Kasar Sin Ta Karyata Rahoto Na Zuki-ta-malle Da Wata Cibiyar Binciken Amurka Ta Fitar Game Da Hadin Gwiwar Sin Da Yammacin Afirka
Published: 23rd, October 2025 GMT
A yau Alhamis 23 ga wata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya karyata wani rahoto na zuki-ta-malle da wata cibiyar bincike ta Amurka ta bayar kan hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka ta Yamma. Ya yi nuni da cewa, rahoton ya kawo rudani ga ra’ayoyi na kaifin basira, sannan daga bangare guda kawai aka tattaro shi, kuma har ma ya ruwaito wasu bayanan da ba a tantance ba, tare da shafa kashin kaji da kuma muzanta hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da kasashen yammacin Afirka.
An ba da rahoton cewa, cibiyar nazarin al’amura ta Amurka ta Atlantic Council, ta fitar da rahotanni da dama a baya-bayan nan, inda ta bayyana cewa, ayyukan hakar ma’adinai, da gandun dazuzzuka da kamun kifi da kasar Sin ke yi a yammacin Afirka, sun haifar da mummunar illa ga muhallin halittu, tare da yin kira ga yankin yammacin Afirka da ya ba da hadin kai wajen karfafa sa ido kan lamarin.
A yayin da yake mayar da martani, Guo Jiakun ya ce, kasar Sin na gudanar da hadin gwiwa da kasashen Afirka bisa ka’idojin gaskiya, da zuciya daya da kyakkyawar manufa, da kuma kyakkyawan ra’ayi na adalci da cin moriya, don ba da gudummawa ga ci gaban tattalin arzikin Afirka da samun habaka mai dorewa, wanda gwamnatoci da jama’ar Afirka suka yi maraba da su.
Ya kara da cewa, babban abin da Afirka ke sha’awa na yin hadin gwiwa da kasar Sin shi ne bayar da misali ta fuskar samun moriyar juna da samun nasara ga bangarorin biyu. A ko da yaushe, gwamnatin kasar Sin tana bukatar kamfanonin kasar Sin da ofisoshin kasuwanci na ketare da su mutunta dokokin da suka dace da hakan. Har ila yau, za ta ci gaba da jagorantar masana’antu don aiwatar da manufar bunkasa muhalli, da shigar da kiyaye muhalli a cikin dukkan matakan tsarin hadin gwiwar Sin da Afirka. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Rasha Ta Yi Maraba Da Cire Sunanta A Matsayin ” Barazanar Da Amurka Teke Fuskanta
Mai Magana da yawun fadar mulkin Rasha Dmitry Viskov ya ce; Fadar mulkin kasar tana maraba da matakin da shugaban kasar Amurka ya dauka na bitar siyasar tsaron kasar, da ta kunshi cire kasar Rasha a matsayin barazanar da Amurkan take fuskanta.
Viskov ya fada wa kamfanin dillancin labarun “Tass” cewa; a cikin sabon tsarin tsaron kasar ta Amurka an cire Rasha a matsayin baraza, don haka yana kira da a samo hanyoyin aiki tare akan muhimman batutuwa na duniya.
Haka nan kuma ya ce; Wannan matakin ci gaba ne sosai.
Wannan sabuwar siyasar tsaron ta Amurka tana yi wa China a matsayin babban kalubale ta fuskar tattalin arziki, don hakan Amurka za ta yi aiki domin sake dawo da adalci da kuma abinda ta kira ‘yancin Amurka.”
Sai dai kuma ta jaddada wajabcin ci gaba da jibge sojoji a yankin tekunan Inida da kuma Pacific domin abinda ta ce kokarin hana afkuwar yaki.
Haka nan kuma ya bayyana fatansa na ganin sabuwar siyasar tsaron Amurka ta share fagen kawo karshen yakin kasar Ukirniya da kuma tattaunawa da bude sabuwar alaka da Amurka, da hakan shi ne ra’ayin shugaba Vladmir Putin.
Matakin na Amurka akan Rasha ya bakantawa kasashen turai da suke son Amurkan ta zamar musu jagora a yakin da suke yi da Rasha ta hanyar kasar Ukiraniya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Majid Majidi Na Iran Ya Sami Kyauyar Girmamawa Daga Cibiyar Fina-finai Na “Eurasia Dake Kasar Rasha December 8, 2025 Benin : Har yanzu Shugaba Patrice Talon ne a kan mulkin_fadar shugaban kasa December 7, 2025 Dole ne Amurka ta amince da ‘yancin Iran na samar da makamashin nukiliya cikin lumana (Araghchi) December 7, 2025 Hamas : ‘’Babu batun kwance damarar makamai matuƙar Isra’ila ta ci gaba da mamaya’’ December 7, 2025 Iran : sabbin dabarun tsaron Amurka cimma maradun Isra’ila December 7, 2025 Masar : ba za mu bari a yi amfani da iyakar Rafah ba don korar Falasdinawa December 7, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 168 December 7, 2025 Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 167 December 7, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 166 December 7, 2025 Rwanda Da Amurka Sun Rattaba Hannu Kan Tallafin Dalar Amurka Miliyon $228 Na Kiwon Lafiya December 7, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci