Iran Ta Yi Allah Wadai Da Hare-Haren Isra’ila Kan Kasar Lebanon
Published: 24th, October 2025 GMT
Kasar Iran ta yi Allah wadai da hare-haren wuce gona da iri da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai kan kasar Lebanon
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta yi Allah wadai da hare-haren da yahudawan sahayoniyya suka kai ta sama kan yankunan kudancin Lebanon da kwarin Beka’a na kasar.
Baqa’i ya bayyana hare-haren da ‘yan sahayoniyya suka kai a ranar Alhamis a yankunan kudancin da kwarin Beka’a na Lebanon, wadanda suka yi sanadiyyar shahada da kuma raunata wasu fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba, ciki har da dalibai a wata makaranta a kwarin Beka’a, tare da bayyana harin a matsayin “laifi na ta’addanci” kuma ya yi suka mai tsanani kan su.
Baqa’i ya gabatar da alhini da ta’aziyya ga iyalan shahidai da kuma al’ummar Lebanon, yana mai jaddada bukatar gurfanar da ‘yan Sahayoniyya a gaban kotun kasa da kasa domin hukunta su saboda laifukan da suka aikata.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ya nuna cewa ci gaba da aikata laifukan ‘yan Sahayoniyya ba tare da daukar matakan shari’a kan su ba saboda goon bayan da suke samu daga Amurka ce iri rufe.
Ya kuma yi la’akari da hare-haren da ‘yan Sahayoniyya ke kai wa kan ‘yantacciyar kasar Lebanon mai cikakken ‘yancin kare kasarta, a matsayin keta yarjejeniyar tsagaita wuta, shaida karara na yanayin ayyukan ta’addanci da kokarin mamaya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Rasha Ta Jaddada Cewa: Kasashen Turai Sun Taka Doka Kan Batun Makamashin Nukiliyar Iran October 24, 2025 Ayatullahi Khatami Ya Ce: Shugaban Amurka Dan Ta’adda Ne October 24, 2025 Shugaban Amurka Ya Ce: Za Su Dauki Matakin Soji Kan Kasar Venezuela Nan Gaba Kadan October 24, 2025 Gwamnatin Iraki Ta Yi Allah Wadai Da Mamaye Yankin Yammacin Kogin Jordan Na Falasdinu October 24, 2025 ‘Yan Sandan Kasar Ghana Sun Tseratar Da ‘Yan Najeriya 57 Da Aka Yi Fasakwaurinsu October 24, 2025 Trump Ya Dakatar Da Tattaunawar Kasuwanci Da Kasar Canada October 24, 2025 Gaza: Tasirin Rashin Abinci Mai Gina Jiki Da Magani Zai Ci Gaba Har Zuriya Mai Zuwa October 24, 2025 Iran Ta Lashe Kambun Duniya Na Kokawar Gargajiya October 24, 2025 Pezeshkian: Iran za ta gwammace takunkumi a kan mika wuya October 24, 2025 Trump: Amurka na shirin kai hare-hare a Venezuela October 24, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: da hare haren
এছাড়াও পড়ুন:
Talauci Yana Karuwa A “Isra’ila” Bayan 7 Ga Watan Oktoba
A wani rahoton da jaridar Jerissalam Post” ta buga ta ambaci cewa; Tun bayan farmakin 7 ga watan Oktoba 2023, ana kara samun matalauta da talauci.
Rahoton ya yi nuni da cewa karuwar talaucin yana da alaka ne da yadda farmakin 7 ga watan Oktoba ya yi tasiri a cikin tattalin arziki “Isra’ila”.
Haka nan kuma rahoton ya ce, da akwai dubban iyalai yahudawa wadanda gabanin yaki, suke rayuwa cikin yanayi mai kyau ta fuskar tattalin arziki, yanzu sun zama matalauta. A dalilin haka cibiyar da ta shirya rahoton ta “ Latit” tana yin gargadi akan cewa; za a iya samun ci gaba da yaduwar talaucin, domin iyalai da dama suna gogoriyon yadda za su iya biyan bukatar yau da kullum, duk da cewa suna da cikakken aiki.
Ita dai kungiyar “Latit” ta ‘yan sahayoniya ce wacce aka kafa a 1996 domin fada da talauci da kuma rashin abinci.
Haka nan kuma rahoton ya bayyana cewa; Adadin iyalan da suke fama da talauci a cikin ‘yan sahayoniyar sun kai 867,000, saboda ba su da lamunin abinci. Adadin daidaikun wadannan iyalan sun kai miliyan 2.8, daga cikinsu da akwai kananan yara miliyan 1.18.
Haka nan kuma wani sashen na rahoton ya ce, talaucin yana karuwa ne da kaso 27-29%.
Da dama daga cikin iyalan ‘yan sahayoniyar suna rayuwa ne ta hanyar samun taimako da tallafi na abinci,domin suna amfani da kudaden da suke samu na aikin yi, domin biyan kudaden wuta da sayen magunguna.
Kaso 40% na tsofaffi suna fama da matsalar tabarbarewar rashin lafiya, da ya faro tun daga farkon yaki.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka AU Ta yi Tir Da Harin RSF A Makarantar Kananan Yara Da Ya Kashe Mutane 80 December 8, 2025 MِِِِDD: Kisan Kare Dangin Da Isra’ila Ta yi A Gaza Shi Ne Farko Da Yafi Jan Hankalin duniya December 8, 2025 Iran Da Azarbaijan Sun Amince Da Ci Gaba Da Tuntubar Juna Domin Warware Matsaloli December 8, 2025 Iran Da Kasashen Afrika Sun Daura Dammarar Karfafa Alakar Kimiyya Tsakaninsu December 8, 2025 Ecowas Ta Tura Sojoji Zuwa Jamhuriyar Benin Don Dakile Juyin Mulki December 8, 2025 IRGC: Makaman Iran Sun Fada Kan Matatan Man Haifa Har Sau Biyu A Yakin Kwanaki 12 December 8, 2025 Najeriya: Gwamnatin Tarayya Ta Bada Sanarwan Kubutar Da Yan Makaranta 100 Da Aka Sace December 8, 2025 Iraki Ta Musanta Cewa Ta Tushe Asusun Hizbullah Da Ansarallah December 8, 2025 Sabon Fada Ya Barke A Tsakanin Thailand Da Cambodia December 8, 2025 Iran Ta Yi Allawadai Da Kisan Fararen Hula A Kasar Sudan December 8, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci