Aminiya:
2025-12-02@20:22:27 GMT

Kamaru: Sojoji da ministoci sun taya ni murnar cin zabe —Issa Tchiroma

Published: 18th, October 2025 GMT

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar adawa a Kamaru, Issa Tchiroma Bakary, ya yi iƙirari cewa ministoci da manyan hafsoshin sojin ƙasar sun taya shi murnar bayan bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka kammala.

Issa Tchiroma Bakary ya bayyana cewa ministoci da manyan jami’an tsaron da ministocin sun kira shi a waya suna jaddada goyon bayansu da niyyar biyayya ga kundin tsarin mulkin ƙasar da kuma abin da al’umma suka zaɓa.

Ya bayyana haka ne wani a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, yana mai nuna godiya ga waɗanda suka goyi bayansa, tare da jaddada cewa wannan lokaci yana da muhimmanci matuka ga kasa.

Ya ce, “Ina godiya daga zuciyata ga ministoci da jami’an gwamnati da suka kira ni kwanan nan domin nuna goyon bayansu. Wannan ba lokaci ba ne na wasa ko lissafi — lokacin ne da makomar ƙasa da zaman lafiya ke cikin haɗari, kowa sai ya zaɓi bangarensa, kuma da dama sun riga sun yi hakan,” in ji shi.

Rashin tsaro: An rufe makarantu sama da 180 a Arewa Ma’aurata 136 sun kashe juna a shekara 4

Bakary ya ƙara da cewa wasu manyan hafsoshin soji sun tabbatar masa da cewa suna tare da al’umma, ba tare da la’akari da matsayi ko iko ba.

“Ina godiya ga wasu manyan hafsoshin soji da suka bayyana cewa ba za su ci amanar aikinsu na kare al’umma ba. Ina fatan sauran za su bi sahu nan gaba, domin tarihi zai tuna da waɗanda suka zaɓi al’umma fiye da jin daɗin kansu.”

Ya kuma yi kira ga ’yan jarida da su guji yaɗa labaran karya ko na son zuciya.

“’Yan jarida, kada ku bari a mayar da ku kayan aikin yaɗa labaran da ba su da tushe saboda neman matsayi ko abin duniya. Matasa na kallon ku a matsayin abin koyi — kada ku zama abokan gaba ga al’umma.”

A ƙarshe, Bakary ya yi kira da a haɗa kai da a zauna cikin shiri da kwarin gwiwa.

“Lokaci yana da tsanani, amma  kyakkyawan fata ya fi ƙarfi. Mu tashi tsaye, mu haɗa kai, mu kasance cikin shiri. Makomar ƙasar nan tana hannunmu.”

Sai dai har yanzu hukumar zabe ta Kamaru ba ta fitar da sakamakon zaɓen ba.

Ana sa ran nan da ranar 26 ga watan nan da muke ciki hukumar za ta sanar da sakamakon zaɓen da aka gudanar a ƙarshe makon da ya gabata.

 

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Goyon Baya Issa Tchiroma Bakary Kamaru Zaɓe

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan bindiga sun sace fasto da matarsa  masu ibada a Kogi 

’Yan bindiga sun yi garkuwa da wani fasto da matarsa da mabiyansa a yayin da suke tsaka da ibada a coci da ke a  Jihar Kogi.

Wani ganau da ke cikin cocin a lokacin da aka kai harin, Adegboyega Ogun, ya ce misalin ƙarfe 9.30 na safe ’yan bindigar suka kai harin suna bude wuta.

“Mutane sun qarshe ta ko’ina, har da faston, wanda aka fi sani da Baba Orlando da matarsa da wasu masu ibada duk an yi garkuwa da su. Gaskiya harin ya yi muni, dukkanmu tserewa muka yi daga cocin.”

Sace masu ibadar a ranar Lahadi a Cocin Cherubim and Seraphim ya auku ne bayan a kwanan nan Gwamna Usman Ododo, ya koka da cewa wasu  manyan jagororin ’yan bindiga sun dawo jihar.

Kafin nan a ranar Asabar ’yan bindiga sun tare hanya, suka yi garkuwa da matafiya cikin motoci uku a kan hanyar Isanlu-MakutuIdofin da ke Ƙaramar Hukumar Yagba ta Gabas.

Wani mazaunin yankin, Enimola Daramola ya bayyana cewa, “mutum ɗaya ne kacal ya samu tserewa a motocin da aka tafi da su cikin daji.”

“Amma mun samu labari yau cewa sojoji da ’yan banga sun bi sawun ’yan bindigar inda suka yi musayar wuta suka ceto wasu daga cikin mutanen,”

A ranar Lahadi kuma aka samu rahoton cewa an kai wa wata motar haya hari.

“Matuƙin motar da fasinjojin sun tsallake rijiya da baya. Yanzu hanyar ta zama mai hatsari sosai,” in ji David Juwon, mazaunin yankin Isanlu.

Sabon harin Cocin Cherubim and Seraphim na zuwa ne makonni kaɗan bayan makarancinsa da ’yan bindiga suka sace mutane 38 a wani Cocin CAC da ke yankin Eruku na Karamar Hukumar Ekiti a Jihar Kwara.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sharhi:’HKI tana fama da karancin sojojin a dukkan rassan sojojin kasar’.
  • Mutane 9,854 na ɗauke da cutar AIDS a Yobe 
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan 164
  • Wani Dan Adawa Da Gwamnatin Paul Biya Ya Mutu A Gidan Yari A Kasar Kamaru
  • ’Yan bindiga sun sace fasto da matarsa  masu ibada a Kogi 
  • Sojoji sun ceto ’yan mata 12 da ISWAP suka sace a Borno
  • ’Yan bindiga sun sace amarya da ƙawenta 14 a Sakkwato
  • Sojoji sun ceto mutum 7 da ’yan bindiga suka sace a Kano
  • An sake zabar Eto’o a matsayin Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Kamaru  
  • Shugaban Pakistan Yayi Kira Da A Gudanar Da Bincike Kan Laifukan Yaki Da HKI Ke Tafkawa