Masu Tasiri a Kafafen Sada Zumunta sun samu horo kan RMNCAH+N, Tsarin Iyali da Rigakafin Cin Zarafin Mata
Published: 23rd, October 2025 GMT
Ƙungiyar Centre for Communication and Social Impact (CCSI) tare da haɗin gwiwar abokan aikin ta na EngenderHealth Consortium sun shirya taron horo na yini ɗaya a Kano domin ƙarfafa ƙwarewar ’yan jarida da masu tasiri a kafafen sada zumunta (social media influencers) wajen yada sahihan bayanai da tallafawa manufofin kiwon lafiya da daidaito tsakanin jinsi.
Taron, mai taken “Daga Masu Bi zuwa Masu Faɗa Aji: Amfani da Kafafen Sada Zumunta wajen Yaɗa Sawun Lafiya da Daidaito”, ya mayar da hankali ne kan batutuwan Reproductive, Maternal, Newborn, Child, and Adolescent Health plus Nutrition (RMNCAH+N), Family Planning (FP), da Gender, Youth, and Social Inclusion (GYSI).
Manufar wannan horo ita ce canza masu tasiri a kafafen sada zumunta zuwa ƙwararrun masu fafutukar yaɗa ilimin lafiya da canjin halayyar jama’a ta hanyar amfani da hujjoji, ladabi, da al’adun da suka dace da al’umma.
A jawabinsa na budewa, Atiku Muhammad Auwal, Manajan Ayyukan Wayar da Kai na CCSI, ya bayyana cewa manufar taron ita ce samar wa masu tasiri a kafafen sada zumunta da ilimi da dabaru domin su zama masu faɗakarwa kan batutuwan RMNCAH+N, Tsarin Iyali, da Daidaito tsakanin jinsi.
Ya ce, horon zai taimaka musu wajen jan hankalin gwamnati da al’umma kan muhimman batutuwan lafiyar jama’a ta hanyar ingantacciyar fafutuka.
“Ta hanyar koyarwa daga masana da atisayen aiki, mahalarta sun koyi dabarun ƙirƙirar abun ciki na dijital mai tasiri, gaskiya, da tausayi ga waɗanda abin ya shafa, tare da hanyoyin yaki da labaran ƙarya da ƙarfafa tattaunawa mai haɗin kai,” in ji shi.
A cikin gabatarwarta mai taken “Matsayin RMNCAH+N, FP da GBV a Jihar Kano da rawar da masu tasiri ke takawa wajen kawo sauyi”, Dr. Mansurah, mai kula da shirye-shiryen Maternal, Newborn and Child Health (MNCH) a jihar, ta bayyana manyan ƙalubale da ke fuskantar sashen lafiya a Kano.
Ta ambaci matsalolin kamar rashin daidaiton rarraba cibiyoyin lafiya (PHCs), ƙarancin ƙwararrun ma’aikatan haihuwa, gibin kayan aiki da gini, ƙarancin kayan lafiya, ƙarancin kwarin gwiwar ma’aikata, raunin tsarin bayanai, da kuma rashin haɗin kan al’umma.
Shi kuwa Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Ƴan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen Kano, Kwamared Mustapha Gambo Muhammad, ya jaddada cewa NUJ na gaba-gaba wajen yaƙi da cin zarafin mata da inganta ilimin lafiya, tsare iyali, da daidaito tsakanin jinsi.
Ya tabbatar da kudirin ƙungiyar wajen ci gaba da wayar da kai ta hanyar kafafen sada zumunta da rahotanni masu inganci.
A nata jawabin, Khadijah Abdullahi Yahaya daga Arewa Radio, ta jaddada rawar da masu tasiri da kafafen watsa labarai ke takawa wajen tallafawa shirye-shiryen tsare iyali da RMNCAH+N.
Ta yi kira da a ƙara haɗin kai da bayar da dama ga jama’a su rika bayyana irin ƙalubalen da suke fuskanta a cikin al’ummarsu.
Taron ya ƙunshi gabatarwa masu mu’amala, tambayoyi da amsoshi tare da masana lafiya, da damar haɗa kai tsakanin masu tasiri, ’yan jarida, da masu ruwa da tsaki a harkokin lafiya.
Khadijah Aliyu
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Na kashe N100bn a kan harkar tsaro a 2025 — Zulum
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce gwamnatinsa ta kashe kusan Naira biliyan 100 a wannan shekara domin inganta tsaro a faɗin jihar.
Ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci Sarkin Uba, inda ya yi masa jaje kan hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutane da dama.
Jami’an tsaro sun kama masu garkuwa da mutane 7 a Gombe Najeriya ta shigo da tataccen man fetur na tiriliyan 12.8 cikin watanni 15Zulum ya yaba wa jami’an tsaro da al’umma kan ceto manoman mata 12 da aka yi garkuwa da su.
Gwamnan, ya ce matsalar tsaro na hana samar da manyan ayyukan ci gaba a yankin.
Ya kuma sake alƙawarin gina makarantu, asibiti, hanyoyi, cibiyar kwamfuta, cibiyar JAMB da kuma Kwaleji a Uba.
“Ziyarar na zo ne don duba yanayin tsaro. Zan gana da jami’an tsaro domin tabbatar da Askira/Uba sun samu kariya.
“Ba za a samu zaman lafiya ba idan babu tsaro. Muna da shirin samar da hanyoyi, ilimi da kiwon lafiya,” in ji Zulum.
Sarkin ya gode wa gwamnan; “Ka yi mana abubuwa da dama. Da doka za ta ba da dama, da mun roƙe ka, ka ci gaba da mulki. Allah Ya yi maka albarka.”