Leadership News Hausa:
2025-10-17@15:44:35 GMT

2027: Peter Obi Ya Shiga Rudani Kan Jam’iyyar Da Zai Tsaya Takara

Published: 17th, October 2025 GMT

2027: Peter Obi Ya Shiga Rudani Kan Jam’iyyar Da Zai Tsaya Takara

Saboda haka, an samu labari daga bangaren Obi cewa, tsohon dan takarar shugaban kasa ba za yi zaben fid da gwani ba da Atiku.

Sai dai kuma, sakataren yada labarai na jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi ya ki cewa uffan kan jita-jitan da ke cewa jam’iyyar ta yanke shawarar gudanar da zaben fid da gwani, wanda hakan ya saba wa tsammanin wasu mambobin, musamman daga bangaren Obi.

A cewar Bolaji, a halin yanzu ADC ba ta mai da hankali kan wane zai tsaya takara a karkashin tutan jam’iyyar ADC a zaben 2027 ba.

“A halin yanzu dai, babu wanda aka tattaunawa kan cewa shi ne sahihin dan takara ko kuma za su gudanar da zaben fitar da gwani. Idan mun kai ga wannan lokaci, za mu yi bayani.

“Wannan ba shi ne abin da muke fifita a wannan lokaci ba. Har yanzu mu jam’iyya ce sabuwa kuma muna mai da hankali kan yadda za mu bunkasa jam’iyyarmu a yanzu. Wannan ya fi muhimmanci a gare mu fiye da magana kan ‘yan takarar shugaban kasa”, in ji shi.

Game da dalilin da ya sa Obi bai yi rajista a matsayin mamba na jam’iyyar ba, Bolaji ya ce, “Mun ce Obi da El-Rufai ba su da katin mamba na ADC tukuna saboda yana son goyon bayan ‘yan takarar jam’iyyarsa ta siyasa ta asali a zaben da ke tafe.”

“A game da Peter Obi, bayan zaben Jihar Anambra ne zai iya zaman cikakken dan jam’iyyar ADC. Idan kuma akwai wani dalili, to ban sani ba.”

A gefe guda kuma, wasu masana siyasa sun yi ikirarin cewa da yiwuwar Obi ya tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2027 a karkashin jam’iyyar LP wacce take da saukin rikici a cikinta.

Wani masanin siyasa, Dakta Anabi Samuel, ya shaida cewa burin tsayawa takarar shugaban kasa na Obi ba zai samu nasara a jam’iyyar LP ba, sakamakon rikicin shugabanci da ya dabaibaye jam’iyyar.

A cewar Anabi, rarrabuwan kai da aka samu saboda shugaban jam’iyyar LP, Julius Abure da wadanda ke cikin tawagarsa za su kawo cikas ga Obi.

“Peter Obi ya samu makiya da yawan gaske a LP, don haka za iyi wuya ya samu damar tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar.

“Kamar jagoran reshen jam’iyyar, Julius Abure, zai tabbatar cewa ya kawo masa cikas tun daga zaben fid da gwani kuma zai yi wuya su ba shi tikiti kai tsaye.

“Mu kaddara ma ya sami tikitin LP, sai ya fuskanci makiya daga wajen jam’iyyar wadanda za su tabbatar da cewa bai yi nasara ba.

“Idan Obi ba zai iya samun tikitin ADC ba, ya kamata ya dakatar da burinsa na takara,  sai dai idan PDP ta amince za ta ba shi tikitin tsayawa takarar shugaban kasa.

“Akwai jita-jitan da ke cewa yana shirin shiga sabon jam’iyyar siyasa. Ya kamata Obi ya watsar da wannan tunanin. 2027 ba kamar 2023 ba ce, yana bukatar jam’iyya da aka sani da kyakkyawan tsari don samun nasara a zaben 2027”, in ji Anabi.

Ko da yake wasu masu nazarin harkokin siyasa suna ganin cewa Peter Obi ne ya haskaka jam’iyyar LP, sai dai kuma jam’iyyar ta nace cewa tsohon gwamnan ba zai samu tikitin kai tsaye ba a 2027.

Sakataren yada labaran na wani bangare na LP, Obiora Ifoh ya shaida cewa bai dace ba a ba Obi tikitin kai tsaye.

“Za a gudanar da zaben fitar da gwani na jam’iyyarmu. Za a wallafa mukaman da ake da su kuma duk wanda ke da sha’awa zai nema ya bi tsarin zaben fid da gwani yadda ya kamata.

“Ba tsarin dimokuradiyya ba ce na bai wa wani dan takara tikiti kai tsaye,” in ji Ifoh.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Tambarin Dimokuradiyya Peter Obi Ya Bukaci INEC Ta Tabbatar Da Shaidar Karatun Dan Takara Kafin Shiga Zabe October 10, 2025 Tambarin Dimokuradiyya Maƙiyan Jonathan Ne Kaɗai Za Su Zuga Shi Ya Fito Takara A 2027 – Oshiomhole October 10, 2025 Tambarin Dimokuradiyya Majalisa Na Duba Yiwuwar Amincewa Da Gudanar Da Zaɓen 2027 A Rana Ɗaya October 10, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: takarar shugaban kasa zaben fid da gwani jam iyyar LP a jam iyyar

এছাড়াও পড়ুন:

Ka da a ɗora wa Tinubu laifin rikicin da ke faruwa a PDP — Fayose

Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya ce bai dace a ɗora wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, laifin rikicin da jam’iyyar PDP ke fama da shi ba.

Ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a ranar Laraba, inda ya ce shugabannin PDP ne suka haddasa matsalolinsu, ba Tinubu ko jam’iyyar APC ba.

Kotu ta daure kocin kwallon kafa a Kano shekara 8 saboda aikata luwadi NAJERIYA A YAU: Yadda Cire Darasin Lissafi Zai Taimakawa Dalibai Shiga Jami’a

A cewarsa, jam’iyyar PDP “ta mutu tun tuni,” kuma ba ya cikin waɗanda za su nemi farfaɗo da ita.

Ya ƙara da cewa yawancin gwamnonin da suka rage a PDP na shirin komawa jam’iyyar APC mai mulki.

“Ba daidai ba ne a zargi Tinubu saboda ficewar Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, da Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri, zuwa APC,” in ji Fayose.

“Su da kansu suka yanke shawara saboda PDP ta rasa shugabanci da tsari.”

Fayose, wanda ya mulki Ekiti sau biyu ƙarƙashin jam’iyyar PDP, ya ce jam’iyyar ta kasa koyon darasi daga kurakurenta na baya, kuma ya sa ta zama mai rauni.

Ya kuma zargi wasu shugabannin PDP da yin siyasa don amfanin kansu maimakon ci gaban jam’iyyar gaba ɗaya.

Maganganunsa na zuwa nedaidai lokacin da ake cece-ku-ce a Najeriya kan yiwuwar komawa tsarin jam’iyya ɗaya, yayin da wasu jiga-jigan jam’iyyun adawa ke ci gaba da komawa APC gabanin zaɓen 2027.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka: Ta Bar Baya Da Kura
  • Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka Ta Bar Baya Da KuraAfuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka Ta Bar Baya Da Kura
  • Tsohon Ɗan Majalisar Bayelsa Ya Shawarci Jonathan Ya Guji Neman Takara A 2027
  • Ka da a ɗora wa Tinubu laifin rikicin da ke faruwa a PDP — Fayose
  • Tinubu na ƙoƙarin mayar da Najeriya mai jam’iyya ɗaya — ADC
  • Xi Jinping Ya Taya Patrick Herminie Murnar Lashe Zaben Shugaban Kasar Seychelles
  • Gwamnan Bayelsa ya fice daga jam’iyyar PDP
  • 2027: Babu Ɗan Siyasar Da Zai Iya Ƙalubalantar Tinubu — Fadar Shugaban Ƙasa
  • Shugaba Tinubu Ya Taya Super Eagles Murnar Samun Cancantar Shiga Gasar Kwallon Kafa Ta Duniya