Ko Alassane Ouattara zai samu wa’adi na 4 a mulkin Ivory Coast?
Published: 23rd, October 2025 GMT
Shugaban ƙasa mai ci, Alassane Ouattara, shi ne wanda aka fi yi wa hasashen nasara a zaɓen da za a gudanar a Ivory Coast ranar Asabar, sakamakon rashin wasu jiga-jigan ’yan adawa da za a fafata da su a zaɓen.
Ouattara, mai shekara 83, yana riƙe da madafun iko tun daga shekarar 2011, lokacin da ƙasar ta fara warwarewa daga rikicin siyasa kuma ta kasance ɗaya daga cikin manyan ƙasashen da ke taka rawa wajen bunƙasar tattalin arzikin yammacin Afirka.
A ƙarƙashin mulkinsa, Ivory Coast — wacce ita ce babbar mai fitar da koko a duniya — ta samu ci gaba a fannoni da dama, kodayake masu suka na ganin tsawon lokacin da ya shafe a karagar mulki na iya ƙara raba kawunan ’yan ƙasar.
Alassane Ouattara na da damar samun tazarce, a yayin da manyan abokan hamayyarsa ciki har da tsohon shugaban ƙasa Laurent Gbagbo da tsohon shugaban bankin Credit Suisse, Tidjane Thiam — duka an hana su tsayawa takara.
A halin yanzu dai ‘yan adawa huɗu Majalisar Tsarin Mulki ta sahalewa takara, inda ta cire Gbagbo da Thiam daga jerin ’yan takarar tana mai ba da dalilin cewa an goge sunayensu daga rajistar zaɓe.
Bayanai sun ce an hana Thiam tsayawa takara ne saboda matsalolin shari’a da suka shafi batun ƙasa da ƙasa, musamman kan yadda ya samu shaidar zama ɗan ƙasar Faransa a matsayin ƙasarsa ta biyu.
A gefe guda kuma, Gbagbo an hana shi shiga takara ne saboda hukuncin da aka taɓa yanke masa a kotu.
A ranar Laraba, Gbagbo ya soki zaɓen da ke tafe yana mai bayyana shi a matsayin “juyin mulki na farar hula” da kuma “satar zaɓe.”
Da yake magana da gidan jaridar AFO Media na Pan-Afirka, tsohon shugaban ƙasa Laurent Gbagbo ya bayyana goyon bayansa ga masu zanga-zangar da ke “adawa da wannan satar zaɓen.”
Rashin halartar fitattun shugabannin adawa irin su Gbagbo da Tidjane Thiam ya ƙara tayar da ƙura a harkar siyasar ƙasar, lamarin da ya jawo tashin hankalin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane huɗu ’yan kwanakin nan — ciki har da ɗan sanda ɗaya.
Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP ya ruwaito cewa, a ranar Talatar da ta gabata ce wani mutum ya rasa ransa yayin da yake taimaka wa jami’an tsaro rushe shingayen da aka kafa a kusa da birnin Yamoussoukro, babban birnin mulkin ƙasa, wanda ke zama cibiya mai ƙarfi ga ’yan adawa.
A wannan yankin dai an toshe hanyoyi da dama yayin da yanayin siyasa ke ƙara ɗaukar zafi gabanin zaɓen da ke tafe.
Haka kuma, a ranar Litinin ce aka ƙone wani ginin hukumar zabe mai zaman kanta ƙurmus, inda tuni mahukunta suka hana ’yan adawa gudanar da gangami ko taruka, suna cewa hakan na iya barazana ga tsaron jama’a.
Haramta GangamiAƙalla jami’an tsaron ko ta kwana 44,000 aka jibge a fadin ƙasar domin daƙile yiwuwar ɓarkewar zanga-zanga, musamman a yankunan kudu da yammacin ƙasar da ake ganin su ne cibiyoyin magoya bayan adawa.
A cikin ’yan makonnin nan, sama da mutane 700 aka kama, wasu bisa zargin aikata “ta’addanci,” a cewar lauyan gwamnati Oumar Braman Koné, yayin da kusan mutum 30 aka yanke musu hukuncin shekaru uku a gidan yari saboda ta da zaune tsaye da karya doka.
Hukumomin ƙasar sun bayyana cewa ba za su bari “rikici” ya sake faruwa kamar yadda aka gani a zaɓen shekarar 2020, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 85.
“Gwamnati tana ɗaukar matakan tsaro na kariya don kauce wa tashin hankali a lokacin zaɓe. Amma hanya mafi inganci ta gudanar da zaɓe cikin lumana ita ce a shirya zaɓen da ya haɗa kowa,” in ji masanin siyasa Geoffroy Kouao.
’Yan adawa 4 da za su ƙalubalanci OuattaraGuda cikin ’yan takarar da ake ganin za su ƙalubalanci Ouattara a zaɓen na ranar 25 ga wata akwai Simone Gbagbo mai shekaru 76, wato tsohuwar matar tsohon shugaba Laurent Gbagbo, wanda ya jagoranci ƙasar a lokacin yaƙin basasar da ya faru tsakanin shekarar 2002 zuwa 2007.
Simone tana tare da Gbagbo lokacin da ya ƙi sauka daga mulkin ƙasar bayan shan kaye a zaɓen 2010, wanda ya kai ga rikicin da ya sabbaba mutuwar mutane aƙalla dubu 3, gabanin kame Simone da Gbagbo cikin watan Afrilun 2011 tare da gurfanar da su gaban kotun hukunta manyan laifuka ta ICC.
Sai dai Simone ta samu sassauci ganin cewa an yi mata shari’a ne a cikin gida ba tare da zuwa Hague ba, saɓanin mijin nata, inda aka yanke mata hukuncin shekaru 20 a gidan yari gabanin afuwar da shugaba Ouattara ya yi mata a shekarar 2018, inda a shekarar 2023 kuma ta kawo ƙarshen aurenta da Gbagbo, tare da jagoranta jam’iyyarta ta daban wanda ƙarƙashinta yanzu haka ta ke takara.
Na biyu a jerin ’yan takarar akwai Jean-Louis Billon mai shekaru 60 da ke wakiltar jam’iyyar Democratic Congress wadda haɗaka ce ta jam’iyyu 18 da suka haɗe waje guda domin ƙalubalantar Ouattara ta hanyar wakilta Billon, wanda tsohon ministan kasuwanci ne kuma na hannun daman madugun adawa Tidjani Thiam da aka haramtawa tsayawa takara a zaɓen na bana.
Na ukun shi ne Ahoua Don Mello mai shekaru 67 kuma tsohon kakakin Laurent Gbagbo yayin rikicin zaɓen 2010 zuwa 2011, kuma yanzu haka yana takara ne a raɗin kansa ba tare da jam’iyya ba, bayan jam’iyyar tsohon shugaba Gbagbo ta kore shi sakamakon aniyar da ya bayyana ta tsayawa takara a wannan zaɓe, kuma ana ganin yana da tasirin da zai iya yiwa Ouattara ɓarna a wannan zaɓe.
Ta ƙarshe a jerin waɗannan ’yan takara, ita ce Henriette Lagou Adjoua, tsohuwar Ministar Mata mai shekaru 66 wadda ta taɓa takara a shekarar 2015 tare da Ouattara amma ta samu ƙasa da kashi 1 na yawan ƙuri’un da aka kaɗa.
Sai dai a wannan karon ana ganin Adjoua ta samu ƙarin magoya baya sakamakon fafutukar da ta ke ci gaba da yi wadda ke tir da matakin ƙyamar mata a madafun iko cikin har da littafin da ta rubuta mai suna Why Not a Woman, wanda kai tsaye ke ƙalubalantar rashin baiwa mata damar shugabanci.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Alassane Ouattara Ivory Coast tsayawa takara mai shekaru
এছাড়াও পড়ুন:
Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Mukaman Gwamnatin Tinubu inji Shugaban FCC
Mukaddashin shugaban hukumar daidaiton rabon muƙamai ta Ƙasa (FCC), Hon. Kayode Oladele, ya bayyana cewa Arewacin Nijeriya ya samu kashi 56.3 cikin 100 na muƙaman gwamnatin tarayya da aka nada karkashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yayin da Kudu ke da kashi 43.7 cikin 100.
Oladele ya bayyana hakan ne a Abuja yayin taron bita na kwana guda kan “Ƙarfafa Jagoranci da Gudanarwa Bisa Renewed Hope Agenda.” Ya ce wannan rabon yana nuna ƙoƙarin gwamnatin Tinubu wajen tabbatar da adalci da daidaiton wakilci kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
A cewarsa, Arewa maso Yamma da Kudu maso Yamma suna da ministoci mafi yawa, mutane 11 kowannensu, yayin da Arewa ta Tsakiya ke da 8, Arewa maso Gabas 7, Kudu maso Kudu 6, da Kudu maso Gabas 5. Bugu da ƙari, Arewa maso Yamma ce ke da yawan muƙaman jagoranci mafi girma (157), sai Arewa ta Tsakiya 139, da Kudu maso Yamma 132.
Ya tabbatar cewa hukumar FCC za ta ci gaba da bibiyar sabbin nade-naɗe don tabbatar da cewa dukkan yankunan ƙasar sun samu wakilci bisa RenewedHope Agenda na Shugaba Tinubu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Grossi: Za a iya warware batun Shirin nukiliyar Iran ne kawai ta hanyar diflomasiyya October 20, 2025 Trump: Shugabanin Hamas ba su da hannu a kisan sojojin Isra’ila 2 a Gaza October 20, 2025 Iran Da Azerbaijan Suna Gudanar Da Atisayen Hadin Guiwa Na Sojojin Ruwa A Tekun Caspian October 20, 2025 Gwamnatin Yamen Tana Tsare Da Ma’aikatan MDD 50 Ta Kuma Kwace Kayakin Aikinsu October 20, 2025 Gwamnatin Colombia Ta Bukaci Bayani Daga Amurka Kan Kashe Wani Dan Kasar A Tekun Carabian October 20, 2025 An Fara Kidayar Kuri’un Zabukan Kananan Hukumomi 16 Da Aka Yi A Libya October 19, 2025 Araqchi: Iran Da Kasashen China Da Rasha Suna Shirin Kawo Karshen Takunkuman Turai October 19, 2025 Miliyoyin Mutanen Amurka Sun Yi Zanga-zanagr Nuna Kin Jinin Donald Trump October 19, 2025 Sheikh Na’im Kassim Ya Mika Sakon Ta’aziyyar Shahadar Gumari Na Kasar Yemen Ga Sayyid Husi October 19, 2025 Sojojin HKI Sun Shiga Cikin Yankin Qunaidhara Na Kasar Syria October 19, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci