Korarren Jami’in Gwamnatin Isra’ila Ya Ce: Dole Ne A Yi Bincike Kan Sakacin Da Hamas Ta Samu Sukunin Kai HariIsra’ila
Published: 22nd, October 2025 GMT
Shugaban kwamitin tsaro na haramtacciyar kasar Isra’ila ya jaddada cewa: Dole ne a gudanar da bincike kan sakacin Isra’ila har Hamas ta kai harin ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023
Tzachi Hanegbi, shugaban kwamitin tsaro na haramtacciyar kasar Isra’ila, ya yi kira da a gudanar da bincike kan bala’in gazawar da aka yi a ranar 7 ga Oktoban shekara ta 2023 har kungiyar Hamas ta yi nasarar aiwatar da gagarumar nasara kan Isra’ila.
Wannan ya zo ne a cikin kalaman farko da Hanegbi ya yi tun bayan da Fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya kore shi daga kan mukaminsa.
Hanegbi ya ce: “Netanyahu ya sanar da shi yau cewa ya kore shi daga kan mukaminsa.”
Ya kara da cewa: “Dole ne a bincika mummunan gazawar ranar 7 ga watan Oktoba domin daukar darasi da kuma taimakawa wajen dawo da amanar da ta ruguje.”
Hanegbi na daya daga cikin fitattun makusantan masu aikata laifukan yaki Benjamin Netanyahu, amma sabanin baya-bayan nan da aka samu tsakanin bangarorin biyu dangane da gudanar da yakin da ake yi a zirin Gaza ya taimaka wajen korar tasa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Wani Masani Dan kasar Iran Ya Samu Lambar Yabo Ta WHO A Yankin October 22, 2025 Majalisar Najeriya Ta Amince Da Dokar Daurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Kananan Yara Fyade October 22, 2025 Birtaniya Ta Cire Kungiyar Tahrirush -Sham Daga Jerin Yan Ta’adda October 22, 2025 China Ta Kammala Gina Cibiyar Adana Bayanai Masu Amfani Da Karfin Iska October 22, 2025 Iran Ta Godewa Rasha Game Da Goyon Bayan Da Ta Bata A Kwamitin Sulhu Na M D D October 22, 2025 Sudan: Jirgin ‘Drone’ Ya Fada Kan Tashar Jiragen Sama Na Khurtum Kafin A Sake Bude Ta October 22, 2025 Sheikh Qasim: Natanyahu Ya Zubar Da Jini Mai Yawa Amma Babu Lamuni Ga Amincin Isra’ila Nan Gaba October 22, 2025 Aragchi Da Guterres Sun Tattauna Kan Gaza Da Rikicin Yemen Ta Wayar Tarho October 22, 2025 Rasha da Habasha sun tattauna kan karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu a fannin nukiliya October 22, 2025 Sayyed al-Houthi: Mun shirya dawowa fagen daga idan Isra’ila ta ci gaba da kisan kiyashi a Gaza October 22, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Na kashe N100bn a kan harkar tsaro a 2025 — Zulum
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce gwamnatinsa ta kashe kusan Naira biliyan 100 a wannan shekara domin inganta tsaro a faɗin jihar.
Ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci Sarkin Uba, inda ya yi masa jaje kan hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutane da dama.
Jami’an tsaro sun kama masu garkuwa da mutane 7 a Gombe Najeriya ta shigo da tataccen man fetur na tiriliyan 12.8 cikin watanni 15Zulum ya yaba wa jami’an tsaro da al’umma kan ceto manoman mata 12 da aka yi garkuwa da su.
Gwamnan, ya ce matsalar tsaro na hana samar da manyan ayyukan ci gaba a yankin.
Ya kuma sake alƙawarin gina makarantu, asibiti, hanyoyi, cibiyar kwamfuta, cibiyar JAMB da kuma Kwaleji a Uba.
“Ziyarar na zo ne don duba yanayin tsaro. Zan gana da jami’an tsaro domin tabbatar da Askira/Uba sun samu kariya.
“Ba za a samu zaman lafiya ba idan babu tsaro. Muna da shirin samar da hanyoyi, ilimi da kiwon lafiya,” in ji Zulum.
Sarkin ya gode wa gwamnan; “Ka yi mana abubuwa da dama. Da doka za ta ba da dama, da mun roƙe ka, ka ci gaba da mulki. Allah Ya yi maka albarka.”