Gwamnatin Iraki Ta Yi Allah Wadai Da Mamaye Yankin Yammacin Kogin Jordan Na Falasdinu
Published: 24th, October 2025 GMT
Gwamnatin kasar Iraki ta yi Allah wadai da matakin da Majalisar Dokokin Isra’ila “Knesset” ta dauka na mamaye yankin Yammacin Kogin Jordan da kuma gine-gine matsugunan yahudawa ‘yan kaka gida ba bisa ka’ida ba
Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar Iraki ta bayyana Allah wadai da amincewa da kudurorin biyu na Majalisar Dokokin Isra’ila “Knesset” ta yi da su da nufin sanya kwace iko da mallakar yankin Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye da kuma gudanar da matsugunan yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida ba bisa ka’ida ba.
Ma’aikatar ta ce a cikin wata sanarwa cewa: “Tana bayyana kakkausar suka da Iraki ta yi kan amincewar da Majalisar Dokokin Isra’ila ta yi da kudurorin biyu da nufin kwace iko da mallake yankin Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye da kuma gudanar da gine-ginen matsugunan yahudawa ‘yan share wuri zauna ba bisa ka’ida ba, matakin da ya zama keta dokokin kasa da kasa da kudurorin Majalisar Tsaro masu dacewa, da kuma take hakki kai tsaye na halaltattun hakkokin al’ummar Falasdinu.”
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iraki ta tabbatar da cewa “waɗannan matakan fadada suna lalata damar samun kwanciyar hankali da kuma ci gaba da tabbatar da mummunan kwace da mamaye yankunan da karfi, don wadannan matakai suna barazana ga tsaro da kwanciyar hankali a yankin baki daya,” tana mai jaddada “matsayinta mai karfi da goyon baya kan manufar Falasdinu da kuma ‘yancin al’ummar Falasdinu na neman ‘yancin kai da kuma kafa kasarsu mai cin gashin kanta, tare da kasancewar Qudus a matsayin babban birninta.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka ‘Yan Sandan Kasar Ghana Sun Tseratar Da ‘Yan Najeriya 57 Da Aka Yi Fasakwaurinsu October 24, 2025 Trump Ya Dakatar Da Tattaunawar Kasuwanci Da Kasar Canada October 24, 2025 Gaza: Tasirin Rashin Abinci Mai Gina Jiki Da Magani Zai Ci Gaba Har Zuriya Mai Zuwa October 24, 2025 Iran Ta Lashe Kambun Duniya Na Kokawar Gargajiya October 24, 2025 Pezeshkian: Iran za ta gwammace takunkumi a kan mika wuya October 24, 2025 Trump: Amurka na shirin kai hare-hare a Venezuela October 24, 2025 Ivory Coast: Ayyukan ma’adinai na fuskantar tsaiko yayin da Ouattara ke neman wa’adi na 4 October 24, 2025 Dangote zai sayar da kaso 10 na hannun jarin matatar man shi October 24, 2025 Larabawan Yankin Tekun Fasha Sun Caccaki Sabon Shirin Isra’ila A Kan Yammacin Kogin Jordan October 24, 2025 Albanese: Wajibi Ne A Kawo Karshen Gwamnatin Mamaya A Falasdinu October 23, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: yankin Yammacin Kogin Jordan
এছাড়াও পড়ুন:
Birtaniya Ta Cire Kungiyar Tahrirush -Sham Daga Jerin Yan Ta’adda
Rahotanni su bayyana cewa gwamnatin birtaniya ta sanar a hukumance cire kungiyar tahrirush shams HTS daga cikin jerin kungiyoyin yan ta’adda a wani yunkuri na ganin ta kara kusantar sabuwar gwamnatin siriya bayan faduwar gwamantin Bashar Al-Asad.
Gwamnatin birtaniya ta bayyana cewa wannan mataki zai sanya su kara kusanci da gwamnatin siriya da Abu mohammad Al-Jolani ke jagoranta wanda aka fi sani da Ahmed sharaa wanda shi ne shugaban kungiyar Al-Qaida kuma kwamandan Daesh.
Wannan sanarwar ta zo ne bayan ziyarar da sakataren harkokin wajen birtaniya David lammy ya kai kasar siriya a watan yuli, wanda ya sanya ya zama shi ne babban jami’in diplomasiya da ya kai ziyara kasar a tsawon shekaru.
Kuma mataki yazo ne duk da hujjoji da ake da su na laifukan yaki, cin zarafin dan adam da kungiyar HTS ta yi musamman ma kan kabilu marasa rinjaye irin su alawiyyawa wanda suke fuskantar gallazawa daga bangaren gwamnati.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka China Ta Kammala Gina Cibiyar Adana Bayanai Masu Amfani Da Karfin Iska October 22, 2025 Iran Ta Godewa Rasha Game Da Goyon Bayan Da Ta Bata A Kwamitin Sulhu Na M D D October 22, 2025 Sudan: Jirgin ‘Drone’ Ya Fada Kan Tashar Jiragen Sama Na Khurtum Kafin A Sake Bude Ta October 22, 2025 Sheikh Qasim: Natanyahu Ya Zubar Da Jini Mai Yawa Amma Babu Lamuni Ga Amincin Isra’ila Nan Gaba October 22, 2025 Aragchi Da Guterres Sun Tattauna Kan Gaza Da Rikicin Yemen Ta Wayar Tarho October 22, 2025 Rasha da Habasha sun tattauna kan karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu a fannin nukiliya October 22, 2025 Sayyed al-Houthi: Mun shirya dawowa fagen daga idan Isra’ila ta ci gaba da kisan kiyashi a Gaza October 22, 2025 Nigeria: “Yan Sanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Neman Sakin Jagoran ‘Yan Awaren Biafara October 21, 2025 HKI Tana Ci Gaba Da Hana Wa Falasdinawa Abinci October 21, 2025 An Yi Fashi Da Makami A Gidan Adana Kayan Tarihin ” Louvre” Na Kasar Faransa October 21, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci