Shugaba Tinubu Ya Taya Super Eagles Murnar Samun Cancantar Shiga Gasar Kwallon Kafa Ta Duniya
Published: 15th, October 2025 GMT
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya kungiyar kwallon kafa ta kasaSuper Eagles murnar nasarar da suka samu ta ci 4 da nema a kan Cheetahs ta Jamhuriyar Benin, tare da yabawa ƙungiyar bisa ƙoƙarin da take yi na ci gaba da kokarin cika al’umma, yayin da suke neman cancantar zuwa gasar cin Kofin Duniya ta FIFA a shekarar 2026.
Shugaban ƙasar ya jinjina wa Super Eagles bisa ƙwazo, da jajircewar da suka nuna a filin wasa na Uyo, yana mai cewa wannan gagarumar nasarar ta sake karfafa ‘yan Najeriya kan harkar ƙwallon ƙafa.
“Yanayin farin ciki da ake ciki a fadin ƙasar nan na nuni da yakinin da muke da shi cewa Najeriya ta cancanci samun gurbi a gasar Kofin Duniya ta 2026, wadda Kanada, da Mexico, da Amurka za su karɓi bakunci.”
“A matsayina na Shugaban ƙasa, ina tabbatar muku da cikakken goyon bayan Gwamnatin Tarayya, yayin da kuke ƙoƙarin tabbatar da gurbin ku a gasar.
Hakazalika ‘yan Najeriya na da yakinin cewa za ku yi nasara, ni ma haka.”
“Muna sa ran ganin ku kuna daga tutar Najeriya cikin alfahari a matakin duniya.” Inji Shi.
Daga Bello Wakili
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU ta Shiga Yajin Aiki
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya ASUU a ranar Lahadi ta sanar da shiga yajin aiki na makonni biyu, wanda zai kasance cikakke kuma gaba ɗaya, a duka jami’o’in gwamnati na ƙasar.
Shugaban ƙungiyar Farfesa Chris Piwuna ne ya sanar da hakan a lokacin wani taron manema labarai da aka gudanar a Jami’ar Abuja, a ranar Lahadi.
Asuu ta ce yajin aikin na gargaɗi ne bayan cikar wa’adin da suka bai wa gwamnatin Najeriya a watan Satumban da ya gabata.
“Yajin aikin gargadin zai kasance cikakke kuma gaba ɗaya, kamar yadda aka amince a taron NEC na ƙarshe,” kamar yadda Piwuna ya bayyana.
RN