Tun da PDP ta bar mulkin Najeriya maguɗin zaɓe ya ragu – Akpabio
Published: 23rd, October 2025 GMT
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce tsarin zabe a Najeriya ya samu gagarumin ci gaba tun bayan da jam’iyyar PDP ta bar mulkin kasar a matakin tarayya.
Akpabio, wanda aka zabe shi sau biyu a matsayin gwamna karkashin PDP kuma ya fara shiga majalisar dattawa a karkashin jam’iyyar, ya bayyana hakan ne a lokacin karatu na biyu a kan dokar gyaran tsarin zabe a zaman majalisa da aka yi a ranar Laraba.
“Ina da tabbacin cewa ni da Sanata Abaribe, wanda muka shafe kusan shekaru 25 muna cikin harkar siyasa, na san ba mu damu da jam’iyya ba, ana iya lashe zabe a ko’ina.
“Ka na da ƙwarewa sosai, amma za ka yarda da ni cewa tun bayan faduwar PDP, zabe ya inganta matuka a wannan ƙasa.
“Na tuna, ina da kusanci da yawancin shugabannin ƙasa tun daga 1999, kuma a 2007 lokacin da na ci zabe a matsayin gwamna, shugaban ƙasa na lokacin, Allah ya jiƙansa, Shugaba Yar’Adua, ya fito fili ya ce zaben da ya kawo shi mulki yana da lam’a.
“Ya ce cike yake da kura-kurai da magudi. Tun daga lokacin, muka fara rufe guraben da ke haifar da matsala.”
Akpabio ya ƙara da cewa duk da cewa ’yan Najeriya na fuskantar ƙalubale, tsarin ya inganta.
“Ka duba zaben da ya gabata, har sai da muka je Kotun Koli muna muhawara kan ko lashe babban birnin tarayya kadai ya isa ya sa dan takara ya zama shugaban ƙasa,” in ji shi.
“Hankali kawai ya isa ya gaya mana cewa ba haka dokar zabe take nufi ba,” in ji Akpabio.
Shugaban majalisar dattawa ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki bayan PDP ta fadi zabe a shekarar 2015.
Ya tsaya takarar Sanata a 2019 a karkashin jam’iyyar APC, amma bai ci ba.
Sai dai tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa shi minista daga bisani, kafin a 2023 kuma ya ci zaben sanatan daga jiharsa ta Akwa Ibom, sannan aka zabe shi shugabancin majalisar.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Yadda Kwankwaso ya yi murnar zagayowar ranar haihuwarsa
Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya sanar da shirinsa na ɗaga darajar Kwalejin Jinya ta Nafisatu da ke Kwankwaso zuwa cikakkiyar Jami’ar Kiwon Lafiya albarkacin bikin zagayowar ranar haihuwarsa.
Taron na wannan Talatar, 21 ga watan Oktoban 2025, ya gudana ne a garinsa na Kwankwaso da ke Karamar Hukumar Madobi, inda aka yaba da ci gaban da makarantar ta samu tun daga kafuwarta a 2019 zuwa yanzu.
Tinubu ya naɗa sabon Minista Alƙaluman wucin-gadi na nuna Paul Biya ya lashe zaɓen KamaruKwankwaso ya ce an ɗauki wannan mataki ne domin ƙara buɗe damammaki ga mata matasa su sami ilimin kiwon lafiya mai zurfi.
Ya jaddada cewa makarantar ita ce ta farko a Najeriya da ke karɓar dalibai mata kaɗai.
Ya kuma gode wa gwamnatin Jihar Kano bisa tallafa wa shirin ungozoma na Community Midwives, wanda ke taimakawa wajen inganta lafiyar mata a ƙauyuka.
A nasa jawabin, Farfaesa Saleh Ngaski Garba, shugaban majalisar gudanarwar makarantar, ya bayyana cewa kwalejin ta taimaka sosai wajen bai wa mazauna ƙauyen ilimin jinya da ungozoma, kuma yanzu tana da ɗalibai sama da 400 da suka kammala karatu.
Kwankwaso ya ce gina jami’ar zai amfanar da Kano da Najeriya baki ɗaya.