Bahrain: Fursunoni 90 Suna Yajin Cin Abinci Saboda Neman ‘Yanci
Published: 26th, October 2025 GMT
Wani rahoto na kafar watsa labarun Birtaniya ya bayyana cewa; Da akwai fiye da fursunoni 90 da suke yajin cin abinci a gidan kurkukun kasar Bahrain suna neman a sake su.
Rahoton ya kuma ce, mafi yawancin fursunonin da suke yajin cin abincin suna babban gidan yarin kasar ne, kuma an kama su da yi musu hukunci ne bisa dalilai na siyasa.
Wannan dai ba shi ne karon farko ba da fursunoni a kasar Bahrain suke yajin cin abinci bisa nema a kyautata yanayin rayuwarsu a inda ake tsare da su, ko kuma neman a sake su ba tare da wani sharadi ba.
Wani sauti na daya daga cikin fursunonin da aka dano daga cikin gidan kurkuku, ya bayyana cewa; Sun fara yajin cin abincin ne dai tun 6 ga watan Oktoba, bayan da su ka aike da wasika zuwa ga jami’an gidan yarin suna neman ‘yancinsu.
Haka nan kuma ya ce; Bayan da aka yi watsi da bukatunsu, sun yanke shawarar fadawa cikin yajin cin abinci da ta fara daga kin karbar Karin kumallo, daga nan kuma sai abincin dare. Daga ranar 14 ga watan Oktoba, fursunonin sun yanke shawarar fadawa cikin yajin cin abinci baki daya.
Da akwai daruruwan fursunonin siyasa a kasar Bahrain da aka daure saboda kiran a samar da sauyin siyasa a kasar.
Bahrain tana bin mulkin mulukiya ne da sarki yake da wuka da nama, ba tare da dokokin da su kayyade aikinsa ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shugaban Kasar Nigeria Ya Yi Sauye-sauye A Rundunonin Sojan Kasar October 26, 2025 Iran Ta Ki Zuwa Taron Sherme-Sheikh Ne Saboda Kar Ta Zama Mai Shaidar Zur Akan Kisan Kiyashin Gaza October 26, 2025 Jami’ar ABU Ta Karyata Zargin Da Ake yi Na Kera Makamin Nukiliya A Asirce October 25, 2025 M D D Ta ce Akalla Mutane miliyan 1.5 Ne Ke Bukatar Taimakon Gaggawa A Gaza October 25, 2025 Tony Balai Na Fuskantar Turjiyar Kasashen Larabawa Game Da Rawar Da Zai Taka A Gaza. October 25, 2025 Yau Ne Ake Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa A Ivory Coast October 25, 2025 Iran Za ta Karbi Bakunci Taron Ministocin Cikin Gida Na Kungiyar ECO October 25, 2025 Jakadan Iran A Majalisar Dinkin Duniya Ya Yi Kiran Da A Nisanci Siyasantar Da Kwamitin Tsaron Majalisar October 25, 2025 Tsohon Shugaban Hukumar Leken Asirin Dakarun IRGC Ya Ce: Yakin Kwanaki 12 Kan Iran Ya Canza Tunanin Makiya October 25, 2025 Rear Admiral Sayyari: Sojojin Iran A Shirye Suke Su Fuskanci Kowace Barazana October 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: yajin cin abinci
এছাড়াও পড়ুন:
Yau Ne Ake Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa A Ivory Coast
A yau Asabar al’ummar kasar Ivory Coast ke zaben shugaban kasa wanda ya raba kan kasar inda wasu ke son shugaba Alassane Ouattara ya yi tazarce, wasu kuma na ganin lokaci ne na samar da sabon shugabanci a kasar.
Fargaba ta karu sosai tun bayan cire manyan ‘yan takara biyu na jam’iyyun hamayya – wato tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo da Tidjane Thiam, wani kusa a fagen siyasa kuma abokin kawancen Ouattara kafin ya zama abokin hamayya.
Rahotanni sun ce Shugaba Ouattara ya yi kira ga magoya bayansa su fito su zabe shi duk da yan kasar da dama na tunanin shi zai lashe zaben, kafin zaben an samu rikici a sassan kasar da dama inda aka kama daruruwan mutane .
Alassane Ouattara mai shekara 83 yana takara ne domin neman mulkin kasar a zango na hudu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Za ta Karbi Bakunci Taron Ministocin Cikin Gida Na Kungiyar ECO October 25, 2025 Jakadan Iran A Majalisar Dinkin Duniya Ya Yi Kiran Da A Nisanci Siyasantar Da Kwamitin Tsaron Majalisar October 25, 2025 Tsohon Shugaban Hukumar Leken Asirin Dakarun IRGC Ya Ce: Yakin Kwanaki 12 Kan Iran Ya Canza Tunanin Makiya October 25, 2025 Rear Admiral Sayyari: Sojojin Iran A Shirye Suke Su Fuskanci Kowace Barazana October 25, 2025 Shugaban Kasar Venezuela Ya Ce; Amurka Tana Son Kaddamar Da Yaki Kan Kasarsa October 25, 2025 Bangarorin Falasdinawa Sun Amince Da Shirin Gudanar Da Zirin Gaza Nan Gaba October 25, 2025 Nawwafa Salam: Yin Mu’amalar Diplomasiyya Da “Isra’ila” Ba Shi Alfanu October 25, 2025 Shugaban Kasar Columbia Ya Yi Watsi Da Takunkumin Da Amurka Ta Kakaba Masa October 25, 2025 Kungiyar Kwallon Kafa Ta Futsal Ta Matan Iran Sun Sami Nasara Akan Kasar Bahrain October 25, 2025 Antonio Gutrress: MDD Tana Bukatuwa Da A Yi Ma Ta Kwaskwarima October 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci