Yawan Hada-hadar Kudaden Kasashen Waje Na Kasar Sin A Farkon Rabu’i Na Uku Na Bana Ya Zarce Dala Triliyan 11
Published: 23rd, October 2025 GMT
Bisa kididdigar da hukumar kula da kudaden kasashen waje ta kasar Sin ta gabatar a yau ranar 22 ga wannan wata, a watan Satumba, yawan kudin da aka yi hada-hadarsu ta fuskar samun kudin shiga da kuma wadanda aka kashe na kamfanoni da daidaikun mutane da sauran hukumomin da ba na banki ba na kasar Sin ya kai dalar Amurka triliyan 1.
Mataimakin shugaban hukumar kuma kakakin hukumar Li Bin ya bayyana cewa, kasar Sin ta kiyaye samun karuwar cinikin waje, yawan kudin shiga a fannin cinikin kaya ya ci gaba da samun karuwa, kana an kiyaye samun hada-hadar kudi a fannonin samar da hidimomi da zuba jari a tsakanin kasa da kasa.
Li Bin ya bayyana cewa, tun daga farkon bana, an tafiyar da kasuwar kudaden waje ta kasar Sin yadda ya kamata yayin da ake fuskantar yanayi na rashin tabbas a kasashen waje, kuma an kiyaye kyakkyawan zaton yadda kasuwa za ta kasance, da tabbatar da yanayin hada-hadar kudaden waje, inda hakan ya shaida karfin kasar Sin a wannan fanni. (Zainab Zhang)
ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: kasar Sin ta
এছাড়াও পড়ুন:
Me Aka Gano Kan Makomar Tattalin Arzikin Kasar Sin Daga Karuwar 5.2% Na Tattalin Arzikinta?
Har ma abun da ba kasafai ake gani ba, tattalin arzikin Sin yana cike da karfin tinkarar duk wani hadari da ka iya kunno kai. Ba sabunta kayayyaki kirar kasar da kara musu inganci kadai aka samu ba, har ma abokan cinikin kasar a ketare suna ta kara yawa.
A jiya Litinin ne aka bude cikakken zama na 4 na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20 a nan Beijing, inda za a tattauna da kuma ba da shawarwari kan shirin shekaru biyar-biyar na 15 na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin. Kasashen duniya na sa ran cewa, kasar Sin za ta ba da sababbin damammarkin neman samun ci gaba ga duniya, bisa ga tsayayyun manufofinta da ci gaba da bude kofarta ga duk duniya baki daya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA