Ya bayyana cewa sarakuna suna taka muhimmiyar rawa wajen kawo ci gaba, musamman a fannin ilimi, inda ya ce zai tabbatar yara sun koma makaranta.

Haka kuma, ya ce zai goyi bayan gwamnati a ɓangaren kiwon lafiya da tsaro, domin inganta rayuwar jama’a.

Sabon Sarkin, wanda kuma shi ne shugaban hukumar kula da ilimi a matakin farko (SUBEB) ta Jihar Bauchi, ya bayyana farin cikinsa da godiyarsa ga Allah da Gwamna Bala Muhammad saboda wannan dama da ya samu.

Ya yi alƙawarin yin aiki tuƙuru domin ci gaban masarautarsa da Jihar Bauchi gaba ɗaya, tare da kira ga jama’ar Duguri da su haɗa kai wajen gina masarautar.

“Mu mutanen Duguri a shirye muke mu taimaka wa gwamnati a duk abin da ta ce. Za mu tura yara makaranta, za mu karɓi rigakafi, kuma za mu ci gaba da zaman lafiya da maƙwabtanmu. Muna godiya sosai ga Gwamna Bala Muhammad bisa wannan dama,” in ji Sarki Adamu.

Sarkin ya bai wa Gwamnan Bauchi sarautar ‘Yariman Duguri.

Da yake miƙa takardar naɗin sarautar, Sakataren Gwamnatin Jihar Bauchi, Aminu Hammayo, ya ce Gwamna Bala Muhammad ya yi amfani da dokar masarautu ta shekarar 2025, musamman sashe na 16 da 17, wajen tabbatar da wannan naɗi.

Ya tunatar da sabon Sarki da ya tafiyar da harkokin masarautar bisa kundin tsarin mulkin ƙasa, dokokin Jihar Bauchi, da umarnin gwamnati, tare da tabbatar da adalci da gaskiya a shugabancinsa.

Gwamnan ya yi fatan sabon Sarkin zai jagoranci masarautar cikin zaman lafiya, haɗin kai, da samar wa al’ummar Duguri da Bauchi ci gaba.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamnatin Kaduna Ta Gano Ma’adanin Zinari Da Tagulla Da Za Su Haɓaka Tattalin Arziƙin Jihar October 24, 2025 Labarai Gwamnatin Katsina Ta Ƙara Samar Da Dakarun Tsaro 200 Domin Maganace Ta’addanci October 24, 2025 Manyan Labarai Gwamnan Bauchi Ya Naɗa Yayansa A Matsayin Sabon Sarkin Duguri October 24, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Jihar Bauchi

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Kaduna Ta Gano Ma’adanin Zinari Da Tagulla Da Za Su Haɓaka Tattalin Arziƙin Jihar

Ya ce Hukumar Binciken Ƙasa ta Nijeriya (NGSA) za ta jagoranci kwamitin, domin ita ce ke da ikon tattara bayanan ma’adinai na ƙasa baki ɗaya.

 “NGSA ta yaba da ƙoƙarin gwamnatin Jihar Kaduna bisa gaskiya da bayyana bayanai, tare da yin kira da a gudanar da binciken tabbatarwa mai zaman kansa,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa wannan haɗin gwiwar zai ƙara goyon bayan masu zuba jari a sashen ma’adinai na Nijeriya, tare da faɗaɗa bayanan kimiyyar ƙasa, wanda zai taimaka wajen haɓɓaka tattalin arzikin ƙasa ta hanyar albarkatun ma’adananta.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamnan Bauchi Ya Naɗa Yayansa A Matsayin Sabon Sarkin Duguri October 24, 2025 Manyan Labarai Tinubu Ya Sauya Hafsoshin Tsaron Nijeriya October 24, 2025 Manyan Labarai Ƴansanda Sun Sake Kama Sowore Bayan An Bayar Da Belinsa October 24, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Kaduna Ta Gano Ma’adanin Zinari Da Tagulla Da Za Su Haɓaka Tattalin Arziƙin Jihar
  • Gwamnan Bauchi ya naɗa ɗan uwansa a matsayin sabon Sarkin Duguri
  • Gwamnan Bauchi Ya Naɗa Yayansa A Matsayin Sabon Sarkin Duguri
  • Ƙungiyoyin Ma’aikatan Jihar Kaduna Sun Yabawa Gwamna Sani Kan Amincewa Da Sabon Albashin  Ma’aikata
  • Dauda Lawal Gwarzon Gwamnan 2025: Ceto Zamfara Domin Ci Gaba
  • Dauda Lawal: Ceto Zamfara Domin Ci Gaba
  • Tinubu ya bukaci sabon shugaban INEC ya gudanar da zaben gaskiya a 2027
  • Tinubu Ya Rantsar Da Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC
  • Nesa Ta Zo Kusa: Maraba Da Sabon Jirgin Kasa Samfurin CR450 Da Kasar Sin Ta Kera