Gwarzon Gwamnan 2025 Sanata Uba Sani: Mai Haɗa Kan Al’ummar Da Suka Rarrabu
Published: 24th, October 2025 GMT
A shekara biyu kaɗai,ya yi ƙoƙarin maida Jihar Kaduna da aka sani da rarrabuwar kai, yanzu ta koma tsintsiya ɗaya sanadiyar hakan.
Yin gyara ta hanyar ci gaba
Gwamna Sani ya hau kan karagar mulki ne a shekarar 2023 ba a matsayin wanda ya iya lamarin siyasa sosai ba, sai dai mai son kawo agyara. Aikinsa na farko ba siyasar bace —mutane ne yafi maida hankali kansu.
Ya fara ƙaddamar da lamarin gaggarumin ci gaban ƙauyuka ta yadda abin ya zama a kowace ƙaramar hukumar akwai aikin da ake yi.Gina hanyoyi, asibitoci, makarantu, kasuwanni an fara gigginasu a ƙananan hukumomi 23 .
Cikin ci gaban daya samu sun haɗa da:
Haɓaka ƙananan asibitoci 225 inda aka mayar da su matsayi na 2, inda tuni aka kammala 174.
An gyara 13 daga cikin manyan asibitoci 33 da kuma sa masu dukkan kayan da suka kamata.
Gadaje 300- na asibitin ƙwararu, da aka yi watsi da shi tun shekarar 2009, an kammala su, Shugaban ƙasa Bola Tinubu — ya ƙaddamar dasu inda aka kawo ƙarshen shekara 16- da aka yi ana jira.
Manyan motoci 400 da suke ɗauke da Takin zamanin da aka rabawa ƙananan manoma 100,000 kyauta, domin samun ingantaccen abinci maikyau da kuma isasshe.
Kowane aikin da aka yi akwai labarain da yake badawa na dalilin da yasa aka yi shi — na gwamnan da shi manufarsa ita ce kowanne al’umma a Jihar Kaduna.,ko a Birni suke ko kuma ƙauye, su san da cewa ba mantawa aka yi dasu ba.
Abubuwan more rayuwa ta hanyar sasantawa
Babban burin shi mai sauƙi ne babu wata wahala: ci gaba shi ne babban lamarin tafiya da haɗin kai domin sasantawa.
Yadda aka yi ayyukan a dukkan faɗin Jihar ba tare da la’akari da Kabila ba ko kuma addini, ballantana ma har ace daga wace shiyya mutum yake, ya koyar da amincewa da yarda a cikin Jihar duk kuwa yadda take da al’umma daban- daban.
A ƙoƙarinsa na haɓaka hanyoyi, kilomitoci na manyan hanyoyi yanzu an haɗa su, waɗanda a shekarun baya an raba mutane da zuwa kasuwannin ƙauyuka. Gadoji waɗanda suka haɗa garuruwa— yanzu sun koma wata dabarar sake haɗa al’ummar da a da basu ga maciji koi zaman manja da doya tsakaninsu, domin da a rabe suke sanadiyar rashin jituwa.
Kaduna a halin da ake ciki yanzu babu wata maganar rarrabuwar kai sai dai ƙarin danƙon- zumunci.
Mai son bunƙasar Mata da Matasa
Gwamna Sani bai tsaya anan ba domin kuwa suma Mata da matasa abin ci gaban ya same su domin kuwa ba mantawa ya yi dasu ba.
A hanyar gidauniyar Uba Sani, an horar da dubban matasa wajen koyon sana’oi, koyon yadda za’a tafiyar da na’urar sadarwa ta zamani, da kuma dabarun sana’oi daban- daban. An kuma raba masu tallafin yadda za su fara sana’oi da wasu kayayyaki waɗanda zasu ɗaukaka mata daga dogaro da wasu, su zama masu nema ba dai a nemo a basu ba.
Hakanan ma ya buɗe hanya inda har ila yau ya taimakawa mata da matasa waɗanda aka sa su wasu wurare masu amfani, inda yake nuna cewa yadda Jihar zata kasance, a gaba abin ya dogara ne kan dukkan al’ummarta gaba ɗaya.
Ya san yadda zai yi mu’amala da mutane
Kafin ya shiga gidan gwamna, Uba Sani ya fara rayuwar zuwa gidan gwamnati ne da zama da zama ɗan gwagwarmaya, ɗan kasuwa, da kuma ma’aikaci —lamarin da kowa yake haɗa hakan ba, shi yasa kuma yadda yake tafiyar da gwamnatinsa abu ne mai sauƙi gare shi.
Ƙuniya mai zaman kanta : A matsayin mataimakin shugaban na ( Arewa) fafutukar kamfen na damukuraɗiyya, daga baya kuma mataimakin Shugaba (Arewa) na JACON ada ke ƙarƙashin Chief Gani Fawehinmi, a Arewacin Nijeriya zamanin mulkin soja.
Kasuwanci: Ɗan kasuwa ne wanda ya samu nasara a harkar sadarwa da kuma gidaje da filaye, daga can ne ya koyi haƙuri idan ya samu riba ko kuma faɗuwa.
Gwamnati: Matsayin Sanata (2019-2023) , yayi shugbancin kwamitin Banki, Inshora da sauran hukumomi masu harkar kuɗaɗe ya bada gudunmawa wajen gyaran da aka yi wanda shi ne ya ƙara haɓaka lamarin kuɗaɗe.
Irin halayya ta gwagwarmaya, kasuwanci, da kum atsarin manufofi hakan ya samar da Shugaba kuma jagora, wanda idan aka aikata rashin adalci zai nuna rashin adalci, akwai ranar da zai nemi ayi zaman sulhu.
Mai ra’ayin ilimi, yin abu yadda ya dace ayi shi, da kuma mutuntawa
An haife shi ranar 31 ga Disamba 1970, a Zariya, Sani yana digiri na biyu a harkokin da suka shafi kuɗi daga Jami’ar Kalaba, sai Difiloma kan harkokin mulki daga Jami’ar Abuja , da kuma Babbar Difiloma ta ƙasa kan Makanikal Injiniya daga makarantar fasaha ta Kaduna.
Hakanan ma shi shi tsohon ɗalibi ne na wani karatun da yayi kan Shugabanci a Amerika. (IƁLP) “yin abu ba tare da amsar ko kwabo ba, sai yadda za ‘a tafiyar da ƙungiyoyi masu zaman kansu.”
Karatuntukan makarantun da yayi ko shakka babu sun kasance fitila gun shin a yadda zai tafiyar da harkokin gwamnati da dai sauran al’amura.
Daga majalisa zuwa gidan gwamnati
A matsayin san a Sanata, Uba Sani ya bar wani abinda ya zama tarihi. Uku daga cikin ƙudurorinsa sun samu amincear Shugaban ƙasa — lamarin da ba kowa bane zai samu irin wannan sa’ar — hakan ne ma yasa ake girmama shi a matsayin ɗan majalisa da yafi amfani a majalisar ƙasa ta 9.
Sa’oin daya samu sun nuna cewar horon ya yi matuƙar taimaka ma shi wajen yadda yake tafiyar da mulkin Jihar Kaduna.
Yanzu shi ne, mataimakin ƙungiyar gwamnonin APC shi ne kuma gwamna da zai sa ido kan lamauran sashen Arew a maso yamma, da kuma daidaituwar manufofin gwamnatin tarayya da Jihohi.
Shugaba mai sauraren jama’arsa
A Jihar Kaduna, koda waɗanda basu yin shi sun amince da gwamna Uba Sani ya na tafiyar da mulkinsa kamar yadda ya dace.
Yana ganawa da al’umma kafin motar da zata yi gyara ta kama aikinta, zai saurare su kafin ya ɗauki mataki, a wurin shi kuma dole ne tilastawa ta biyo bayan tausayawa.Yadda yake sauraren al’umma yasa suna amincewa da duk waɗansu abubuwan daya kawo gabansu tsakanin Sarakunan gargajiya, Shugabannin addini, da kuma ƙungiyoyi masu zaman kansu.
Ba wani abin mamaki bane tunda yanzu tarurrukan zaman lafiya yanzu sun fi zanga- zanga, ga kuma uwa- uba yadda ake haɗa kai tsakanin al’ummomi shi ne ya maye gurbin yadda ake zama a shekarun baya.
Ayyukan da ya yi sun sa amincewa da yadda yake
Gwamnan Kaduna Uba Sani ba wai ya fi kowa iya mulki bane, amma akwai ci gaba a Jihar saboda da akwai yarda juna, wanda ta hakan ma ana samun ci gaba.
Mulkinsa ya maida hankali ne kan abubuwan more rayuwa, kula da lafiyar al’umma, aikin moma, da kuma masana’antu, irin hakan ne ya jawo hankalin al’umma a iyakokin Nijeriya.
Shi ya sa mutane ke son tun daga zucci, ɗan gwagwarmayar da ya taɓa yi zanga- zanga domin a wanzar da mulkin farar hula —yanzu shi ne mai gina damukuraɗiyya da hanyoyi, makarantu, da kuma asibitoci.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: Jihar Kaduna
এছাড়াও পড়ুন:
Gwarzuwar Shekarar 2025 Sanata Oluremi Tinubu
Uwargidan Tinubu Ta Ƙaddamar Da Ɗakin Karatu Na E-learning A Zamfara Sanatan Bauchi Ta Arewa Ya Fice Daga Jam’iyyar PDPHar ila yau, shirin nan nata Mata A Aikin Noma, ya bai wa matan karkara sama da 20,000 tallafi da horarwa da ƙara samun kuɗin shiga ga iyalai da kuma wadatar da al’umma. Kazalika, shirin Tallafin Ilimi, ya samar wa fiye da ɗalibai 3,000, guraben karatu, kwamfiyutoci da kuma jagoranci na gari. Ga tsofaffi kuma, Asusun Tallafa wa Tsofaffi ya bai wa tsofaffi 5,000 alawus-alawus da kula da lafiyarsu tare kuma da maido da martabar musamman waɗanda aka yi watsi da su, aka kuma manta da su.
Lokacin da iftila’i ya afku a Jihohin Filato da Benuwe a tsakiyar 2025, ba saƙo ta aike da shi; cikin gaggawa ta garzaya domin jajanta musu. Ta ziyarci waɗanda abin ya shafa, ta jajanta wa waɗanda suka rasa matsugunansu, sannan ta bayar da gudummawar Naira biliyan ɗaya ga kowace jihohin guda biyu. Daga baya a watan Agusta, ta ba da irin wannan agaji da ya kai kimanin Naira biliyan ɗaya ga al’ummomin da ambaliyar ruwa ta shafa a Jihar Neja tare da buhunhunan shinkafa da kayan sawa 2,000.
A watan Satumba, ta mayar da bikin cikarta shekaru 65 zuwa hidimar ƙasa, inda ta tara kuɗi kimanin Naira biliyan 20.4, domin kammala ginin ɗakin karatu na ƙasa da aka daɗe ba a yi ba tare da yin watsi da shi a Abuja. Sannan, ta ƙi karɓar wasu kyaututtuka da aka ba ta, wanda hakan ke nuna kyakkyawan shugabanci na-gari.
Tausaya Wa Nakasassu
Tausayinta ga nakasassu ya bayyana a fili cikin shirin nan ‘Renewed Hope Initiatiɓe’, a ɓangaren nan na koyar da sana’a’i, wanda ya horar da aƙalla mutum 1,200 ilimin kwamfuta, samar da ‘yan kasuwa tare da horar da wasu. Ta kuma ba da tallafin kiwon lafiya da wayar da kan jama’a tare da tantance ‘yan Nijeriya sama da 100,000 masu fama da cututtukan hawan jini, ciwon siga da kuma matsalar ido, domin tabbatar da ko suna ɗauke da cututtukan tare da ɗaukar matakan gaggawa.
Ta hanyar dagewa wajen ganin shirin ya tafi yadda ya kamata, Sanata Tinubu ta gabatar da kyakkyawan tsari, domin aiwatar da ayyukan jin ƙai. Dagewarta kan nuna gaskiya, ya sa shirin RHI ya samu karramawa daga ƙungiyoyin farar hula da sauran abokan ci gaban ƙasa da ƙasa.
Sabunta Harkokin Ilimi
Tsohuwar malamar makaranta, Sanata Tinubu na kallon ajujuwa a matsayin wurin da aka samar da sabbin sauye-sauye. Shirin da ta samar na matasa masu ilimi, wanda aka ƙaddamar a shekarar 2024, aka kuma sake faɗaɗa shi a 2025, na tallafa wa ɗalibai masu hazaƙa, waɗanda iyayensu ke da ƙaramin ƙarfi (Talakawa), wanda ya dace da su tare da ba su shawarwari, musamman ta fuskar harkar ilimin kimiyya da fasaha. Fiye da ɗalibai 1,200 a halin yanzu sun samu damar shiga shirin, wanda ke nuni da cewa; sama da kashi 95 cikin 100 na waɗanda suka rabauta, ba su taɓa mantawa da wannan abin alhairi da aka yi musa ba.
Tasirin Abin Da Za A Iya Ƙirgawa Da Kuma Wanda Ke Shafar Ruwa Kai Tsaye
A duk fadin Najeriya, za a iya ƙirga ayyukanta, ba kawai a ƙididdiga ba, a cikin labarai.
Mata manoma 20,000 a halin yanzu, suna samun kuɗin shiga akai-akai, saboda tallafin noma da horo na RHI. Dubban ɗalibai, sun faɗa kasadar ficewa daga makarantusu, amma yanzu ƙarƙashin wannan shiri nata, sun koma azuzuwansu sakamakon bayar da tallafin karatun da ta yi.
Haka zalika, sama da ‘yan Nijeriya 100,000 ne aka yi wa gwajin kamuwa da cututtuka masu tsanani daban-daban, sannan da dama daga cikinsu sun samu tallafin ceton rai. Yanzu haka, tsofaffi dubu biyar ne ke cin gajiyar alawus-alawus na yau da kullun da kuma zuwa duba lafyarsu, yayin da nakasassu kuma aka ba su kayan aiki, domin fara sana’o’insu, wasu kuma da kansu sun zama masu horar da su.
A kowane irin hali, alƙalumman na ba da labari iri guda: a ƙarƙashin Sanata Tinubu, tausayi ya zama shi ne abin aunawa, sannan kuma abubuwan da ake sa rai da su, sun tabbata.
Imani, Iyali da kuma Amfanin Shugabanci
Kasancewarta mai tsananin tausayi da gaskiya, jagora tagari, mai kuma son yin aiki ta hanyar yin haɗin gwiwa, Sanata Tinubu na ɗaya daga cikin waɗanda ke jagorantar al’ummar da samar da haɗin kai tare da tausayinsu. Ta auri Shugaba Bola Ahmed Tinubu, sannan ta daidaita buƙatun shugabancin ƙasa da iyali, imani da kuma tawali’u.
Nutsuwa da halinta da kuma ɗabi’un aikinta, sun haifar da sha’awa; har ma daga masu suka, suna sake fasalin ofishin Uwargidan Shugabancin a matsayin ɗaya daga cikin kulawa, maimakon alama. Ta nuna cewa, mulki a cikin lumana, ka iya haifar da sakamako mai kyau tare da kuma tausayi.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA