Shugaban Kasar Nigeria Ya Yi Sauye-sauye A Rundunonin Sojan Kasar
Published: 26th, October 2025 GMT
Kafar watsa labaru ta “Afircanews” ta bayyana cewa, babu wani cikakken dalili da aka gabatar dangane da sauye-sauyen, tare da kuma kore jita-jitar da aka rika watsawa akan yunkurin juyin Mulki a kasar a watan Satumba, dda ya kai ga tsare sojoji 20 daga ciki har da Birgediya janar da kuma kanar.
Mai Magana da yawun shugaban kasar ta Nigeria, ya bayyana cewa; shugaba Ahamd Tinubu ya salami manyan jami’an sojoji da su ka hada babban hafsan hafsoshi Emmanuel Ogalla, shugaban sojan ruwa, da Hassan Abubakar, shugaban sojan sama.
Shugaba Ahmad Tinubu ya nada Olufemi Oluyedi, tsohon hafsan hafsoshin soja a matsayin sabon ministan tsaro.
Sabon shugaban sojan kasa shi ne Manjo janar W. Shaibu
Shugaban sojan Sama kuma shi ne S.K Akene
Sabon shugaban sojan ruwa kuwa shi ne Rear Admiral I. Abbas
Tare da cewa babbar shalkwatar sojojin kasar ta Nigeria a Abuja, ta kore jita-jitar juyin Mulki sai dai haka bai kawar da tsoro a tsakanin ‘yan kasa ba.
Wani dan majalisar dattijai Sanata Irogebu ya ce da alama hukuma tana Fifita bai wa kanta kariya ne, fiye da sauran barazanar tsaro da ake fuskanta.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta Ki Zuwa Taron Sherme-Sheikh Ne Saboda Kar Ta Zama Mai Shaidar Zur Akan Kisan Kiyashin Gaza October 26, 2025 Jami’ar ABU Ta Karyata Zargin Da Ake yi Na Kera Makamin Nukiliya A Asirce October 25, 2025 M D D Ta ce Akalla Mutane miliyan 1.5 Ne Ke Bukatar Taimakon Gaggawa A Gaza October 25, 2025 Tony Balai Na Fuskantar Turjiyar Kasashen Larabawa Game Da Rawar Da Zai Taka A Gaza. October 25, 2025 Yau Ne Ake Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa A Ivory Coast October 25, 2025 Iran Za ta Karbi Bakunci Taron Ministocin Cikin Gida Na Kungiyar ECO October 25, 2025 Jakadan Iran A Majalisar Dinkin Duniya Ya Yi Kiran Da A Nisanci Siyasantar Da Kwamitin Tsaron Majalisar October 25, 2025 Tsohon Shugaban Hukumar Leken Asirin Dakarun IRGC Ya Ce: Yakin Kwanaki 12 Kan Iran Ya Canza Tunanin Makiya October 25, 2025 Rear Admiral Sayyari: Sojojin Iran A Shirye Suke Su Fuskanci Kowace Barazana October 25, 2025 Shugaban Kasar Venezuela Ya Ce; Amurka Tana Son Kaddamar Da Yaki Kan Kasarsa October 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Antonio Gutrress: MDD Tana Bukatuwa Da A Yi Ma Ta Kwaskwarima
Babban magatakardar MDD Antonio Gutrress ya bayyana cewa majalisar tana da bukatuwa da a yi kwaskwarima da gyare-gyare.
Gutrress dai ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabin cika shekaru 80 da kafuwar MDD.
Gutrress ya kuma ce, tare da cewa ayyukan da Majalisar take aiwatarsa suna da matukar muhimmanci,amma kuma halarcinta yana tangal-tangal, sannan kuma ya kara da cewa an dade ana sauraron a yi ma ta kwaskwarima.
A wani sashe na jawabin nashi, ya zargi wasu daga cikin mambobin MDD da cewa a lokuta da dama suna yin abubuwan da suke cin karo da dokokin majalisar, da hakan yake sa ake yin shakku akan ita kanta majalisar ta dinkin duniya.
Har ila yau, Guterres ya ce; Majalisar Dinkin Duniya ba aikinta mamaya ba, kuma ba mallakin wata daula ba ce, tare da yin kira da gyara gibin da ake samu na kasafin kudi.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Lebanon: An Sami Shahidai 3 Sanadiyyar Hare-haren HKI A Kudancin Lebanon October 25, 2025 Iran Ta Yi Allah Wadai Da Hare-Haren Isra’ila Kan Kasar Lebanon October 24, 2025 Rasha Ta Jaddada Cewa: Kasashen Turai Sun Taka Doka Kan Batun Makamashin Nukiliyar Iran October 24, 2025 Ayatullahi Khatami Ya Ce: Shugaban Kasar Amurka Trump Dan Ta’adda Ne October 24, 2025 Shugaban Amurka Ya Ce: Za Su Dauki Matakin Soji Kan Kasar Venezuela Nan Gaba Kadan October 24, 2025 Gwamnatin Iraki Ta Yi Allah Wadai Da Mamaye Yankin Yammacin Kogin Jordan Na Falasdinu October 24, 2025 ‘Yan Sandan Kasar Ghana Sun Tseratar Da ‘Yan Najeriya 57 Da Aka Yi Fasakwaurinsu October 24, 2025 Trump Ya Dakatar Da Tattaunawar Kasuwanci Da Kasar Canada October 24, 2025 Gaza: Tasirin Rashin Abinci Mai Gina Jiki Da Magani Zai Ci Gaba Har Zuriya Mai Zuwa October 24, 2025 Iran Ta Lashe Kambun Duniya Na Kokawar Gargajiya October 24, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci