Sanarwar Bayan Taron Jks: Mene Ne Sirrin Kwarin Gwiwar Kasar Sin?
Published: 23rd, October 2025 GMT
A cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan, sakamakon matakan takunkumi da kasar Amurka ta dauka kan kamfanonin fasahohin zamani na kasar Sin, kasar Sin ta kara saurin yin kirkire-kirkire a matsayin mai zaman kanta, wanda ya haifar da karuwar sabbin nasarori a fannonin da suka hada da fasahohin kere-kere, da na’urar mutum-mutumi, har ma ta zarce sauran kasashe a wasu muhimman fasahohin zamani.
Sa’an nan, dangane da takunkumin da wasu kasashen yammacin duniya suka kakaba mata, kasar Sin ta yi kokarin inganta karfin jure wahalhalu da tabbatar da kiyaye bangaren masana’antu da samar da kayayyaki, tare da rage tasirin matsalolin da kan taso daga waje yadda ya kamata. Wadannan ingantattun hanyoyin mayar da martani ga matsin lamba daga ketare sun nuna cikakkiyar juriyar tattalin arzikin kasar Sin.
Bisa wannan kwarin gwiwa, kasar Sin ta shirya wajen fuskantar kowane irin kalubale, da kiyaye saurin bunkasar tattalin arziki da kwanciyar hankalin zaman al’umma a cikin dogon lokaci, da kuma sa kaimi ga aikinta na zamanantar da al’umma. (Bello Wang)
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Trump Ya Dakatar Da Tattaunawar Kasuwanci Da Kasar Canada
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da kawi karshen tattaunawa da kasar Canada dangane da batun kasuwanci
Shugabann a kasar Amurka ya zargi Canada da yin amfani da kalmomin tsohon shugaban kasar Amurka Ronald Regan ta hanayar da ba ta dace ba a cikin wasu tallace-tallace akan kudaden fito, inda ya bayyana cewa; ” Saboda la’akari da halayyarsu an kawo karshen tattaunawar kasuwanci da kasar Canada.”
Shugaban kasar na Amurka ya ci gaba da cewa; Cibiyar Ronald Ragan ta sanar da cea, Canada ta murguda zancen Regan yana Magana akan illolin kudin fito, kuma an yi hakan ne domin yin tasiri a cikin matakin da kotun koli ta Amurka za ta dauka akan batun da ake jiran ta fitar da hukunci nan gaba.
Cibiyar ta Regan ta wallafa sako a shafinta na X cewa; hukumar yankin Ontario a kasar Canada ta yanko maganar tsohon shugaban kasar ta Amurka da ya yi a watan Aprilu a 1987, don haka tana tunanin matakan da za ta dauka akan haka ta fuskar shari’a.
A can kasar ta Canada hukumar yankin Ontario ta sanar da cewa, maganar Regan da ta watsa ta jawo hankalin Donald Trump.
Firimiyan gundumar ta Ontario a Canada Dodge Ford ya ce; Na tabbata Trump ba zai ji dadin wannan sanarwar da mu ka wats aba.
Tun da fari, Fira ministan kasar ta Canada Mark Joseph Carney ya fada wa manema labaru cewa; Ba za mu bar Amurka ta cimma manufarta wacce babu adalci a ciki ba dangane da batun kasuwanci.”
Kasar ta Canada dai tana takaddama da Amurka akan batun kara kudaden fito da Trump yake yi kasashe abokan kasuwanci.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gaza Tasirin Rashin Abinci Mai Gina Jiki Da Magani Zai Ci Gaba Akan Yara Da Matan Har Zuriya Mai Zuwa October 24, 2025 Iran Ta Lashe Kambun Duniya Na Kokawar Gargajiya October 24, 2025 Pezeshkian: Iran za ta gwammace takunkumi a kan mika wuya October 24, 2025 Trump: Amurka na shirin kai hare-hare a Venezuela October 24, 2025 Ivory Coast: Ayyukan ma’adinai na fuskantar tsaiko yayin da Ouattara ke neman wa’adi na 4 October 24, 2025 Dangote zai sayar da kaso 10 na hannun jarin matatar man shi October 24, 2025 Larabawan Yankin Tekun Fasha Sun Caccaki Sabon Shirin Isra’ila A Kan Yammacin Kogin Jordan October 24, 2025 Albanese: Wajibi Ne A Kawo Karshen Gwamnatin Mamaya A Falasdinu October 23, 2025 Rasha: Shugaba Putin Ya Duba Atisayen Rundunar Nukiliyar Kasar October 23, 2025 Shugaban Amurka Ya Soke Shirin Ganawa Da Takwaransa Na Rasha October 23, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci