ুন: