Madugun ’yan adawar kasar Kenya, Raila Odinga, ya mutu
Published: 15th, October 2025 GMT
Jagoran ’yan adawa na kasar Kenya kuma tsohon Firaministan kasar, Raila Odinga, ya mutu yana da shekaru 80 a lokacin da yake karɓar magani a ƙasar Indiya, kamar yadda majiyoyin asibiti da ’yan sanda suka tabbatar a ranar Laraba.
Rahotanni daga Asibitin Devamatha da ke Kerala, kudancin Indiya, sun ce Odinga ya samu bugun zuciya mai tsanani a lokacin da yake yawo da safe kusa da otal ɗinsa a birnin Kochi.
An garzaya da shi zuwa asibiti nan take, amma likitoci sun tabbatar da rasuwarsa lokacin da suka isa.
Hukumomin ’yan sanda na Indiya sun ce gogaggen ɗan siyasar yana tare da ’yar uwarsa, ’yarsa, likitan kansa, da jami’an tsaro daga Kenya da India a lokacin da lamarin ya faru.
“An kai shi wani asibiti mai zaman kansa da ke kusa, amma aka tabbatar da rasuwarsa,” in ji Krishnan M, Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda na Ernakulam a jihar Kerala.
Jami’ai daga ofishin Odinga da ke Nairobi su ma sun tabbatar da rasuwarsa, yayin da jaridar India ta Mathrubhumi ta rawaito cewa Odinga yana karɓar magani na musamman a Kochi kan wata cuta da ba a bayyana ba.
Odinga, wanda ake ɗaukarsa a matsayin ɗaya daga cikin fitattun ’yan siyasa a tarihin Kenya tun bayan samun ’yancin kai, ya taba yin takarar shugabancin ƙasa har sau biyar daga tsakanin 1997 zuwa 2022, amma bai taɓa yin nasara ba.
Duk da rashin nasara, ya ci gaba da kasancewa ginshiƙi a siyasar Kenya da kuma zama alamar gwagwarmayar kafuwar dimokuraɗiyya kawo sauyi da kuma juriya.
Rasuwarsa ta kawo ƙarshen wani zamani a siyasar adawa a Kenya, wanda ya jagoranta tsawon shekaru, kuma ta bar babban gibi na jagoranci gabanin zaɓen kasar na 2027 da ke tafe.
Labarin rasuwar Odinga ya haifar da alhini a faɗin Kenya.
Shugaban ƙasa William Ruto ya ziyarci gidan iyalan Odinga da ke unguwar Karen a Nairobi domin jajanta musu.
Daruruwan magoya bayan marigayin kuma sun taru a wajen gidan, da dama daga cikinsu suna kuka, suna raira waƙoƙin haɗin kai, suna daga rassan itatuwa, alamar gargajiya, yayin da suke jimamin mutuwar mutumin da suka fi sani da “Baba,” lakabi da aka fi kiransa da shi a faɗin ƙasar.
An ci gaba da samun sakonnin ta’aziyya daga ɓangarori daban-daban na siyasa da ma daga ƙasashen waje.
Odinga, ɗan Jaramogi Oginga Odinga, mataimakin shugaban ƙasa na farko a Kenya, ya yi wa ƙasar aiki a matsayin Firaminista daga 2008 zuwa 2013 a ƙarƙashin gwamnatin haɗin gwiwa da aka kafa bayan rikicin zaɓen shugaban ƙasa na 2007.
Ya mutu ya bar matarsa Ida Odinga, ’ya’yansu, da jikokinsu.
Ana sa ran iyalansa za su sanar da shirye-shiryen jana’iza tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Kenya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Kenya Raila Odinga
এছাড়াও পড়ুন:
Ni na nema wa Maryam Sanda yafiya —Mahaifin mijinta
Mahaifin margayi Bilyaminu wanda matarsa Maryam Sanda ta kashe, ya ce shi ne ya roki Shugaba Tinubu ya yafe mata duk da hukuncin kisa da kotu ta yanke mata kan laifin.
Malam Ahmed Bello Isa ya bayyana haka ne yayin ganawa da ’yan jarida, tare da mahaifin Maryam, Alhaji Garba Sanda.
Sun gudanar da taron ’yan jaridar ne bayan ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan yafiyar da Shugaban Kasa ya yi mata tare da wasu mutane 174 da ke tsare a gidajen yari bayan an yanke musu hukunci kan manyan laifuka daban-daban.
Aminiya ta ruwaito dangin Bilyaminu ta hannun Dakta Halliru Bello Muhammad, wanda kawu marigayin ne kuma a hannunsa ya taso yana bayyana yafiyar da aka yi wa Maryam Sanda a matsayin kololuwar rashin adalaci da za a yi wa iyalan.
Amma a taron manema labaran, mahaifin na Bilyaminu ya ce dalilin da ya sanya shi roka wa Maryam Afuwa, shi ne don ta rungumi ’ya’yansu biyu da margayin ya bari.
Ya ce a ganinsa, hukuncin kisan da aka yanke mata ba zai dawo masa da dansa ba.
Ya kuma gabatar wa kwafin wata takarda da ke nuna cewa an rubuta ta tun lokacin da ake binciken shari’ar a 2019, yana sanar da Kwamishinan ’Yan Sanda na Babban Birnin Tarayya cewa a janye batun, saboda ya yafe a matsayinsa na mahaifin mamacin.
Sai dai kuma laifin kisa abu ne da ya shafi hakkin hukuma, don haka hukuma ke da hakkin gurfanarwa.
A shekarar 2023 Kotun Koli ta Tabbatar da hukuncin kisa kan Maryam Sanda kamar yadda Kotun Daukaka Kara ta Abuja da Babbar Kotun Daukaka Kara suka yanke mata da farko.
Tun lokacin aka tura ta zuwa Gidan Yarin da ke Suleja tana zaman jiran a yanke mata hukunci.