Gwamnatin Nijar Ta Yaye Tsofaffin Mayaka 369 Da Aka Bai Wa Horon Sauya Tunani
Published: 19th, October 2025 GMT
A ta bakin shugaban bikin, kuma gwamnan Jihar Tillabery Maina Boukar, taron na wannan karo ya shaida aniyar gwamnatin Nijar, ta bai wa wadanda suka rungumi shirin ajiye makamai damar sauya rayuwarsu, da taimaka musu wajen cimma nasarar komawa cikin al’umma cikin mutunci.
Boukar ya ce, “Wannan muhimmin zabi, ya nuna aniyar gwamnatin Nijar ta kare ikon mulkin kai, da wanzar da tsaro, da tabbatar da zaman lafiya karkashin kyawawan manufofin kasa, ba tare da dogaro ga wasu ajandoji daga ketare ba.
এছাড়াও পড়ুন:
Mutane 9,854 na ɗauke da cutar AIDS a Yobe
Gwamnatin Yobe ta bayyana cewa aƙalla mutane 9,854 ne ke ɗauke da cutar AIDS a jihar, kuma dukkaninsu na karɓar maganin ceton rai.
Hukumar ta tabbatar da cewa waɗannan marasa lafiya suna rayuwa cikin ƙoshin lafiya, tare da rage yiwuwar yaɗa cutar ga wasu.
Babban Daraktan Hukumar Kula da Cutar AIDS ta Jihar Yobe (YOSACA), Dakta Jibril Adamu Damazai, ne ya bayyana cewa Yobe na da mafi ƙarancin adadin masu ɗauke da cutar a ƙasar nan da kashi 0.4%, inda ya danganta hakan da dabarun yaƙi da cutar da ake aiwatarwa a jihar.
“Ba mu tsaya a kan wannan nasara ba, muna ƙara ƙoƙari don rage yawan kamuwa da cutar,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta kashe sama da Naira miliyan 120 wajen sayen kayan gwaji, abin da ya bai wa ƙungiyoyi damar gano mutanen da ba a san suna ɗauke da cutar ba a cikin al’umma, domin a ba su magani.
A cewarsa, Yobe na kan gaba wajen daidaita dabarun yaƙi da cutar AIDS, musamman ganin yadda ake samun sauye-sauye a kuɗaɗen da ake kashewa a duniya.
Dakta Damazai ya kuma bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta fara shirye-shiryen samar da magungunan ƙwayar cutar HIV a cikin gida.
Ya yaba da jajircewar gwamna Mai Mala Buni, wanda ya ƙara kuɗaɗen da ake bai wa hukumar kula da cutar AIDS da kashi 400%, tare da samar da katafaren ofis na dindindin ga hukumar.