HausaTv:
2025-10-16@09:00:51 GMT

Ministocin Harkokin Wajen Kungiyar NAN Sun Nuna Goyon Bayansu Ga Venezuela

Published: 16th, October 2025 GMT

Ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar ‘yan baruwanmu a  taronsu karo na 19  da ke gudana a birnin Kampala na kasar Uganda a ranakun 15 da 16 ga wannan wata na Oktoban 2025, sun bayyana matukar damuwarsu kan halin da ake ciki a yankin Caribbean, tare da tabbatar da cikakken goyon bayansu ga Jamhuriyar Venezuela wajen fuskantar duk wata barazana daga waje.

Ministocin sun bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa, inda suka nuna matukar damuwa kan yadda lamurra suka kara tabarbarewa sakamakon tura karin sojoji da kayan yaki da Amurka ta jibge a yankin, wanda hakan ke nuni karuwar barazana ta tsaro a daukacin yankin.

Haka nan kuma Ministocin sun yi nuni da muhawarar baya bayan nan da aka yi a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a ranar 10 ga watan Oktoban 2025, wanda ya tabbatar da bukatar bin ka’idoji na Majalisar Dinkin Duniya, da dokokin kasa da kasa, da kuma Fifita hanyoyi na tattaunawa, da diflomasiyya domin warware batutuwa masu sarkakiya da ake da sabani a kansu a tsakanin kasashen duniya.

Sannan kuma sun yi gargadin cewa, daukar duk wani mataki na soji a kan kasar Venezuela, tabbas zi yi mummunan tasiri ga makomar yankin Caribbean  baki daya.

Har ila yau, a cikin bayanin nasu sun jaddada wajabcin kare hakkokin kasashe da rashin tsoma baki cikin harkokinsu na  cikin gida, tare da goyon bayan ‘yancin  Venezuela bisa  tsarin dokokin kasa da kasa.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sojojin Pakistan Sun Tarwatsa Tankokin Yaki 6 Na Afghanistan A Rikicin kan Iyaka October 15, 2025 Tawagar Super Eagles Ta Nijeriya Ta Lallasa Benin Da ci 4-0 A Uyo October 15, 2025 Matakin Kasashen Yamma Na Maidowa Da Iran Takunkumi Ya Sabawa Doka. October 15, 2025 Kasar Indunusiya Ta Sanar Da Goyon Bayanta Ga Alummar Falasdinu October 15, 2025 Isra’ila  Za Ta Sake Kai Hare-hare Idan Ta Karbi Dukkan Mutanenta Da Hamas Ta Kama. October 15, 2025 Trump Ya Fadawa Hamas Su Mika Makamansu Ko Kuma A Kwace Su Da Karfi October 15, 2025 Iran Ta Samarda Sabbin Hanyoyi Na Fuskantar  Barazanar Makiya October 15, 2025 Hamas Ta Ce HKI Tana Cikas Neman Gawawwakin Yahudawa A Gaza October 15, 2025 Yansandan Italiya Sun Kara Da Masu Goyon Bayan Falasdinawa A Garin Udine October 15, 2025 Iran Ta Yi Allah Wadai Da Kalaman Kin Jinin Iran Da Trump Ya Yi A Majalisar Dokokin Isra’ila                            October 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Kasar Indunusiya Ta Sanar Da Goyon Bayanta Ga Alummar Falasdinu

Shugaban kasar Indonusiya  Prabowo Subianto ya sanar da irin ci gaban da aka samu game da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a gaza, kana ya sanar cewa Jakarta a shirye take ta aike da dakarun tabbatar da zaman lafiya, domin nuna irin tsawon lokacin da kasar ta dauka tana nuna goyon bayanta ga alummar falasdinu a gwagwarmyar neman yanci da suke yi.

Kasar Indonusiya tana da tsohon tarihi wajen nuna goyon bayan neman bada yancin ga alummar falasdinu, sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da aka yi a Gaza ya bude wata kofa ta tabbatar da zaman lafiya a yankin, kuma kasar a shirye take ta aike da kayan agaji,  bangaren diplomasiya, aikewa da dakarun tabbatar da zaman lafiya domin ganin an samu zaman lafiya mai dorewa.

Shugaban kasar na Indonusiya ya bayyana zaman lafiyar da aka samu a baya bayan nan a gaza, a matsayin wani mataki na samun tabbaci, kuma yayi ishara game da kalubalen da ake fuskanta, inda yace indunusiya ta yarda da zaman lafiya, taimakon agaji a yanki, kana kuma ya jaddada shirin kasar na bada duk wata gudunmawa wajen aikewa da dakarun tabbatar da zaman lafiya na kasa da kasa.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Isra’ila  Za Ta Sake Kai Hare-hare Idan Ta Karbi Dukkan Mutanenta Da Hamas Ta Kama. October 15, 2025 Trump Ya Fadawa Hamas Su Mika Makamansu Ko Kuma A Kwace Su Da Karfi October 15, 2025 Iran Ta Samarda Sabbin Hanyoyi Na Fuskantar  Barazanar Makiya October 15, 2025 Hamas Ta Ce HKI Tana Cikas Neman Gawawwakin Yahudawa A Gaza October 15, 2025 Yansandan Italiya Sun Kara Da Masu Goyon Bayan Falasdinawa A Garin Udine October 15, 2025 Iran Ta Yi Allah Wadai Da Kalaman Kin Jinin Iran Da Trump Ya Yi A Majalisar Dokokin Isra’ila                            October 15, 2025 A Lokacin Yaki, Iran Ta Tarwatsa Wata Cibiyar Leken Asirin Yahudawan Sahayoniyya Da Ke Yankin Farar Hula October 15, 2025 Shugaban Kasar Columbia Ya Yi Dirar Mikiya Kan Donald Trump Kan Bai Wa Isra’ila Makamai October 15, 2025 Kungiyar Jihadul-Islami Ta Falasdinu Ta Ce; ‘Yantar Da Fursunonin Falasdinawa Abu Ne Mai Muhaimmanci October 15, 2025 Majalisar Dinkin Duniya Ta Bayyana Cewa: Sake Gina Gaza Zai Ci Dala Biliyan 70 October 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kasar Indunusiya Ta Sanar Da Goyon Bayanta Ga Alummar Falasdinu
  • Yansandan Italiya Sun Kara Da Masu Goyon Bayan Falasdinawa A Garin Udine
  • Kungiyar Jihadul-Islami Ta Falasdinu Ta Ce; ‘Yantar Da Fursunonin Falasdinawa Abu Ne Mai Muhaimmanci
  • Aragchi Yana Uganda Don Halattan Taron Ministocin Kungiyar NAN
  • Ma’aikatar Harkokin wajen Kasar Iran Ta Yi Tir Da Jawabin Trump A Knesset Ta HKI
  • An Gudanar Gagarumar Zanga Zangar Goyon Bayan Falasdinawa A Australia Da Indonasia
  • Larijani:  Gagarumar Tarbar Da Aka Yi Wa  Fursunonin Falasdinawa Ta Nuna Hakikanin Wanda Ya Sami Nasara
  • Kungiyar Hamas Ta Mika Yahudawa 7 Daga Cikin 20 Da ke Hannunta  Ga Kungiyar Red Cross
  • Kungiyar (ASUU) Ta Sanar Da Shiga Yajin Aikin  Gargadi A Kasa Baki Daya .