Yunwa: Iyaye na kuka, yara na ramewa a Arewa
Published: 25th, October 2025 GMT
Najeriya na fama da ɗaya daga cikin mafi munin matsalar jinƙai ta yunwa, talauci, da rashin abinci mai gina jiki.
Rahoton Yanayin Ci-Gaban Nijeriya da Bankin Duniya ya fitar a watan Oktoba, ya nuna mutane miliyan 139 a ƙasar na rayuwa cikin talauci a shekarar 2025. Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da rahoton, da cewa sauye-sauyen da ta yi a fannin tattalin arziki na haifar da sakamako mai kyau.
Aminiya ta gudanar da bincike don gano gaskiyar halin da ’yan Nijeriya ke ciki a birane da ƙauyuka. Wakilinmu ya samu damar shiga cibiyoyin kula da masu fama da rashin abinci mai gina jiki da Ƙungiyar Likitoci ta Duniya (MSF) ke tallafawa a Kano da Maiduguri, inda ya gano mummunan tasirin yunwa da dangoginsa.
Tsadar kayan abinci da rashin tsaro da sauyin yanayi da janye tallafin ƙasashen waje sun sa miliyoyin ’yan ƙasar na kwana da yunwa, wanda da ya haddasa yaɗuwar matsalar rashin abinci mai gina jiki, har ta kai ana kwantar da mutum biyu a gadon asibiti guda, a yayin jami’an lafiya ke fama da majinyata a asibitoci.
An kama Sakataren APC na mazaba a Yobe kan zargin aikata kisan kai ’Yan sanda sun sake kama Sowore bayan kotu ta bayar da belinsaMiliyoyin yara a Nijeriya na fama da ƙarancin sinadarai da bitamin, inda kimanin yara miliyan 2 ke fama da rashin abinci mai gina jiki, a cewar Asusun Kuka da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF).
Yara 625 sun mutu a Katsina — MSFWannan matsala ta shafi ƙananan hukumomi 10 a faɗin jihar. Binciken Aminiya ya gano cewa dubban iyalai a cikin ƙananan hukumomi 34 na jihar Katsina sun rage yawan cin abinci a kowace rana daga watan Yuni zuwa Agusta.
A wata ziyara da wakilinmu ya kai cibiyar CMAM da ke cikin birnin Katsina, ya ga yadda ɗaruruwan mata suke zuwa da ’ya’yansu da ke fama da rashin abinci mai gina jiki, inda ma’aikatan lafiya ke kula da su. Cibiyar na karɓar yara tsakanin 50 zuwa 60 a kowane mako, dukkansu masu alamun matsanancin rashin abinci mai gina jiki.
Zainab Kamaladeen, wata uwa mai shayarwa da ke cibiyar tare da ɗanta Ibrahim mai shekaru huɗu, ta ce: “Ɗana ba ya iya cin abinci ko shan ruwa, kuma yana fama da yawan bayan gida. Gwamnati na kula da yaranmu kyauta a wannan asibiti.”
Sai dai ba yara kaɗai ba ne ke fama da wannan matsala — mata masu juna biyu da masu shayarwa ma na cikin halin ƙunci.
A watan Yuli, MSF ta gudanar da tantancewa a kan mata 750 da ke kula da yara masu rashin abinci mai gina jiki a cibiyoyinta guda biyar, inda aka gano cewa rabinsu na fama da rashin abinci mai gina jiki, kuma kashi 13% na fama da matsananciyar matsalar.
A rahotonta na baya-bayan nan, MSF ta ce yara 652 sun mutu a cibiyoyinta tsakanin watan Janairu zuwa Yuni 2025, sakamakon rashin samun kulawa cikin lokaci.
Rahoton ya ƙara bayyana cewa yawan yara da ke fama mafi tsanani da haɗarin rashin abinci mai gina jiki — ya ƙaru da kashi 208% a cikin wannan lokaci idan aka kwatanta da shekarar 2024.
A watan Yuni kaɗai, MSF ta kula da yara 70,000 da ke fama da rashin abinci mai gina jiki a jihar, ciki har da kusan 10,000 da aka kwantar da su a asibiti.
UNICEF ta bayyana cewa kashi 75.5% na yara a Katsina na fama da talauci mai fuskoki da dama, ciki har da rashin lafiyar jiki da abinci mai gina jiki. A wani taron manema labarai kan kasafin kuɗi mai la’akari da yara, Rahama Mohammed Farah, shugaban ofishin UNICEF na shiyyar Kano, ya ce, “Kashi 51.3% na yara ƙasa da shekaru biyar na fama da rashin girma. Yaro 1 cikin 6 na mutuwa kafin ya kai shekara biyar.”
Gwamnatin Katsina ta ƙaryata rahotonMSF ta fara raba kayan abinci mai gina jiki ga yara 66,000 a Ƙaramar Hukumar Mashi. Haka kuma ta buɗe cibiyar kula da yara a Turai da Mashi, inda aka samar da gadaje 900 a asibitoci biyu.
Gwamnatin jihar Katsina tare da UNICEF sun raba katunan abinci mai gina jiki (RUTF) guda 7,000 da sauran kayan tallafi da darajarsu ta kai Naira miliyan 400.
Kwamishinan Lafiya, Musa Adamu-Funtua, ya ce gwamnati ta ware Naira miliyan 500 domin yaƙi da rashin abinci mai gina jiki. Sai dai ya ƙi amincewa da rahoton MSF na mutuwar yara 652. “Ba gaskiya ba ne. Ban san inda suka samo wannan rahoto ba. Na gayyace su su zo su bayyana yadda suka samo shi,” in ji shi.
Sayar da RUTF ya ƙara barazana Duk da ƙoƙarin gwamnati da abokan haɗin gwiwa, yara da dama ba sa samun RUTF. Ana sayar da shi a shaguna, tituna, har ma ana yawo da shi daga gida zuwa gida a ƙananan hukumomin Jibia, Kaita, Mashi, Mai’Adua da Katsina.
Bincike ya nuna cewa masu sayar da shi sun san amfaninsa kuma sun san cewa laifi ne. Wasu iyaye ma na hana ’ya’yansu abinci har sai sun rame don su samu RUTF su sayar.
Wannan ya ƙara janyo matsaloli a fannin lafiya fiye da ribar da ake samu. Masu ruwa da tsaki sun ce dole ne a dakile wannan al’amari.
Ƙungiyoyin agaji sun ce matsalar za ta ƙara tsananta sakamakon rage tallafin ƙasashen waje. Amurka, Birtaniya da Tarayyar Turai sun rage tallafi, lamarin da ke barazana ga ayyukan agaji.
Masana sun buƙaci Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin Gwamna Dikko Umaru Radda da ta ɗauki matakan gaggawa na inganta tsarin samar da abinci mai gina jiki ta hanyar tallafa wa ƙananan manoma, musamman mata.
Haka kuma a tabbatar da sakin kuɗin abinci cikin lokaci da ƙara kasafin kuɗi ga lafiyar yara, sannan a da tallafi ga iyalai masu rauni ta hanyar kuɗi ko abinci.
Sauran sun haɗa da ƙarfafa shayarwa na tsawon watanni 6 da wayar da kan iyalai kan abinci mai gina jiki. Sa’annan a magance matsalolin tsaro, talauci, rashin daidaito, da rashin tsafta da kuma ƙarfafa cibiyoyin lafiya.
Wannan matsala ba ta Katsina kaɗai ba ce — al’amari ne da ke bukatar haɗin gwiwa da gaggawa domin ceto rayukan yara da mata a Arewacin Najeriya.
Girman matsalar a KanoA Jihar Kano, wani magidanci mai sana’ar gyaran keke a unguwar unguwar Sabon Gari a Kano, Malan Mustapha Mustapha Ismail, ya shaida mana yadda yaje kasuwa domin yi wa iyalinsa cefane, amma saboda tsadar kaya, rabin mudun shinkafa ya iya sayowa — wanda ba zai ishe shi da matarsa da ’ya’yansu ba.
Malam Mustapha ya ce da ƙyar kuɗin da yake samu daga sana’ar bai fi N1,500 ba a yini, kuma ba ya iya saya masu abin rayuwa.
Haka miliyoyin ’yan Nijeriya irinsa ke rayuwa, inda kuɗin da suke samu ba ya iya saya musu lafiyayyen abinci mai gina jiki. Saboda haka yawancin abincinsu gari ne ko nau’in tuwo.
“Tsadar rayuwa ta sa idan na sayar da kaya ba na iya sayo wasu su maye gurbinsu, ko da tayar keke ɗaya ce. A da nakan samu N2,500 a rana, amma yanzu da ƙyar nake samun N1,500.
“Ba ma iya sayen nama. Idan na ɗan samu ɗan wani abu lemo biyu nake saya, a yanka kowanne gida huɗu, sai in sha yanka biyu, sauran in kai wa matata da yara” in ji shi.
An kwantar da ’yarsa mai shekara biyu, Rahama da ke fama da rashin abinci mai gina jiki a Cibiyar Kula da Lafiya a Matakin Farko (PHC) ta Unguwa Uku, wadda MSF take tallafawa.
Kafin zuwansu can, sai da iyayen suka kai ta wasu asibitoci huɗu — amma ba a karɓe ta ba, babu wuri. A Unguwa Ukun PHC ma sai da suka yi mako guda kafin ta samu gado a wani ɗaki, wanda saboda tsabar cikarsa, akwai gadon da mutum huɗu ke amfani da shi — jarirai biyu da uwayensu.
Rahama wadda ke dogaro na’urar iskar Oksijin da nadarar jinya ta shafe kwana 13 a gadon asibiti. Likitoci sun ce tana samun sauƙi, amma mahaifiyarta Rukayya Ibrahim, na fargabar cewa idan aka sallame ta, iyayen ba za su iya saya mata nau’o’in abincin da likitoci suka rubuta ba.
“A da muna iya sayen abinci masu gina jiki kamar wake da kifi da nama sosai, amma yanzu rayuwar ta canza. Ina roƙon gwamnati taimaka, gaskiya talakawa na cikin mawuyacin hali. Yanzu yara ba sa samun abinci mai gina jiki,” in ji ta.
Izaja Mustafa, wadda ɗanta ke fama da irin matsalar Rahama ta ce, “Mun wahala kafin mu zo nan asibitin, ban san sa shi ba, kwana biyu ana wa ɗana ƙarin ruwa kafin ya samu ƙarfi, bayan an yi masa gwaji aka ce yana fama da rashin abinci mai gina jiki. Baya cin komai, ba ya sha komai. Suna tambaya ko ina ba shi kifi ko wake da alayyyahu ko ina girki da manja, na ce musu a’a. Ina roƙon gwamnati ta taimaka wa talakawa saboda tsadar rayuwa.
“Ba ni da jarin yin sana’a. Na kai wata ba ni da ko N5 ta kaina, idan ma yara suka tambaye ni kuɗi, ba ni da shi, sai dai mu ci kukan baƙin ciki. Ya kamata a taimaka wa talakawa da jari, wanda ba sai mace ta dogara da miji ba. Yawanci mazan ba sa nan, ba su san damuwar yaro ba, shi ma yaro idan yana son abu ke zai tambaya,” in ji Malama Izaja.
Malama Hauwa ta ce likitoci sun rubuta wa ’yarta abinci masu gina jiki bayan an sallame su, amma ta ce, “Ba zan iya sayen wasu ba saboda rashin kuɗi. Mijina talaka ne kuma muna da ’ya’ya da yawa, koko nake ba wa ƙananan idan na yaye su, ko idan na samu ƙarancin ruwan nono.”
Lantana Jibrin wadda suka yi kwana 13 da ’yarta Shema’u, a Unguwa Uku PHC, ta ce a ƙauyensu da ƙyar suke iya samun abinci mai gina jiki: “Tuwo nake ba ta ko shinkafa ko taliya, ba na iya saya mata kifi ko nama.”
Unguwa-Uku PHC ta cikar maƙil da marasa lafiya kimanin 200 maimakon 120. Manajan Ayyukan Lafiya na MSF a cibiyar, Dakta Arinze Osigwe, ya bayyana yadda suke fama.
“Akwai wata yarinya da uwarta ta kawo ta daga nesa sosai, kuma mafi yawan tafiyar ta yi ne a ƙafa saboda rashin kuɗi. Sai da ta yi kwana biyu kafin ta iso nan. ’Yar ta fi sati biyu tana fama da rashin abinci mai gina jiki. Abin takaici, ko da suka iso, babu abin da za mu iya yi domin ceto ’yar.
“Kai tsaye yunwa na haddasa rashin abinci mai gina jiki, tunda abu ne da ya shafi yawan abinci da kuma ingancinsa, dole ya zama kowannensu ya wadata. Cin zallar gari babu ganyayyaki da sinadarin bitamin da sauran ajujuwan abinci, ba zai taimaka ba, dole sai an samu abinci mai yawa kuma mai ingancin da ya kamata.
“Idan da yunwa ko abinci ya yi kaɗan, ingancinsa ma zai gaza, wannan shi ne alaƙar yunwa da ƙarancin abinci mai gina jiki,” in ji shi.
MSF na da cibiyoyi biyar a Kano. Daga watan Janairu zuwa Agustan 2025, sun kula da yara 26,000 masu fama da rashin abinci mai gina jiki, daga ciki aka kwantar da 5,533 wasu 469 kuma suka rasu.
Wani mai kula da ma’aikatan jibya, Nasir Muhammad ya ce, “Wata uku ke nan muna samun ƙaruwar marasa lafiya. A makon jiya mun kwantar da yara sun kai 1,000 masu tamowa a (Unguwa-Uku PHC) kaɗai.”
Shirin Abinci na Duniya (WFP) ya ce ’yan Nijeeiya miliyan 30.6 na fuskantar barazanar rashin abinci, wanda masana suke ce yana tafiya kafaɗa-da-kafaɗa da rashin abinci mai gina jiki. UNICEF ya bayyana cewa kashi 51.9 na yara a Kano a tsamure suke saboda rashin abinci mai gina jiki.
Martanin Gwamnatin KanoKwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Ibrahim Waiya ya ce; “An ɓullo da shiryeshirye don magance matsalar yunwa da rashin cin abinci mai gina jiki a Jihar Kano.
“Baya ga ware kimanin Naira miliyan 500 da aka yi kwanan nan domin magance matsalar, an ɓullo da Tsarin Abinci Mai Gina Jiki na shekara biyar daga 2025 zuwa 2030, saboda ba za mu yaƙi takauci ba da yunwa sai idan an tallafa wa mutane, wanda hakan ke cikin abubuwan da gwamnati ke yi a kowane wata. Duk wata, gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf tana bayar da tallafin kuɗaɗe ga mata 5,200,” in ji Ibrahim Waiya.
Amma duk da haka, magidanta irin su Malam Mustapha suna fama da talauci da yunwa.
Borono: Tamowa ta tsanantaKimanin mutum miliyan 4.6 na fuskantar barazanar ƙarancin abinci a jihohin Borno da Yobe da Adamawa da ke yankin Arewa maso Gabas inda rashin tsaro da sauyin yanayi ke ta’azzara.
Matsalar yunwa da talauci ta fi muni a Borno sakamakon rikicin ta’addanci na shekara 16, wanda ya sa wasu mazauna suka koma yin bara domin samun abin rayuwa.
A farkon shekarar nan ta 2025 Amurka ta yanke kashi 92% na tallafin USAID ga Nijeriya. Majalisar Ɗinkin Duniya ta zaftare Dala miliyan 610 daga tallafin da take ba wa Nijeriya daga Dala miliyan 910 zuwa Dala miliyan 300.
Masana sun ce yanke tallafin gami da matsalar sauyin yanayi da janye tallafin mai a 2023, sun ta’azzara matsalar ƙarancin abinci a Arewacin Nijeriya.
Dakta Babakura Mamman, Babban Sakataren Hukumar Kula da Ci-gaba Mai Ɗorewa da Jinƙai, ya bayyana, cewa, “Yankewar tallafin ƙasashen waje, yana nufin yara kaɗan ne za su samu abinci, iyaye kaɗan ne za su samu tallafin kiwon lafiya, sa’annan za ta shafi gajiyayyu sosai saboda haka abin zai shafi miliyoyin mutane, musamman a sashen nan na duniya da mutane da dama suka rasa muhallansu. Yawancin abokan hulɗarmu (NGOs) sun taƙaita ayyukansu, wasu ma sun rufe ayyukansu a yankunan da ke da ɗinbin mutane masu rauni,” in ji Dakta Babakura.
A asibitin MSF da ke Maiduguri, inda ake jinyar yara masu fama da rashin abinci mai gina jiki, mun iske Khadija Abubakar mai shekara 20 ta kai ’yarta Fatima ’yar watanni 22 da ke fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki.
Ta ce “Sun ce ’yata na fama da tamowa wadda yunwa ke haddasawa, babu mai son yunwa ta kama jikinsa idan har yana da hali. Idan kana da abin da za ka ci, za ki wanda ya ishe ka, amma idan ba ka da hali, ko ka na so, dole ka haƙura,” in ji Khadija, tana mai kira ga gwamnati ta tallafa wa talakawa.
Daga watan Janairu zuwa Satumba 2025 an kwantar da yara 9,335 kan rashin abinci mai gina jiki a cibiyoyin MSF da ke Maiduguri. Daga cikin mutanen an sallami 8,946.
Manajan Ayyukan Likitanci a Asibitin MSF da ke Maiduguri, Dakta Muhammad Bashir, ya bayyana yadda suke fama da kwararowar irin waɗannan marasa lafiya.
“Kafin mutanen da aka kwanta ya kai haka yanzu, aƙalla duk wata mukan sallami kashi 97 na marasa lafiya, bayan sun murmure, a mayar da su sashen da za a riƙa ba su abinci murmure na tsawon mako huɗu zuwa shida, kafin a sallame su gaba ɗaya.
Amma a wata guda da ya gabata adadin ya ƙaru zuwa 95-96%, wanda ke nufin kashi 3% zuwa kashi 5% na mutanen sun mutu.’ A nan,“a cewar Dakta Bashir.
Martanin Gwamnatin BornoDa yake bayani kan matsalar da kuma matakan da Gwamnatin Jihar Borno take ɗauka domin magance matsalar, Dakta Babakura Mamman ya ce, “Gwamnatin Borno ta tashi tsaye wajen ba wa manoma tallafin da ya dace don su yi noma, ciki har da ba su jami’an tsaro su raka su zuwa gonakinsu da kuma tanadin jigilar su. Motoci kan ke su, sannan su jira su ɗauko su, su dawo da su. Wanda hakan ya taimaka wajen inganta tsaro.
Bara idan mun lura an samu matsalar ƙarancin abinci. Amma bana yankin noman ya ƙaru da aƙalla kashi 80%,” a cewar Dakta Babakura.
Ma’aikatar Nona ta Tarayya ta ce Nijeriya na da ƙasar noma da faɗinta ya kai hekta miiliyan 73, amma hekta 40 ake nomawa, duk da wannan ɗimbin albarkatun ƙasa.
Wani masanin Ci-gaban Tattalin Arzik, Dakta Emeka Okengwu ya ce, “Idan muka san yawan mutanen da za mu ciyar, da irin abincin da za mu samar da inda za mu noma, to sai mu yi amfani da da wannan hekta miliyan 70 na ƙasar noma yadda ya kamata. A tsara yadda za a samar da kowane abinci da kuma wurin da za a noma, ta yadda misali, idan aka ce Jihar Katsina za ta noma kaza, an yi ne ba don da ki ɗan jihar ba ne, kuma kai ne ministan aikin noma. A tsara abin da kowace jiha
Za ta riƙa samarwa bisa la’akari da girman amfanin da za a samu fiye da sauran wurare,” a cewar masanin.
Tashin farashi?Duk da cewa hauhawar farashin kaya a Nijeriya ya sauka zuwa kashi 21.88% a watan Yulin 2025 daga kashi 34.8% da yake a watan Disambar 2024, har yanzu ’yan ƙasar na fama da tsadar rayuwa.
Ko me ya jawo hakan? Dakta Sambo Ingawa, Masanin Ci-gaban Tattalin Arziki, ya ce,
“Akwai matsaloli da dama. Ɗaya daga ciki ita ce matsalar abinci, wanda ke haddasa hauhawar farashi — da ke kawo cikas ga samar da kayayyaki — wanda a ƙarshe yake hana ci-gaba a fannin tattalin arziki .
“Saboda haka, matsalolin da suka fi shekara 10 suna addabar ƙasar nan, su ne sanadiyya. Idan har mafitar gaggawa za ka samar domin magance wannan matsala, ti ba za ta ɗore ba, matsalar za ta sake dawowa,” in ji Dakta Sambo Ingawa.
Ma’aikatar Jinƙai da Rage Talauci ta Tarayya ta ce tana aiki da gwamnatocin jihohi domin magance matsalar ƙarancin abinci.
A wata hira ta musamman da wakilinmu, Ƙaramin Ministan Ma’aikatar, Dakta Yusuf Tanko Sun ya bayyana damuwar shugaban ƙasa kan matsalar yunwa da ƙarancin abinci mai gina jiki a Nijeriya.
“Muna da muhimman wuraren da muke magance matsalolin yunwa da talauci da samar da ayyuka. Idan ka sama wa mutum aikin yi, ka sama masa hanyar samun abinci, shi da kansa zai yi abin da zai kawar da yunwarsa.
Shi ya sa muka ɓullo da tsarin tallafin zuba jari, wanda Shugaban Ƙasa ke so mutane miliyan 15 masu ƙaramin ƙarfi su amfana. Da N25,000 sau uku, wato N75,000.
Zuwa yanzu iyalai miliyan 8.1 sun samu kashi na farko ko na biyu, wasu ma na uku, kimanin Naira biliyan 340. Wasu za su yi jayayya, amma nan gaba kaɗan za mu fitar da alƙaluman ’yan Nijeriya su gani.” In ji ministan.
Da aka tambaye shi, me gwamnati ke yi don magance matsalar rashin abinci mai gina jiki,
Dakta Yusuf, ya ce shugaban ƙasa ya sahale bayar da tallafi.
“A matakin Gwamnatin Tarayya, shugaban ƙasa ya ba izinin tallafi, wanda zai samar da sinadaran abinci masu gina jiki, magunguna da sauran gudummawa.
“Nan gaba kaɗan za mu tabbatar da rabon su cikin adalci, musamman a jihohi 11 da matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki da kuma ’yan gudun hijira ta fi muni.
“Misali, nan ba da jimawa ba ƙungiyar ECOWAS za ta samar da kuɗi Dala miliyan biyu domin tallafa wa samar da abinci, musamman masu samar da sinadaran gina jiki ga yara masu fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki, da sauransu a wasu wurare,” in ji ministan.
Duk da irin waɗannan tabbacin, miliyoyin ’yan Nijeriya na fama da yunwa.
Matsalar ta fi muni a jihohi irin su Borno, Adamawa, Yobe, Katsina, Sakkwato, Kano, Kebbi, da Zamfara inda dubban ɗaruwan yara ke fama da rashin girma.
A watan Agustan 2025, a raba Naira tiriliyan 2.22 a Asusun Tarayya (FAAC) a tsakanin Gwamnatin Tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi.
Amma duk da haka al’umma na fama da rayuwa cikin ƙunci, lamarin da ke haifar da tambaya game da gaskiya wajen gudanar da dukiyar al’umma a ƙasar, wadda ake wa laƙabi da Giwar Afirka.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Nijeriya rahsin abinci mai gina jiki Tsaro yunwa ke fama da rashin abinci mai gina jiki rashin abinci mai gina jiki a matsalar ƙarancin abinci na fama da rashin magance matsalar fama da rashin A wannan matsala Dakta Babakura Jihar Katsina marasa lafiya jihar Katsina yan Nijeriya Dala miliyan kula da yara ce matsalar gwamnati ta
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnonin Arewa sun yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a fashewar tanka a Neja
Ƙungiyar Gwamnonin Arewa (NSGF), ta bayyana hatsarin fashewar tankar mai da ya auku a ƙauyen Essa a Ƙaramar Hukumar Katcha a Jihar Neja, a matsayin abin baƙin ciki da tausayi.
Shugaban ƙungiyar kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ne, ya yi alhinin lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
Waɗanda ke son rusa Kano ba za su yi nasara ba — Sanusi II Majalisar Yobe ta nemi a dauki mataki kan yawaitar hadura a hanyar Damaturu–PotiskumYa miƙa saƙon ta’aziyyae ga gwamnatin Jihar Neja da al’ummarta da kuma iyalan da abin ya shafa.
“Wannan lamari abin baƙin ciki ne ƙwarai da gaske. Addu’o’inmu suna tare da iyalan mamatan da kuma jama’ar Jihar Neja a wannan lokaci na jimami,” in ji Yahaya.
Ya kuma gargaɗi jama’a da su guji ɗibar man da ya zube a kan hanya saboda guje wa hatsari.
“Wannan mummunan lamari ya sake tunatar da mu buƙatar tabbatar da ingantattun matakan tsaro da kuma ƙara wayar da kan jama’a game da hatsarin dakon mai.
“Gwamnati, hukumomi da jama’a dole su haɗa kai don hana aukuwar irin waɗannan abubuwan da za a iya gujewa,” in ji shi.
Gwamnan, ya yaba da ƙoƙarin ma’aikatan ceto, jami’an tsaro, da ‘yan sa-kai waɗanda suka yi aiki tuƙuru wajen ceto waɗanda abin ya rutsa da su.
Ya yi addu’ar Allah Ya jiƙan waɗanda suka rasu, Ya kuma bai wa waɗanda suka jikkata lafiya.
Gwamnan, ya kuma tabbatar da cewa ƙungiyar za ta ci gaba da aiki tare da hukumomin gwamnati na tarayya da na jihohi domin ƙarfafa tsarin kare rayuka da dukiyoyin al’umma a yankin.