Hamas Ta Ce: Kungiyar Ta Ba Da ‘Yanci Ga Masu Shiga Tsakani Zabar Membobin Kwamitin Gudanar Da Gaza
Published: 27th, October 2025 GMT
Shugaban ƙungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya bayyana cewa: Sun bai wa masu shiga tsakani cikakken ‘yanci na zaɓar membobin Kwamitin Gudanar da Gaza
Khalil al-Hayya, shugaban ƙungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya ce: ƙungiyar ta Hamas ta bai wa masu shiga tsakani ‘yancin zaɓar membobin kwamitin da za su gudanar da mulkin Gaza, wanda zai sami cikakken iko a yankin.
A wata hira da aka watsa a gidan talabijin na Al- Jazeera a yammacin Lahadi, al-Hayya ya jaddada cewa; Akwai batutuwan ƙasa waɗanda ba wai Hamas kaɗai ke da alhakinsu ba, amma alhakin dukkan ƙungiyoyin ƙasa ne. Ya bayyana cewa ƙungiyar ta gudanar da tarurruka da dama da ƙungiyoyi, ciki har da Fatah.
Ya ƙara da cewa abin da aka cimma da ƙungiyoyin Falasɗinu kusan iri ɗaya ne da abin da ta cimma da Fatah. Ya lura cewa sanarwar ƙungiyar, a cikin sashe na farko, ta tabbatar da kafa kwamitin gudanarwa da masu shiga tsakani ke neman kafawa don ɗaukar alhakin gudanar da mulkin Gaza. Ya lura cewa Hamas ta amince da jerin sunayen da Misirawa suka gabatar.
Ya bayyana cewa ƙungiyar ta bai wa Misirawa jerin sunayen mutane sama da 40 waɗanda ba su da alaƙa da siyasa, kimanin watanni huɗu da suka gabata, kuma ya nemi su zaɓi waɗanda suka ga sun dace. Ya ƙara da cewa za a sami rundunar ‘yan sanda ta farar hula wacce ke ƙarƙashin kwamitin gudanarwa a yankin Gaza.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kashe ‘Yan kasar Lebanon Biyu Tare Da Jikkatan Wasu Biyu Na Daban October 27, 2025 Amnesty International Ta Bukaci Bayyana Makomar Masu Fafutukar Kare Hakkin Bil’Adama Da Suka Bace A Uganda October 27, 2025 Dakarun Kai Daukin Gaggawa Sun Yi Da’awar Kwace Karin Wasu Garuruwa A Sudan October 27, 2025 Qalibaf: Sakon Iran, Rasha da China ga MDD manuniya ce ta hadin gwiwa mai karfi October 27, 2025 Sheikh Naim: Hezbollah a shirye take ta fuskanci Isra’ila idan yaki ya barke October 27, 2025 Catherine Connolly ta lashe zaben shugaban Ireland October 27, 2025 Hamas ta sake jaddada wajabcin aiwatar da Shirin tsagaita wuta a Gaza October 27, 2025 Sudan: Dakarun sa kai na Jama’a a Arewacin Darfur sun karyata RSF kan kwace iko da El Fasher October 27, 2025 Araghchi : Iran na maraba da tattaunawar diflomatsiyya da Amurka amma cikin mutunta juna October 26, 2025 Ana Zaman dar-dar gabanin bayyana sakamakon zaben shugaban kasa a Kamaru October 26, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Ki Zuwa Taron Sherme-Sheikh Ne Saboda Kar Ta Zama Mai Shaidar Zur Akan Kisan Kiyashin Gaza
Babban sakataren Majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya bayyana cewa; Bayan da aka dauki shekaru biyu ana yi wa mutanen Gaza kisan kiyashi, wanda mutane 70,000 su ka yi shahada, wasu fiye da 100,000 su ka jikkata, suna son a rufe wannan laifin da taron zaman lafiya.
Ali Larijani ya kara da cewa; Sun kashe al’ummar Falasdinu, sun hana shi abinci da ruwa, yanzu kuma suna son bayyana kawukansu a matsayin masu ceto da Falasdinawa, don haka wannan taron ba komai ba ne sai wasan kwaikwaiyo.
Taron da aka yi a Sherm-Sheikh na Masar an yi shi ne a karkashin jagorancin shugaban Amurka Donald Trump wanda kasarsa ce ta kasance a gaba wajen bayar da makamai ga HKI a tsawon lokacin yaki.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Jami’ar ABU Ta Karyata Zargin Da Ake yi Na Kera Makamin Nukiliya A Asirce October 25, 2025 M D D Ta ce Akalla Mutane miliyan 1.5 Ne Ke Bukatar Taimakon Gaggawa A Gaza October 25, 2025 Tony Balai Na Fuskantar Turjiyar Kasashen Larabawa Game Da Rawar Da Zai Taka A Gaza. October 25, 2025 Yau Ne Ake Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa A Ivory Coast October 25, 2025 Iran Za ta Karbi Bakunci Taron Ministocin Cikin Gida Na Kungiyar ECO October 25, 2025 Jakadan Iran A Majalisar Dinkin Duniya Ya Yi Kiran Da A Nisanci Siyasantar Da Kwamitin Tsaron Majalisar October 25, 2025 Tsohon Shugaban Hukumar Leken Asirin Dakarun IRGC Ya Ce: Yakin Kwanaki 12 Kan Iran Ya Canza Tunanin Makiya October 25, 2025 Rear Admiral Sayyari: Sojojin Iran A Shirye Suke Su Fuskanci Kowace Barazana October 25, 2025 Shugaban Kasar Venezuela Ya Ce; Amurka Tana Son Kaddamar Da Yaki Kan Kasarsa October 25, 2025 Bangarorin Falasdinawa Sun Amince Da Shirin Gudanar Da Zirin Gaza Nan Gaba October 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci