Tony Balai Na Fuskantar Turjiyar Kasashen Larabawa Game Da Rawar Da Zai Taka A Gaza.
Published: 25th, October 2025 GMT
Matakatin shugaban Amurka Donald Trump na nada tsohon fira ministan birtaniya Tony Blair a matsayin mai ruwa da tsaki cikin alamuran gaza bayan dakatar da bude wuta ya fuskancin turjiya daga kasashen larabawa da kuma na musulmi, Balair shi ne mutum daya da aka ayyana sunansa daga cikin mambobin kwamitin tabbatar da sulhu da trump ya bada shawara na sanya ido bayan kawo karshen yaki tsakanin bangarorin biyu.
Akwai damuwa sosai da shakku kan kasancewar Blair daga cikin masu ruwa da tsaki a alamuran yankin, musamman bayan goyon bayan da ya nuna wajen kai wa iraki hari tare da tsohon shugaban Amurka na wancan lokacin a shekara ta 2003 ,a gefe daya kuma yana kare Isra’ila, jamai’an diplomasiyan larabawa sun nuna damuwa sosai inda suke ganin shigar da blair cikin lamarin zai raunana matsayin falasdinu, kuma zai kara dagula kokarin samar da zaman lafiya a Gaza,
Jami’an diplomasiyar kasashen larabawa 3 sun bayyana wa jaridar financial times cewa nada blair da aka yi ya dauki hankali sosai, da kuma yadda aka ajiye falasdinawa a gefe, ana son sake dawo da wani nau’in mulkin mallaka ta wani sabon salo,
Wasu kasashen larabawa da na musulmi ciki har da Saudi arebiya, masar, jodan, turkiya da kuma kasar Indonesia an tuntubesu game da shirin kuma ana fatan za su bada gudunmawar dakaru da kuma shirin sake gina yankin gaza , sai dai dama daga cikinsu suna ci gaba da nuna shakku kan mambobin kwamitin zaman lafiya musamman kasancewar blair a ciki, da suke ganin haka zai kawo cikas wajen aiwatar da shirin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Yau Ne Ake Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa A Ivory Coast October 25, 2025 Iran Za ta Karbi Bakunci Taron Ministocin Cikin Gida Na Kungiyar ECO October 25, 2025 Jakadan Iran A Majalisar Dinkin Duniya Ya Yi Kiran Da A Nisanci Siyasantar Da Kwamitin Tsaron Majalisar October 25, 2025 Tsohon Shugaban Hukumar Leken Asirin Dakarun IRGC Ya Ce: Yakin Kwanaki 12 Kan Iran Ya Canza Tunanin Makiya October 25, 2025 Rear Admiral Sayyari: Sojojin Iran A Shirye Suke Su Fuskanci Kowace Barazana October 25, 2025 Shugaban Kasar Venezuela Ya Ce; Amurka Tana Son Kaddamar Da Yaki Kan Kasarsa October 25, 2025 Bangarorin Falasdinawa Sun Amince Da Shirin Gudanar Da Zirin Gaza Nan Gaba October 25, 2025 Nawwafa Salam: Yin Mu’amalar Diplomasiyya Da “Isra’ila” Ba Shi Alfanu October 25, 2025 Shugaban Kasar Columbia Ya Yi Watsi Da Takunkumin Da Amurka Ta Kakaba Masa October 25, 2025 Kungiyar Kwallon Kafa Ta Futsal Ta Matan Iran Sun Sami Nasara Akan Kasar Bahrain October 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An Fito Da Gawawwakin Shahidai 98 Da Aka Binne Cikin Gaggawa A Asibitin “Ash-Shifa”
Masu aikin ceto a Falasdinu, sun fada a ranar Litinin din da ta gabata cewa; An fito da gawawwakin shahidai 98 da aka binne su cikin gaggawa a lokacin yaki, a cikin harabar asibitin al-Shifa a cikin birnin Gaza.
An fito da gawawwakin ne dai domin kai su zuwa sanannun makabartun da ake da su a cikin yankin na Gaza,domin binnewa.
Sanarwar hukumar ceton ta ce; A tsakanin shahidan da akwai wasu 55 da ba iya tantance ko su wanene ba, sai dai an mika su ga kwararrun likitoci domin tantance da gano ko su wanene.
Ma’aikatan agaji suna ci gaba da fito da wasu gawawwakin na shahidai da aka binne a cikin asibitin, domin tantance su, kuma ana yin hakan ne dai a cikin kare hurumin matattun.
A farko-farkon kwanakin yakin Gaza, sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila, sun kai hari akan wannan asibitin, wanda ya yi sanadiyyar shahadar mutane 500 a lokaci daya.
A wani labarin na daban, ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta sanar da cewa; A cikin sa’oi 24 da su ka gabata an kai gawawwakin shahidai 5, uku daga cikinsu sun kwanta dama ne sanadiyyar sabbin hare-haren da sojojin mamaya suke kai wa, duk da cewa an tsagaita wutar yaki. Sauran shahidan biyu kuwa wadanda aka fito da su ne daga karkashin baraguzai na gine-ginen da ‘yan sahayoniya su ka rusa gidaje da mutane a cikinsu a tsawon ranakun yaki.
Ma’aikatar kiwon lafiyar ta Gaza ta kuma ce, har yanzu da kawai adadi mai yawa na shahidai da suke a karkashin baraguzai, ana kuma samun jinkirin fito da su ne saboda rashin kayan aiki.
Daga tsagaita wutar yaki a ranar 11 ga watan Oktoba 2025 zuwa yanzu adadin wadanda su ka yi shahada sun kai 376, wadanda su ka jikkata kuwa sun kai 981. Haka nan kuma an tono gawawwakin shahidai 626.
Idan aka koma zuwa Oktoba na 2023 kuwa, to adadin shahidan Falasdinawa ya kai 70,365, wadanda su ka jikkata kuwa sun kai 171,058.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Talauci Yana Karuwa A “Isra’ila” Bayan 7 Ga Watan Oktoba December 9, 2025 AU Ta yi Tir Da Harin RSF A Makarantar Kananan Yara Da Ya Kashe Mutane 80 December 8, 2025 MِِِِDD: Kisan Kare Dangin Da Isra’ila Ta yi A Gaza Shi Ne Farko Da Yafi Jan Hankalin duniya December 8, 2025 Iran Da Azarbaijan Sun Amince Da Ci Gaba Da Tuntubar Juna Domin Warware Matsaloli December 8, 2025 Iran Da Kasashen Afrika Sun Daura Dammarar Karfafa Alakar Kimiyya Tsakaninsu December 8, 2025 Ecowas Ta Tura Sojoji Zuwa Jamhuriyar Benin Don Dakile Juyin Mulki December 8, 2025 IRGC: Makaman Iran Sun Fada Kan Matatan Man Haifa Har Sau Biyu A Yakin Kwanaki 12 December 8, 2025 Najeriya: Gwamnatin Tarayya Ta Bada Sanarwan Kubutar Da Yan Makaranta 100 Da Aka Sace December 8, 2025 Iraki Ta Musanta Cewa Ta Tushe Asusun Hizbullah Da Ansarallah December 8, 2025 Sabon Fada Ya Barke A Tsakanin Thailand Da Cambodia December 8, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci