Rasha ta kai wa tawagar kayan agajin MDD hari a Ukraine
Published: 14th, October 2025 GMT
Rasha ta kai harin jirage kan ayarin kayan agajin Majalisar Dinkin Duniya a makwabciyarta kasar Ukraine da suka fi shekara biyu suna yaki.
Hukumomin Ukraine sun dakarun soji da ke yankin kudancin Kherson da suka mamaye a Ukraine ne suka kai harin a ranar Talata, inda suka lalata motocin Shirin Abinci na Duniya, a yayin da ma’akatan agajin suka shafe kimanin awa hudu ba su motsa ba saboda luguden bamabaman.
Kwamandan hukumar soji da ke yankin ta bayyana cewa an kona motoci hudu tare da lalata wata a cikin tawagar kayan agajin, amma ba a samu asarar rayuka ba a harin da aka kai da jirage marasa matuka da manyan bindigogin atilare a garin Bilozerka.
Ministan Harkokin Wajen Ukraine, Andriy Sybiga ya bayyana harin a matsayin “wani mummunan karya dokokin kasa da kasa, wanda ke tababtar da cewa Rasha ba ta mutunta rayukan fararen hula da nauyin da ya rataya a wuyanta na kasa da kasa.”
Shugaban Hukumar Zaɓen Yobe Jihar Yobe ya rasu Issa Bakary Tchiroma ne ya lashe zaɓen Kamaru —’Yan adawaKawo yanzu dai Majalisar Dinkin Duniya ko Rasha ko Amurka ba su ce uffan kan lamarin ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Majalisar Dinkin Duniya Rasha Ukraine
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaba Xi Jinping Ya Gabatar Da Shawarwari Hudu A Taron Kolin Mata Na Duniya
Na farko, hada kai don samar da yanayi mai kyau ga ci gaban mata. Na biyu, a karfafa abubuwan da za su habaka ingancin ayyukan mata cikin hadin kai. Kana na uku, a gina tsarin kare hakkin mata tare. Sai na hudu, a bude sabon babin hadin gwiwa tsakanin mata a duniya.
Za a gudanar da taron kolin mata na duniya a yau da gobe Talata a birnin Beijing. Kuma tuni shugaban kasar Sin Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan, suka yi musafaha da shugabannin tawagogin kasashe, da kungiyoyin duniya da suka halarci taron, tare da daukar hotuna tare da su. (Amina Xu)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA