Pezeshkian: Iran za ta gwammace takunkumi a kan mika wuya
Published: 24th, October 2025 GMT
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce kasarsa za ta gwammace ta fuskanci takunkumin maimakon mika wuya ga manufofin ‘yan mulkin malla.
“Mun cimma yarjejeniya da bangarori na Turai, amma ra’ayin Amurka ya bambanta, kuma abu ne na hankali kan cewa Iran ba zata mika wuya ga dukkanin abin da Amurka take bukata ba, domin hakan ya yi hannun riga da maslahar Iran.
Amurka da kawayenta, wadanda ake kira da E3, sun ki amincewa da wani daftarin kuduri daga Rasha da China, wanda ya nemi jinkirta aiwatar da tsarin dawo da takunkumai kan Iran a karkashin yarjejeniyar nukiliya ta JCPOA.
Pezeshkian ya kara da cewa Amurkawa “suna son mu ba su dukkan sinadarin uranium da aka tace, wanda ba za a amince da shi ta kowace hanya ba.”
Shugaban na Iran ya nanata cewa da alama Amurka za ta matsa kaimi don “fara mayar da martani” na takunkumin a cikin watanni masu zuwa, yana mai kara jaddada cewa idan aka tilastawa Iran yin zabi, to za ta zabi abin da ya dace da maslaharta da al’ummarta, maimakon biyan bukatar da ta yi hannun riga da maslahar kasa, yana mai shan alwashin cewa “duk da haka, za mu magance dukkan matsalolinmu.”
Ya ba da tabbacin cewa, an dauki matakan da suka wajaba don wannan yanayin, yana mai nuni da kawancen Iran da kasashe makwabta, BRICS, da kasashen kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai, da kuma juriyar al’ummar Iran, duka za su taimaka wajen shawo kan wannan lamarin.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Trump: Amurka na shirin kai hare-hare a Venezuela October 24, 2025 Ivory Coast: Ayyukan ma’adinai na fuskantar tsaiko yayin da Ouattara ke neman wa’adi na 4 October 24, 2025 Dangote zai sayar da kaso 10 na hannun jarin matatar man shi October 24, 2025 Larabawan Yankin Tekun Fasha Sun Caccaki Sabon Shirin Isra’ila A Kan Yammacin Kogin Jordan October 24, 2025 Albanese: Wajibi Ne A Kawo Karshen Gwamnatin Mamaya A Falasdinu October 23, 2025 Rasha: Shugaba Putin Ya Duba Atisayen Rundunar Nukiliyar Kasar October 23, 2025 Shugaban Amurka Ya Soke Shirin Ganawa Da Takwaransa Na Rasha October 23, 2025 Venezuela Ta Sanar Da Mallakar Makamai Masu Linzami Samfurin “ Igla-s” 5,000 Domin Kare Kanta October 23, 2025 Jagora: Allamah Na’ini Ya Kasance Ma’abocin Ilimi Da Sanin Siyasa October 23, 2025 Kimanin Bakin Haure 40 Ne Suka Mutu A Kokarin Ketarawa Turai Ta Tekun Mediterranean October 23, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Rasha: Shugaba Putin Ya Sa Ido Akan Atisayen Rundunar Nukiliyar Kasar
Fadar mulkin kasar Rasha Krimlne ta sanar da cewa, shugaban kasar Valdmir Putin ne ya sa ido akan yadda rundunar dake kula da makaman Nukiliya ta gudanar da rawar daji a sansnain “Blisitiks”.
Sanarwar ta kara da cewa, rundunar dake kula da muhimman makakan Nukiliyar kasar ta Rasha ta yi amfani da makamai masu linzami samfurori mabanbanta.
Haka nan kuma fadar gwamnatin Rashan ta ce, an gudanar da dukkanin gwaje-gwajen cikin nasara, an kuma yi ne domin tabbatar da cewa rundunar tana cikin shirin ko-ta-kwana.
A wani labari mai alaka da Rasha, ma’aikatar harkokin waje ta gargadi kasashen turai akan kokarin bai wa Ukiraniya kudadenta da suke a cikin bankunansu.
MA’aikatar harkokin wajen Rasha ya fadawa kasashen turai din cewa martanin da kasar za ta mayar idan har su ka kuskura su ka taba mata kudinta dake cikin bankunansu, zai zama mai tsanani.
Kasashen turai dai suna tattauna hanyoyin doka da za su basu damar dibar kudaden Rasha da suke cikin bankunansu, domin bai wa kasar Ukiraniya ta sayi makamai da su.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shugaban Kasar Amurka Ya Soke Shirin Ganawa Da Takwaransa Na Kasar Rasha October 23, 2025 Venezuela Ta Sanar Da Mallakar Makamai Masu Linzami Samfurin “ Igla-s” 5,000 Domi Kare Kanta October 23, 2025 Jagora: Allamah Na’ini Ya Kasance Ma’abocin Ilimi Da Sanin Siyasa October 23, 2025 Kimanin Bakin Haure 40 Ne Suka Mutu A Kokarin Ketare wa Turai Ta Tekun Mediterranean October 23, 2025 Hamas Tayi Maraba Da Karyata Ikirarin Isra’ila da Kotun Duniya ICJ Tayi Kan UNRWA October 23, 2025 Alkalai Sun Yi Watsi Da Karar Da Yan Adawa Suka Shigar Kan Zargin Magudi A Zaben Kamaru October 23, 2025 Yahudawa A Kasashen Duniya Sunyi Kira Ga M D D Da Ta Kakabawa Isra’ila Takunkumi October 23, 2025 Ministan Leken Asiri: Iran Bata Da Tabbacin Kare Maslaharta A Tattaunawa Da Amurka. October 23, 2025 ICJ : Isra’ila ta karya dokokin duniya wajen hana shigar da kayan agaji a Gaza October 23, 2025 Amurka : Shirin Isra’ila na mamaye yammacin kogin Jordan, barazana ne ga tsagaita wuta a Gaza October 23, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci