Diflomasiyyar Shugabanni Na Matukar Taka Rawar Gani Wajen Jagorantar Dangantakar Sin Da Amurka
Published: 23rd, October 2025 GMT
A yau Laraba 22 ga wata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana cewa, huldar diflomasiyya ta shugabanni na matukar taka rawar gani wajen jagorantar dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka, kuma shugabannin kasashen biyu suna ci gaba da cudanya da kuma sadarwa a tsakaninsu.
Shugaban Amurka Trump ya ce, yana sa ran kasashen Sin da Amurka za su cimma matsaya kan batutuwan kasuwanci a taron kolin APEC da za a yi a mako mai zuwa, amma ya ce, watakila shugabannin Sin da Amurka ba za su gana ba a lokacin. Guo Jiakun ya yi wadannan bayanai ne a lokacin da yake amsa tambayoyi game da wannan batu, inda ya yi nuni da cewa, a halin yanzu babu wani cikakken bayani dangane da ganawar shugabannin Sin da Amurka.
Game da tattaunawar gaggawa tsakanin EU da kasar Sin kan batun hana fitar da ma’adanan farin karfe da kasar Sin ta yi kuwa, Guo Jiakun ya ce, yana fatan bangaren EU zai mutunta kudurinsa na nuna goyon baya ga cinikayya cikin ‘yanci, da adawa da kariyar cinikayya, da samar da yanayin kasuwanci na gaskiya da adalci da rashin nuna wariya ga daukacin kamfanonin kasashen duniya, da daukar kwararan matakai don kiyaye tattalin arzikin kasuwanci da ka’idojin hukumar kasuwanci ta duniya (WTO), da kafe kai da fata a kan amfani da tattaunawa da tuntuba wajen warware takaddamar kasuwanci yadda ya kamata. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Wakilin Amurka Na Musamman A Siriya Ya Matsa Don Ganin Kasashen Saudiyya Da Lebanon Da Kuma Siriya Sun Kulla Alaka Da Isra’ila
Wakilin Amurka na Musamman a kasar Siriya ya matsa kaimi domin ganin kasashen Saudiyya da Lebanon da kuma Siriya sun kulla alakar jakadanci da haramtacciyar kasar Isra’ila
Wakilin Amurka na musamman a Siriya Tom Barrack, ya gabatar da manufofinsa na sake fasalin yankin Gabas taTsakiya a siyasance bayan kawo karshen yakin Gaza.
A cikin dogon hangen nesa, wanda ya wallafa a shafinsa na Twitter, Barrack ya yi ikirarin cewa abu mafi muhimmanci shi ne samar da zaman lafiya a yankin, da kwance damarar Hizbullah, da shigar da kasashen Labanon da Siriya cikin yarjejeniyoyin kyautata alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila. Ya kara da cewa Saudiyya ma tana dab da kyautata alakarta da haramtacciyar kasar Isra’ila.
Barrak ya bayyana cewa: Taron Sharm el-Sheikh da aka gudanar a ranar 13 ga watan Oktoba tare da halartar shugaba Trump da shugabannin kasashen Larabawa da na musulmi, ya wakilci wani muhimmin lokaci a harkokin diflomasiyya na zamani na gabas ta tsakiya, la’akari da cewa abin da aka fara a matsayin sulhu a Gaza ya rikide zuwa “sabon aikin hadin gwiwa da shugaba Trump ya jagoranta na sake ginawa da bunkasa ci gaban yankin.”
Barrak ya yi imanin cewa, kasashen Larabawa da na yammacin duniya sun hade kansu a kan manufar “maye gurbin tsoro da dama da kuma keben wata kasa da bude kofa,” yana mai cewa taron na Sharm el-Sheikh “ba wai kawai bikin tsagaita bude wuta ba ne da kuma sako mutanen da aka yi garkuwa da su ba, a’a mafarin shirin zaman lafiya na dogon lokaci da ya danganci ci gaba da hadewar yankin,” in ji shi.
Amnesty International
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kungiyar Kare Hakkin Bil-Adama Ta Amnesty Ta Zargi Gwamnatin Tanzaniya Da Musgunawa ‘Yan Adawa October 20, 2025 Dakarun kare Juyin Musulunci Na Iran Sun Bayyan Shirinsu Na Karfafa Dabarun Hadin Guiwa Da yamen October 20, 2025 October 20, 2025 Kotu A Faransa Ta Yanke Hukumci Zama Gidan Yari Ga Tsohon Shugaban Kasar Nicola Sarkozi October 20, 2025 Isra’ila Ta Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta Sau 80 Ta Kashe Mutane 97 Ta Jikkata 230 October 20, 2025 Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Mukaman Gwamnatin Tinubu inji Shugaban FCC October 20, 2025 Grossi: Za a iya warware batun Shirin nukiliyar Iran ne kawai ta hanyar diflomasiyya October 20, 2025 Trump: Shugabanin Hamas ba su da hannu a kisan sojojin Isra’ila 2 a Gaza October 20, 2025 Iran Da Azerbaijan Suna Gudanar Da Atisayen Hadin Guiwa Na Sojojin Ruwa A Tekun Caspian October 20, 2025 Gwamnatin Yamen Tana Tsare Da Ma’aikatan MDD 50 Ta Kuma Kwace Kayakin Aikinsu October 20, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci