Islamic Jihad : jarumtakar ‘yan gwagwarmaya ce ta haifar da sako fursunonin falasdinawa
Published: 14th, October 2025 GMT
Kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Islamic Jihad ta yi maraba da sako Falasdinawa kusan 2000 daga gidajen yarin Isra’ila, tare da cewa jarumtakar mayakan gwagwarmaya da hadin kan al’ummar Falasdinu ne ya haifar da wannan babbar nasara.
A cikin wata sanarwa da babban sakataren kungiyar Ziyad al-Nakhalah ya fitar ya bayyana cewa, wannan yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta samo asali ne sakamakon jajircewa da tsayin daka da hadin kan al’ummar Falasdinu, wanda idan ba tare da hakan ba yarjejeniyar ba za ta taba cimma ruwa ba.
Bayan shafe sama da shekaru biyu ana kai hare-hare ba kakkautawa wanda ya yi sanadiyar mutuwar dubun dubatan Falasdinawa, gwamnatin Isra’ila bisa matsin lambar kasa da kasa ta amince da yarjejeniyar da Amurka ta kulla na kawo karshen yakin da take yi a zirin Gaza da kuma musayar fursunoni da kungiyoyin gwagwarmayar Falastinawa, inji Islamic Jihad.
A matakin farko na yarjejeniyar da ta fara aiki ranar Juma’a, Hamas ta sako wasu ‘yan Isra’ila 20 da tayi garkuwa da su, yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen mika gawarwakin wasu 28 na daban.
A maimakon haka, Isra’ila ta saki Falasdinawa kusan 2,000.
Falasdinawan da aka saki sun hada da kusan 1,700 da Isra’ila ke rike da su ba tare da tuhumar su ba tun watan Oktoban 2023 da kuma wasu 250 da ke daurin rai da rai.
Ofishin yada labarai na fursunonin Falasdinu ya bayar da rahoton cewa, 154 daga cikin wadanda aka sako an tilasta musu yin gudun hijira a Masar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Aragchi Yana Uganda Don Halattan Taron Ministocin Kungiyar NAM October 14, 2025 Iran Ta Jadda Cewa A Shirye Take Ta Kare Kanta A Duk Wani Yaki Wanda Makiya Zasu Dora Mata October 14, 2025 Ma’aikatar Harkokin wajen Kasar Iran Ta Yi Tir Da Jawabin Trump A Knesset Ta HKI October 14, 2025 An Gudanar Gagarumar Zanga Zangar Goyon Bayan Falasdinawa A Australia Da Indonasia October 14, 2025 Syria: Busaina Sha’aban Ta Karyata Labaran Da Aka Danganta Ma Ta Na Ganawa Da Jami’an Iraniyawa October 14, 2025 Mahalarta Taron ‘Sherm-Sheikh” Sun Rattaba Hannu Akan Yarjejeniyar Zaman Lafiya October 14, 2025 MDD: Mutane 300,000 Su Ka Gudu Daga Sudan Ta Kudu A 2025 October 14, 2025 Iran Ta Gabatar Da Shawarar Kulla Yarjejeniyar Tausayawa A Tsakanin Matan Duniya October 14, 2025 Larijani: Gagarumar Tarbar Da Aka Yi Wa Fursunonin Falasdinawa Ta Nuna Hakikanin Wanda Ya Sami Nasara October 14, 2025 Hamas Ta Mika Yahudawa 7 Daga Cikin 20 Da ke Hannunta Ga Kungiyar Red Cross October 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
UNDP : An ruguza fiye da kashi 80 cikin 100 na gine-ginen Gaza
Hukumar ci gaban kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya (UNDP) ta fitar da wani rahoto dake cewa an ruguza fiye da kashi 80 cikin 100 na gine-ginen zirin Gaza.
UNDP ta ce, a Gaza kadai an lalata fiye kashi 92 cikin 100 na gine-ginen birnin.
Kakakin hukumar ya bayyana rugujewar gine-ginen da ”mummuna”,inda ta kiyasta cewa akwai akalla tan miliyan 55 na baraguzai da ke bukatar sharewa a yankin.
UNDP ta ce tuni ta fara aikin share baraguzan yankin, amma barazanar abubuwan fashewa da aka binne na kawo musu cikas a aikin.
Hukumar ta kara da cewa akwai gawarwakin mutane da ake ta tonowa yayin aikin.
Majalisar Dinkin Duniya da Bankin Duniya da kungiyar Tarayyar Turai sun kiyasta bukatar dala biliyan 70 domin sake gina Gaza.
shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyib Erdogan dake cikin shugabannin da suka ratabba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Gaza ya ce ya yi imanin cewa za a samar da kudin sake gina Gaza.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Araghchi : Trump bai cancanci mai samar da zaman lafiya ba yayin da yake haifar da yake-yake October 14, 2025 Sojojin Madagaska sun karbe mulkin kasar October 14, 2025 Trump ya ce zai yi shawara game da batun kafa kasar Falasdinu October 14, 2025 Islamic Jihad : jarumtakar ‘yan gwagwarmaya ce ta haifar da sako fursunonin falasdinawa October 14, 2025 Aragchi Yana Uganda Don Halattan Taron Ministocin Kungiyar NAM October 14, 2025 Iran Ta Jadda Cewa A Shirye Take Ta Kare Kanta A Duk Wani Yaki Wanda Makiya Zasu Dora Mata October 14, 2025 Ma’aikatar Harkokin wajen Kasar Iran Ta Yi Tir Da Jawabin Trump A Knesset Ta HKI October 14, 2025 An Gudanar Gagarumar Zanga Zangar Goyon Bayan Falasdinawa A Australia Da Indonasia October 14, 2025 Syria: Busaina Sha’aban Ta Karyata Labaran Da Aka Danganta Ma Ta Na Ganawa Da Jami’an Iraniyawa October 14, 2025 Mahalarta Taron ‘Sherm-Sheikh” Sun Rattaba Hannu Akan Yarjejeniyar Zaman Lafiya October 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci