Gwamnatin Tarayya ta bayyana alhinin ta kan mummunar haɗarin fashewar motar mai da ta faru a ƙauyen Essa, cikin Karamar Hukumar Katcha ta Jihar Neja, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu da yawa.

 

A cikin wata sanarwa da Ministan Yada Labarai da Tsarin Ƙasa, Mohammed Idris, ya sanya wa hannu, Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyya ga Gwamnatin Jihar Neja da al’ummar jihar bisa wannan babban rashi, tana mai bayyana lamarin a matsayin abin tunawa da illar da ke tattare da haɗarin motocin mai a ƙasar.

 

Sanarwar ta nuna damuwa kan yadda, duk da wayar da kai da gargadin da ake yi a kai a kai, wasu ’yan ƙasa har yanzu ke shiga cikin haɗari ta hanyar kwasar mai daga motoci da suka kife, wanda hakan kan haifar da asarar rayuka da dukiya.

 

Ministan ya jaddada cewa duk rayuwar ɗan Najeriya tana da muhimmanci, tare da yin kira da a ƙara lura da bin matakan tsaro a lokutan gaggawa.

 

Ya yaba wa Gwamnatin Jihar Neja, jami’an tsaro, da kuma masu aikin ceto bisa saurin da suka nuna wajen kashe wutar da kuma ceto rayuka.

 

Haka kuma, Ministan ya bayyana cewa Hukumar Kula da Bala’o’i ta Ƙasa (NEMA) ta samu umarni da ta ci gaba da ba da tallafi da taimakon gaggawa ga waɗanda abin ya shafa, yayin da Hukumar Wayar da Kan Jama’a (NOA) za ta ƙara ƙaimi wajen yaɗa faɗakarwa domin hana irin wannan bala’i a nan gaba.

 

Gwamnatin Tarayya ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan waɗanda suka mutu, tare da yin addu’a ga Allah Ya jikansu, Ya kuma ba waɗanda suka jikkata lafiya ta ƙwarai.

 

Bello Wakili

 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Gwamnatin Tarayya ta

এছাড়াও পড়ুন:

Dan Wasan Barkwanci A Finafinan Indiya, Asrani Ya Rasu

Fitaccen jarumin barkwancin finafinan Indiyan nan Asrani ra rasu.

Asrani, wanda  asalin sunansa shi ne Govardhan Asrani, ya rasu yana mai shekaru 84, kuma ya shafe sama da shekara 50 yana fitowa a finafinan Indiya, inda ya fito a finafinai sama da 350.

Dan wasan finafinan, ya shahara wajen taka rawar barkwanci da kuma ƙaramin jarumi wanda ake kira da mai taimaka wa jarumi wato supporting actor. Daga cikin fina-finansa da suka yi fice akwai Sholay, inda ya fito a matsayin ɗansand da Bawarchi da Chupke-Chupke da Hera Pheri da Muqabla da Dhamaal da Yamla Pagla Deewana da Dillagi da Welcome da Bhool Bhulaiya da Garam Masala da Baghban da The Burning Train da Ajnabee da Seeta aur Geeta da Sargam da dai sauransu.

Ya karbi lambobin yabo da dama da suka hada da jarumin da yafi kowa iya barkwanci wanda kamfanin Film Fare ya ba shi.

Ya mutu ya bar matarsa wadda ita ma jaruma ce wato Manju Asrani da kuma ɗansa Naveen Asrani.

Ya yi fina-finai da jarumai da dama da suka hada Amita Bachchan da Dharamendra da Jeetandra da Shatugan Sinha da Rajesh Khanna da Rishi Kapoor da Vinod Khanna da Akshay Kumar, da Shahrukh Khan da Aamir Khan da Salman Khan da Ajay Devgan da Sanjay Dutt da dai sauransu.

Bbc

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ’Yan uwana 8 sun rasu a fashewar tanka a Neja — Wani Mutum
  • Gwamnatin Tarayya Ta Jajantawa Waɗanda Fashewar Tankar Mai Ta Rutsa Da Su A Neja 
  • Majalisa Ta Buƙaci Gwamnatin Tarayya Ta Kai Agajin Gaggawa Ga Waɗanda Fashewar Tanka Ta Shafa A Neja
  • Gwamnonin Arewa sun yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a fashewar tanka a Neja
  • Gwamnoni Sun Yi Ta’aziyyar Mutanen Da Suka Rasu A Fashewar Tankar Mai A Neja
  • Fashewar tankar mai ta yi ajalin mutum 30 a Neja
  • Da Ɗumi-ɗumi: Fashewar Tankar Man Fetur Ta Yi Ajalin Rayuka 30 A Neja
  • Mutane 3,433 Sun Rasu a Hatsarin Mota 6,858 Cikin Wata 9 A Nijeriya – FRSC
  • Dan Wasan Barkwanci A Finafinan Indiya, Asrani Ya Rasu