ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Babaganaru Ya Zama Sabon Kocin Kano Pillars October 22, 2025 Labarai Morocco Ta Lashe Kofin Duniya Na Ƴan Ƙasa Da Shekara 20 Karo Na Farko A Tarihinta October 20, 2025 Wasanni Kano Pillars Ta Dakatar Da Manyan Masu Horas Da ‘Yan Wasanta Saboda Rashin Nasara October 20, 2025

.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025 Na Jaridar Leadership: Dauda Lawal

Wannan tsarin na taimaka wa yara su samu ilimi mai zurfi da zai ba su damar daidaita da tsarin rayuwarsu na yau da kullum.

Makarantun suna da ɗakunan kwana, gidajen malamai, wutar lantarki mai amfani da hasken rana, rijiyoyin burtsatse, kujeru, kayan karatu, da cibiyar koyon sana’o’i kamar ɗinki, sassaƙa, kwamfuta, da sauransu.

Haka kuma, gwamnan ya gyara Ma’aikatar Harkokin Mata da Ci gaban Jama’a ta Jihar Zamfara da kuma Kwalejin Fasaha da Kimiyya ta Zamfara (ZACAS).

A ɓangaren lafiya kuwa, gwamnatinsa ta gyara asibitoci da cibiyoyin lafiya da dama a faɗin jihar.

Don rage mace-macen mata da jarirai a yayin haihuwa, ya ɗauki ƙarin ma’aikatan lafiya, tare da samar da magunguna da kayan aiki, tare d harkar kyautata kiwon lafiya ga mata masu juna biyu da yara kyauta.

Asibitin Ƙwararru na Yeriman Bakura an gyara shi gaba ɗaya tare da samar da kayan aiki na zamani.

Asibitin Gwamnati na Kauran Namoda ma an sabunta shi da kayan gwaje-gwaje, kujerun haihuwa, injinan ECG, da sauran kayan asibiti na zamani.

A Nasarawa Burkullu, an gina sabbin sassa a Asibitin Gwamnati, ciki har da ɗakin agajin gaggawa, ɗakin tiyata, ɗakin haihuwa, ɗakunan jinya na maza da mata, ɗakin gwaje-gwaje, da ɗakin magani.

Haka kuma an samar da masallatai, gidajen ma’aikata, da rijiyoyin burtsatse.

A ƙaramar hukumar Maru, Asibitin Gwamnati ma an gyara shi tare da sanya kayan aiki na zamani.

Gwamnan, ya kuma ƙaddamar da shirin sabunta birane wanda ya haɗa da gyaran manyan hanyoyi da gine-gine a biranen jihar.

A ɓangaren tsaro, Jihar Zamfara ta samu sauƙin yawaitar hare-hare a ’yan shekarun nan.

An rage kashe-kashe da satar mutane sosai.

Wannan ya faru ne saboda ƙirƙirar rundunar ‘Community Protection Guards’ a kowace ƙaramar hukuma 14 da ke jihar.

An zaɓi mutanen ne bayan cikakken bincike da DSS ta jagoranta, sannan aka horar da su don taimaka wa jami’an tsaro wajen yaƙi da ’yan ta’adda.

Gwamnan ya kuma raba motoci 140 ga hukumomin tsaro daban-daban a jihar.

Tarihin Gwamna Dauda Lawal

An haifi Dauda Lawal a ranar 2 ga watan Satumba, 1965 a Jihar Zamfara.

Ya kammala karatunsa na digiri da digiri na biyu a Fannin Siyasa a Jami’ar Ahmadu Bello, da ke Zariya, sannan ya yi digirin digirgir a Fannin Kasuwanci a Jami’ar Usmanu Danfodiyo, da ke Sakkwato.

Hakazalika, ya yi kwasai-kwasai na horo a Harvard Business School, Oxford University, London School of Economics, da Lagos Business School.

Kafin ya shiga siyasa, ya yi aiki a MAMSER, sannan ya yi aiki a Ofishin Jakadancin Nijeriya a Washington DC a matsayin jami’in shige da fice.

Daga baya ya koma aiki a bankin First Bank of Nigeria, inda ya zama Daraktan Ayyukan Jama’a na Arewa.

Ya shiga siyasa a shekarar 2018, inda ya tsaya takarar gwamna a jam’iyyar APC, amma bai yi nasara ba.

A zaɓen 2023, ya tsaya takarar gwamna a jam’iyyar PDP kuma ya lashe zaɓen, tare da Gwamnan Jihar Zamfara.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Shugaban NAHCON Ya Musanta Zargin Tsare Ɗan Jarida Da Aikata Cin Hanci October 22, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aiki, Ta Bai Wa Gwamnati Wa’adin Wata Guda Don Biyan Buƙatunta October 22, 2025 Labarai Rashin Abinci Mai Gina Jiki Barazana Ce Ga Lafiyar Al’umma – Gwamna Lawal October 22, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Adadin Yawon Shakatawa Da Mutanen Sin Suka Yi A Cikin Gida Ya Zarce Biliyan 4.998 Tsakanin Janairu Da Satumban Bana
  • Jerin ’yan wasan da ke takarar lashe kyautar gwarzon Afirka na bana
  • Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025 Na Jaridar Leadership: Dauda Lawal
  • Babaganaru Ya Zama Sabon Kocin Kano Pillars
  • Sudan: Jirgin ‘Drone’ Ya Fada Kan Tashar Jiragen Sama Na Khurtum Kafin A Sake Bude Ta
  • Dembele ya dawo PSG bayan jinyar makonni
  • Kano Pillars ta dakatar da Kocinta
  • Kano Pillars Ta Dakatar Da Babban Kocinta Bisa Rashin Katabus A Kakar Wasa Ta NPFL
  • Kano Pillars Ta Dakatar Da Manyan Masu Horas Da ‘Yan Wasanta Saboda Rashin Nasara