2025-06-15@23:30:28 GMT
إجمالي نتائج البحث: 41
«Sanarwar ta»:
A cewarsa, dukkanin takardar neman kirkirar sabon masarauta ko sarki ko gunduma dole ne a aike zuwa addireshin gwamnan jihar ta hannun babbar sakatariyar ma’aikatar kananan hukumomi da kula da masarautu na jihar. Kazalika, ya ce dole ne masu nema su gabatar da takaitaccen tarihin al’ummar da suke nema wa masarauta ko sarki ko gudunmawa tare da tarihin masarautar ko sarki ko gundumar da ke yankin da suke neman fita daga ciki. Sanarwar ta kuma nemi a sanya dukkanin wani muhimmin bayanin da aka san zai iya taimakawa wajen la’akari da bukatar masu nema. Har ila yau, sanarwar ta ce dole ne a takardar neman a samu sahihin sanya hannun hakimi, sarakunam kauye, da shugabannin al’umma tare da tabbacin wannan...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta ce mayar da martani ga gwamnatin Isra’ila hakki ne na shari’a ga Iran kamar yadda doka ta 51 ta kundin tsarin mulkin MDD ta tanada. Da farko dai ma’aikatar ta mika ta’aziyyar shahadar wasu kwamandoji da jami’an kasar Iran a harin da Isra’ila ta kai wa kasar. “Hare-haren da gwamnatin sahyoniyawan ta kai wa Iran sun sabawa doka ta 4 sakin layi na 2 na kundin tsarin mulkin majalisar dinkin duniya a matsayin wani mataki na wuce gona da iri kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kuma Iran tana da hakki na shari’a na halal ta mayar da martani kan wannan zalunci kamar yadda yake a cikin sashe na 51 na kundin tsarin mulkin majalisar...
Iran ta yi Allah-wadai da wani kuduri da ta danganta da na siyasa da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ta dauka, tana mai cewa ba shi da tushe na fasaha ko doka. Hukumar kula da makamashin nukiliya ta Iran (AEOI) da ma’aikatar harkokin wajen kasar sun fitar da sanarwar hadin gwiwa yau Alhamis bayan da majalisar gwamnonin hukumar ta IAEA suka amince da wani kuduri da ke zargin Iran da rashin cika alkawuran da ta dauka na nukiliya. Kuri’u 19 ne suka amince da kudurin wanda Amurka da Birtaniya da Faransa da Jamus suka tsara. Kasashen Rasha, China da Burkina Faso sun kada kuri’ar kin amincewa da shi, Yayin da kasashen Afirka ta Kudu, Indiya, Pakistan, Masar,...
Bayan kammala aikin Hajjin bana, Saudiyya za ta fara bayar da bizar umara daga gobe Laraba. Kazalika mahukuntan ƙasar sun ce dakatarwar shiga birnin Makkah ba tare da takardar izini ba zai ƙare daga ranar Larabar 11 ga watan Yunin 2025. Dalilin da Nijeriya ke fuskantar tsaiko wajen karɓar rancen $5bn daga Saudiyya Gwamnan Kebbi ya bai wa ’yan kasuwar katako tallafin ibtila’in gobara Ma’aikatar Hajji da Umarah ta Saudiyya ta ce za ta fara karɓar sabbin baƙi masu shigar ƙasar da bizar Umarah daga gobe Laraba, 11 ga watan Yuni. Sanarwar na zuwa bayan kammala aikin Hajjin bana wanda kimanin mutum miliyan 1.6 daga faɗin duniya suka halarta. Saudiyya takan dakatar da bayar da bizar umara makonni gabanin aikin...
Kasar Sin ta yi nasarar harba sabon rukunin taurarin dan adam mai da’ira a kusa da doron kasa, daga cibiyar harba tauraron dan Adam ta Taiyuan dake lardin Shanxi na arewacin kasar Sin. An harba rukunin wanda shi ne irinsa na 4 da ya kunshi taurari masu samar da sadarwar intanet da misalin karfe 4:45 na sanyin safiyar yau Juma’a agogon Beijing, ta hanyar amfani da rokar Long March-6 da aka sakewa fasali. Kuma dukkan taurarin sun shiga da’irarsu cikin nasara. Wannan shi ne karo na 580 da aka yi amfani da dangin rokar Long March wajen gudanar da irin wannan aiki. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai...
Sanarwar bayan taron koli na hadin gwiwar Sin da kungiyar tarayyar kasashen kudu maso gabashin Asiya wato ASEAN, da kwamitin hadin gwiwar kasashen Larabawa na yankin Gulf wato GCC, ta jaddada burin sassan uku na bunkasa hadin gwiwar raya tattalin arziki, musamman ta hanyar gudanar da cinikayya marar shinge, da kammala yarjejeniyar gudanar da cinikayya cikin ’yanci tsakanin Sin da da GCC. Idan mun waiwayi wannan sanarwa ta hadin gwiwa, za ku gano manufofin da sassan uku ke fatan cimmawa, wadanda suka hada da fatan dunkule shiyyoyinsu waje guda, da kara yin tafiya tare, da neman samun ci gaba mai dorewa. Karkashin wadannan burika, sassan uku za su yi amfani da fifikonsu wajen cimma moriyar juna da karfafa kawance a...
A jiya Talata ne aka fitar da sanarwar hadin gwiwa ta taron kolin ASEAN-Sin-GCC karo na farko a birnin Kuala Lumpur fadar mulkin kasar Malaysia. Sanarwar ta ce bangarorin uku sun amince hulda, da mu’amalar al’adu, da kuma hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin kungiyar tarayyar kasashen kudu maso gabashin Asiya wato ASEAN, da Sin, da kuma kwamitin hadin gwiwar kasashen Larabawa na yankin Gulf wato GCC na da dogon tarihi, don aka ana fatan kara inganta dangantakar sassan uku karkashin jagorancin ka’idoji, da ra’ayoyi, da manufofi, da alkawuran da aka cimma matsaya daya kan su, ciki har da tsarin dokokin MDD. A cikin sanarwar, an kuma yabawa kasar Sin, bisa muhimmiyar gudummawa da take bayarwa wajen inganta zaman lafiya,...
Hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano ta dakatar da haska shirin Labarina, Dadin Kowa da wasu ƙarin fina-finan Hausa guda 20 a kafafen Internet ko gidajen talabijin. Hukumar ta ce ta ɗauki matakin ne a ƙoƙarinta na tabbatar da ana bin dokar tace fina-finai sau da ƙafa tare da ƙara dora masana’antar Kannywood a kan saiti. A cewar wata sanarwar da jami’in yaɗa labarai na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya fitar da daren Lahadi, fina-finan da dakatarwar ta shafa sun haɗa da Labarina, Dadin Kowa, Manyan Mata, Garwashi, Jamilun Jidda da kuma Gidan Sarauta. Sanarwar ta ce umarnin ya fito ne daga bakin shugaban hukumar, Abba El-Mustapha, bayan wani zamanta da kuma tattaunawar da ta gudanar. An kama ƙasurgumin ɗan...
Wata takardar bayani da aka wallafa a yau Lahadi 18 ga watan Mayun shekarar 2024, ta nuna cewa, jimillar kudin da aka samu a masana’antar harkokin sadarwar tauraron dan Adam na kasar Sin ta kai yuan biliyan 575.8, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 79.9, a shekarar 2024, adadin da ya karu da kaso 7.39 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara. Takardar game da bunkasar masana’antar harkokin sadarwar tauraron dan Adam ta kasar Sin, ta yi nuni da cewa, a karshen shekarar 2024, yawan adadin manhajojin fasahar sadarwar tauraron dan Adam a kasar Sin ya zarce 129,000, kuma an sanya wa kusan wayoyin salula miliyan 288 a kasar tsarin da suke iya amfani da sadarwar daga tsarin amfani da tauraron dan...
A yau Litinin, mai magana da yawun ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ya bayyana cewa, Sin da Amurka sun cimma matsaya tare da fitar da sanarwar hadin gwiwa bayan taron kolin tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu, inda ya kara da cewa, hakan wani muhimmin mataki ne da bangarorin biyu suka dauka na warware sabaninsu ta hanyar yin shawarwari da tuntuba bisa daidaito, tare da aza tubali da samar da yanayi na kara dinke baraka da zurfafa hadin gwiwa. Daga bangarenta kuwa, Darakta-Janar ta Hukumar Kasuwanci ta Duniya (WTO) Ngozi Okonjo-Iweala, a jiya Lahadi ta bayyana cewa, ta yi farin cikin ganin an samu sakamako mai kyau yayin taron kolin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka. A cikin...

Sanarwar Hadin Gwiwa Ta Bayan Taron Tattauna Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka
Kasar Sin za ta sauya matsaya kan adadin harajin fito da ta ayyana kan hajojin dake shiga kasar daga Amurka karkashin sanarwar sashen haraji na hukumar kwastam mai lambar 4 ta 2025, ta hanyar dage karin kaso 24 bisa dari a wa’adin farko na kwanaki 90, tare da wanzar da karin kaso 10 bisa dari kan kayayyakin, da jingine sauyin harajin fiton karkashin tanajin sashen haraji na hukumar kwastam mai lambar 5 na 2025, da sanarwar sashen haraji na hukumar kwastam mai lamba 6 na 2025. Kazalika Sin za ta aiwatar da dukkanin matakai na hukuma wajen dage sauran matakan ramuwar gayya da ba na karin haraji ba da ta ayyana kan Amurka tun daga ranar 2 ga watan Afirilun...
Kazalika, sanarwar ta sanar da cewa, ana bukatar kwamtin ya sanya ido wajen ganin an gabatar da kasidu da alkalan da za su yi hunci kan bayanan da za a tattauna a wajen taron da baje kolin kanana da matsakaitan sana’oi da za a yi a wajen taron tare da kuma mika kyaututtuka ga ‘yan kasuwar kasar da suka dace, a wajen taron. Acewar sanarwar, Mataimakin Shugaban Ma’aikata da ke a ofishin Mataimakin Shugaban kasa Sanata Ibrahim Hassan Hadejia ne, zai shugabaci kwamtin. Sauran ‘ya’yan kwamtin sun hada da, Ministar Ma’aikatar Kasuwanci da zuba hannun jari Dakta Jumoke Oduwole; Ministan sadarwa da kere-kere da kuma tattalin arziki na fasahar zamani Dakta Bosun Tijani; Ministar yawon bude ido da kirkiren tattalin...

Sin Da Rasha Sun Fitar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Game Da Zurfafa Dangantakar Abokantaka Ta Hadin Gwiwa Bisa Manyan Tsare-tsare A Sabon Zamani
Bugu da kari, Sanarwar ta ce Sin da Rasha na goyon bayan kasancewar MDD jigo na shugabancin batutuwan da suka shafi kirkirarriyar basira ko AI, da jaddada muhimmancin martaba ikon mulkin kai na kasashe daban daban, da nacewa bin dokokin kasashe mabanbanta, da martaba ka’idojin MDD yayin gudanar da hakan. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A yau Alhamis ne shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Rasha Vladimir Putin suka rattaba hannu kan wata sanarwa ta hadin gwiwa game da kara zurfafa hadin gwiwar abokantaka bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni tsakanin Sin da Rasha a sabon zamani. (Mai fassara: Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen ta mabiya Al-Houthi ta sanar da cewa: Sanarwar da shugaban Amurka ta fitar kan Yemen gazawa ce ga Netanyahu Kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen ta sanar a jiya Talata cewa: Sanarwar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi dangane da kasar Yemen gazawa ce ga Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu. Mohammed Ali al-Houthi mamba a majalisar koli ta siyasa ta kungiyar Ansarullahi ya bayyana cewa: Sanarwar Trump gazawa ce ga Netanyahu, kuma dole ne fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi murabus daga kan mukaminsa. Ya kara da cewa: “Za su fara tantance sanarwar da Trump ya bayar na dakatar da hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yemen,” bisa la’akari...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya yaba da sadaukarwar da ‘yan jarida suka bayar da suke ba da labaran irin wahalhalun da Falasdinawa ke ciki A wani sako da ya wallafa a shafinsa na twitter na ranar ‘yancin ‘yan jarida ta duniya, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana jin dadinsa ga irin sadaukarwar da ‘yan jarida suka yi, wadanda suka rubuta irin wahalhalun da al’ummar Falastinu suke yi da kuma laifukan da yahudawan sahayoniyya suka yi a tsawon shekaru biyu da suka yi a zirin Gaza. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya rubuta a shafin sada zumunta na “X” a jiya Asabar cewa: Ranar ‘yancin ‘yan jarida ta duniya ta tuna da jarumtakar ‘yan...
Fadar shugaban kasa ta musanta rahotannin da ke nuni da cewa an hana mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, GCON shiga fadar shugaban kasa, inda ta bayyana ikirarin a matsayin shirme, kage da kuma karya gaba daya. Wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da sadarwa na ofishin mataimakin shugaban kasa Stanley Nkwocha ya sanyawa hannu, ta ce rahoton da wasu shafukan da ba su da tushe suka yada shi, na cikin jerin labaran karya da aka kitsa domin haifar da rashin jituwa tsakanin shugaban kasa da mataimakinsa. Sanarwar ta kara da cewa, “Wannan wani yunkuri ne mai rauni na cin mutuncin mutum da ofishin Mai Girma, Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima....
Kantoman Ribas, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas, ya amince da naɗin sabbin kantomomi na ƙananan hukumomi 23 da ke faɗin jihar. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Ribas, Farfesa Ibibia Lucky Worika ya fitar a safiyar wannan Larabar a birnin Fatakwal. ’Yan bindiga sun kashe masunta 3 a Sakkwato Likitocin Nijeriya dubu 16 sun yi ƙaura zuwa ƙetare — Ministan Lafiya Sanarwar ta ce Ibas ya kuma amince da sauya duk majalisun gudanarwa na ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnatin jihar da a baya aka dakatar da ayyukansu. Sanarwar ta ce naɗin sabbin masu kula da gudanarwar ƙananan hukumomin zai fara aiki ne nan take daga ranar Litinin, 7 ga watan Afrilu. Sunayen kantomomin ƙananan hukumomin Ribas
Ƙungiyar ta Kano Pillars ta tabbatar da hakan a shafinta na X da rubutun “Barka Da Dawowa Koci”. A halin yanzu, Kano Pillars na matsayi na takwas a teburin NPFL, da maki 44 bayan buga wasanni 31. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wasu lauyoyi 77 a Jamus sun bukaci gwamnatin kasar da ta mutunta sammacin kotun hukunta manya laifuka ta duniya ICC, na cafke firaministan Isra’ila Banjamin Netanyahu. A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da da suka fitar, fitattun lauyoyin 77 sun kuma bayyana yiwuwar kasancewar Netanyahu a Jamus a matsayin take doka da kuma hakkin kasar. Lauyoyin sun soki Friedrich Martin Josef Merz, dan siyasa kuma shugaban gwamnati a nan gaba, saboda sanarwar da ya yi a lokacin yakin neman zabe cewa zai samo hanyar gayyatar firaministan Isra’ila da kuma tattaunawa ta wayar tarho da Netanyahu bayan nasararsa. Lauyoyin sun kuma yi Allah wadai da halin wasu jami’o’in da suka soke jawabin da Francesca Albanese mai kula da harkokin kare hakkin...
Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya sanya hannu kan dokar majalisar gudanarwar kasar Sin, mai kunshe da matakan dakile takunkuman kasashen waje ta janhuriyar jama’ar kasar Sin. Tanadin dokar zai fara aiki ne tun daga ranar kaddamar da ita. Dokar ta tanadi matakai da aka inganta na dakile takunkumai daga kasashen waje, da tsararrun matakan mayar da martani, da karfafa tsarin gudanar da ayyuka masu nasaba, tsakanin ofisoshin sassan majalisar gudanarwar kasar Sin, da karfafa matakan aiwatar da sassan dokar. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko...
Matatar Dangote ta sanar da dakatar da sayar da Man Fetur da Naira na wucin gadi. Kamfanin ya bayyana wannan mataki ne a cikin wata sanarwa da ya aike wa dillalan man fetur a ranar Laraba da rana. Dokar Ta-ɓaci: Fubara ya fice daga gidan gwamnatin Ribas Fubara ya magantu bayan ayyana dokar ta ɓaci a Ribas A cewar sanarwar, matatar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne domin guje wa matsalar biyan kuɗin ɗanyen mai da ta ke saya da dalar Amurka. “Ya zuwa yanzu, mun sayar da sama da adadin man fetur da muka samu a Naira. “Domin daidaita cinikayyarmu da sayen ɗanyen mai, dole ne mu ɗauki wannan mataki na wucin gadi,” in ji sanarwar. Kamfanin Dangote...
Babban sakantaren MDD António Guterres, ya yi kira ga mabambantan bangarori masu ruwa da tsaki a Yemen da su yi iyakacin kokarin yin hakuri da juna, su kuma dakatar da kowane irin matakin soja, inji kakakinsa a wata sanarwa. Sanarwar ta ce, “Mun lura da cewa, Amurka ta kai hare-hare da dama kan wasu wurare dake karkashin ikon ‘dakarun’yan Houthi, lamarin da ya haddasa asarar rayuka da dama. Sanarwar ta kara da cewa, “Kowane matakin soja da za a dauka na iya tsananta halin da ake ciki, zai kuma haifar da mummunan tasiri, tare da gurgunta yanayin kwanciyar hankali a Yemen, kana zai kara kamarin kalubalen halin jin kai a kasar.” ‘Yan Houthi dai sun yi barazanar karin kai...
Kasar Sin ta bayyana matukar adawa da zarge-zargen kungiyar G7 kan tekun kudancin kasar da manufofinta na tattalin arziki, kuma ta bayyana korafinta ga kasar Canada. Ofishin jakadancin kasar Sin dake Canada ne ya bayyana haka a yau Asabar. A cewar ofishin jakadancin, sanarwar taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar G7 da sanarwar ministocin game da tsaron teku, sun yi shisshigi cikin harkokin gidan Sin, kana sun bata mata suna. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar kula da tituna ta tarayya (FERMA) ta jaddada kudirinta na kula da titunan gwamnatin tarayya da inganta ababen more rayuwa a fadin kasar nan. Daraktan hukumar ta FERMA, Injiniya Kabiru Iliyasu Dan-Mulki ne ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ) daga gidan rediyon tarayya (FRCN) da kuma gidan talabijin na Najeriya (NTA) Kaduna a ofishinsa da ke Kaduna. Injiniya Dan-Mulki ya jaddada babban nauyin da ya rataya a wuyan hukumar ta FERMA na tabbatar da cewa titunan gwamnatin tarayya sun kasance masu kyau domin saukaka zirga-zirga a fadin kasar nan. Ya bayyana muhimmancin hada hannu da masu ruwa da tsaki, musamman kafafen yada labarai, domin wayar da kan...
Rundunar hadaka ta jami’an tsaro da suka hada da ‘yan banga sun yi nasarar hallaka wani kasurgumin jigon kungiyar Lakurawa da aka fi sani da Maigemu a jihar Kebbi. Sanarwar da Daraktan Tsaron, Alhaji AbdulRahman Usman Zagga, ya fitar, ta ce an kashe Maigemu ne a ranar Alhamis a Kuncin Baba da ke karamar hukumar Arewa, bayan musayar wuta da jami’an tsoro. Sanarwar ta ce, wannan nasarar ta zo ne mako guda bayan da Gwamnan Jihar Kebbi, Kwamared Nasir Idris ya ziyarci al’ummar Bagiza da Rausa Kade a yankin karamar Hukumar Arewa, domin jajantawa al’ummar yankin bisa kashe wasu mutane shida da ake zargin barayin shanun Lakurawa ne suka yi. An bayyana cewa, matakin da gwamnan jihar ya dauka kan...
Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya dage dakatarwar da aka yi wa mai bashi shawara na musamman kan harkokin albashi da fansho, Bashir Ado Kazaure da aka mishi a baya ba tare da bata lokaci ba. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Jigawa Malam Bala Ibrahim ya sanyawa hannu kuma ya bai wa manema labarai. Sanarwar ta bayyana cewa, matakin na zuwa ne bayan wani kwakkwaran bincike da kwamitin da aka kafa karkashin jagorancin babban lauyan gwamnati kuma kwamishinan shari’a na jihar Barista Bello Abdulkadir Fanini ya gudanar. “Rahoton kwamitin ya yi tsokaci kan al’amuran da suka dabaibaye dakatarwar da aka yi wa Bashir Kazaure, biyo bayan sanarwar batun biyan mafi karancin albashi...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya (NDLEA) ta bayyana cewa ta kama wani mutum da take zargin madugun fataucin ƙwayoyi ne, Ogbonnaya Kevin Jeff, a maɓoyarsa da ke Jihar Legas. Sanarwar da mai magana da yawun NDLEA, Femi Baba Femi, ya fitar ta ce kamen mutumin mai shekaru 59 na zuwa ne bayan shafe shekaru 17 yana ɓuya, inda yake fataucin miyagun ƙwayoyi na biliyoyin nairori a faɗin duniya. Sanarwar ta ambato Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Muhammad Buba Marwa mai ritaya yana bayyana hakan yayin taron manema labarai a Abuja a yau Litinin. Shugaban NDLEA ya kuma bayyana yadda jami’an sashen ayyukan musamman na hukumar suka riƙa bin diddigin Ogbonnaya biyo bayan nemansa ruwa a jallo...
Rundinar kare juyin juya halin musulinci ta Iran, ta bayyana bikin jana’izar sakataren kungiyar Hezbollah ta Lebanon mai rasuwa Sayyed Hassan Nasrallah da kuma Sayyed Safiedinne da aka gudanar a matsayin wani babban sako na ‘yan gwagwarmaya ga duniya baki daya. Wannan babban taron da akayi a Beirut abun tarihi ne ga duniyar musulmi, ya kuma nuna cewa kungiyar Hizbullah, na da karfinta da kuma akidar kyamar sahyoniyawan. Sanarwar ta kara da cewa: “Bikin da ya samu halartar miliyoyin mutane, a daidai lokacin da ake barazana da jiragen yakin Isra’ila, ya zama wata alama ta karfin Musulunci da cikakken hadin kan al’ummar kasar Labanon. Sanarwar ta yi nuni da cewa, gagarumin taron makoki daga kasashe daban-daban, addinai da kabilu, da...

Kasar Sin Ta Taya Mahmoud Ali Youssouf Murnar Zabarsa Da Aka Yi A Matsayin Sabon Shugaban Hukumar Gudanarwar AU
A kwanan nan ne dai aka gudanar da taron kolin Kungiyar Tarayyar Afirka wato AU karo na 38, inda aka zabi ministan harkokin wajen kasar Djibouti Mahmoud Ali Youssouf a matsayin sabon shugaban hukumar gudanarwar AU na tsawon shekaru hudu. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya taya shi murna a yau 17 ga wata, ya kuma jaddada cewa, kasar Sin a shirye take ta yi hadin gwiwa tare da Youssouf, da sabuwar hukumar gudanarwa ta AU. Yayin da yake amsa tambayoyi a gun taron manema labaru na yau, Guo Jiakun ya bayyana cewa, kasar Sin tana kallon dangantakarta da AU daga mahanga mai muhimmanci kuma na dogon lokaci. Yana mai cewa “A halin yanzu, zaman lafiya da...
An zabi dan takarar kasar Djibouti Mahamoud Ali Youssouf a matsayin sabon shugaban kwamitin gudanarwar kungiyar tarayyar Afrika ta AU. An zabe shi ne a yayin zaman taron kungiyar a birnin Addis Ababa na kasar Habasha da yammacin yau Asabar. Ya samu nasara ne a zagaye na 7 da kuri’u 33 daga cikin 49. Dan shekaru 59 da haihuwa, wanda shi ne ministan harkokin wajen kasar Djibouti zai gaji Moussa Faki Mahamat na Chadi wanda wa’adinsa na biyu kan shugabancin kungiyar zai kare a ranar 15 ga watan Maris. Manyan kalubalen dake gaban sabon shugaban kwamitin gudanarwa na kungiyar ta AU sun hada da rikicin gabashin Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango da Sudan da kuma matakin da shugaban Amurka Donald Trump ya...
Shugaban Kungiyar Yarbawa zalla ta Afenifere, Pa Ayodele Adebanjo ya rasu yana da shekara 96. Rahotanni sun ce dattijon ya rasu ne da safiyar Juma’a a gidansa da ke Lekki a Jihar Legas. An tabbatar da rasuwarsa a wata sanarwa da iyalansa suka fitar. Fursunoni 3 sun lashe Gasar Al-Ƙur’ani a Kano Ta kacame tsakanin mahaifiyar 2Face da budurwarsa “Ya rasu a safiyar yau Juma’a, 14 ga Fabrairu, 2025, a gidansa da ke Lekki, a Legas Nijeriya yana da shekara 96. Za mu ci gaba da riƙe alƙawarinsa na fafutukar tabbatar da gaskiya da adalci. Sanarwar ta ƙara da cewa, har zuwa ƙarshen rayuwarsa ya yi ta bayyana halayansa da gwagwarmayar na tabbatar da samun ’yanci da ci gaban Najeriya...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta jinkirta sakin sauren karin ‘yan Isra’ila da take garkuwa dasu “har sai an ga abinda hali ya yi”, saboda keta dokar da Isra’ila ta yi na tsagaita wuta a Gaza. Sanarwar da bangaren soji na Hamas ta fitar bakin kakakinta Abu Obeida, ta bayyana cewa ‘’fiye da mako uku makiya sun gaza wajen cika yarjejeniyar da suka cimma’’. Hamas ta ce ‘’sakin karin wasu yahudawa na ranar Asabar 25 ga wata an jingine shi, sai nan gaba, yayin da suke jiran makiya su mutunta yarjejeniyar da aka fara aiwatarwa makkonin da suka gabata. Tuni dai Isra’ila ta mayar da martani dangane da sanarwar ta Hamas inda a wata sanarwa da ministan tsaron kasar ya...
A ranar Lahadi ne mahukuntan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars suka bayar da sanarwar dakatar da mai koyarwa, Usman Abdallah mako uku, sakamakon rashin kokarin kungiyar a baya bayan nan a bana da kuma nuna halin rashin hakuri ga magoya bayan kungiyar a lokacin da aka tashi daga wasan da kungiyar ta tashi canjaras da kungiyar Bayelsa United a filin wasa na Sani Abacha dake kofar mata a Kano. A wata sanarwa da aka fitar a shafin sada zumunta na facebook, kungiyar ta ce kociyan ya nuna halin rashin da’a, bayan tashi ba ci a wasa da Bayelsa ba kuma halayyar da ya nunawa magoya baya ba ta dace ba saboda a matsayinsa na mai koyarwa dole ne sai...
Kasashe 79 na duniya sun yi watsi da matakin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dauka na kakabawa kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC takunkumi, suna masu cewa matakin na raunana tsarin dokokin kasa da kasa. Wadannan kasashen da suka hada da Canada, Jamus, Faransa, Afirka ta Kudu da kuma Mexico, a wata sanarwar hadin gwiwa na cewa irin wadannan matakan na kara barazanar rashin hukunta masu manyan laifuka. Har ila yau a cikin sanarwar, kasashen 79 sun jaddada cewa takunkumin da Amurka ta kakabawa kotun ta ICC na iya yin illa ga sirrin bayanan da suka shafi wadanda abin ya shafa, da shaidu da kuma jami’an shari’a, wadanda ‘yan asalin wadannan kasashe ne. Sanarwar ta zo ne...
Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta sanar da naɗa sabon shugabanta, Farfesa Adamu Ahmed. Majalisar Gudanarwar jami’ar ce ta zaɓi Farfesa Adamu Ahmed a matsayin wanda zai maye gurbin Farfesa Kabir Bala. An soma rigimar haraji tsakanin China da Amurka Dalilin da farashin citta ya yi tashin gwauron zabo An sanar da zaɓen Farfesa Adamu da misalin ƙarfe 6:15 na safiyar wannan Larabar a yayin zaman Majalisar Gudanarwar jami’ar wanda Mahmud Yayale Ahmed CFR ya jagoranta. Farfesa Adamu Ahmed dai malami ne a sashen nazarin tsara birane na jami’ar ta ABU. Ya taɓa riƙe muƙamin Darektan Cibiyar Bunƙasa Jami’ar kuma a yanzu shi ne Uban Jami’ar Ilimi ta Tarayya da ke Kano.
Sakamakon sanarwar da Amurka ta fitar kwanan baya a kan kara haraji na kashi 10 cikin dari a kan daukacin kayayyakin kasar Sin da ake kaiwa kasar tare da kafa hujja da wasu batutuwa irin su maganin Fentanyl, a yau Talata, ma’aikatar cinikayya da takwararta ta kudi ta kasar Sin sun fitar da wata sanarwa cewa, Sin ta dauki matakan mayar da martani a kan Amurka tare da fara aiwatarwa. Matakan da suka jibanci lamarin sun hada da cewa, da farko, kasar Sin za ta sanya harajin kashi 10% zuwa 15% kan wasu kayayyakin da ake shigowa da su daga Amurka, daga ranar 10 ga Fabrairu. Sannan na biyu, kasar Sin ta yanke shawarar shigar da rukunin kamfanonin US PVH...
Hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa a Nijeriya (NCDC) ta tsaurara matakan sanya idanu akan hanyoyin shigowa ƙasar sakamakon sabuwar ɓarkewar cutar Ebola a Uganda. NCDC ta gargaɗi ’yan ƙasar da su guji yin tafiye-tafiye zuwa Uganda saboda ɓullar cutar Ebola da aka tabbatar a ƙasar. EU ta yaba wa Gwamna Zulum kan farfaɗo da Jihar Borno Masarautar Fika ta buɗe gasar ƙwallon ƙafa karo na uku a Potiskum Shawarar NCDC na zuwa ne bayan sanarwar Ma’aikatar Lafiya ta Uganda a ranar 30 ga watan Janairun 2025 kan ɓarkewar wani nau’in cutar Ebola mai suna Sudan a gundumomin Wakiso da Mukono da kuma Mbale na ƙasar. Ko da yake sanarwar NCDC ta ce ba a samu wani rahoto ba game...
Kotu ta ba da umarnin tsare tsohon Shugaban Hukumar Inshorar Lafiya ta Kasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf a Gidan Yarin Kuje. Mai Shari’a Chinyere Nwecheonwu ta Babbar Kotun Birnin Tarayya da ke Abuja ta ba da umarnin ne bayan Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arziƙin Ƙasa (EFCC) ta gurfanar da Farfesa Usman Yusuf kan zargin almundahana. A safiyar Litinin ne EFCC ta gurfanar da Farfesa Usman Yusuf, inda bayan an karanta masa tuhumar da ake masa ya musanta aikata laifin. Daga nan ne lauyansa O.I Habeeb, ya buƙaci umarnin kotu na tsare shi a ofisoshin EFCC zuwa lokacin zai shigar da buƙatar beli. Gwamnatin Najeriya za ta sake ƙara kuɗin lantarki NAJERIYA A YAU: Dalilin Da Za Mu Kashe...

Sanarwar Yiwuwar Kai Harin Ta’addanci Kano Lokacin Maulidi: Mun Cafke Wani Da Bama-bamai – Kwamishina
Ya bayyana cewa, wadanda ake zargin sun tsere daga jihar biyo bayan tona musu asiri, amma an cafko daya an dawo da shi Kano bayan ya tsere da farko. CP Dogo, ya jaddada mahimmancin samun rahoton leken asiri wajen dakile barazanar da ake iya fuskanta, tare da yin cikakken bayani kan yadda ‘yansanda suka hada kai da masu ruwa da tsaki don inganta tsaro a lokacin taron.