Aminiya:
2025-09-17@22:12:29 GMT

Tinubu ya umarci sojoji su murƙushe ’yan ta’adda a faɗin Najeriya 

Published: 6th, July 2025 GMT

Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya umarci dakarun sojin Najeriya da su murƙushe ’yan ta’adda, masu tada ƙayar baya, da ’yan awaren Biyafara da ke barazana ga zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.

Yayin bikin Ranar Sojoji ta 2025 da ya gudana a Jihar Kaduna, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya wakilci Shugaba Tinubu.

Mutum 21 sun rasu a hatsarin mota a kan hanyar Zariya–Kano Zulum ya musanta shirin ficewa daga APC

Tinubu ya ce: “Lokacin tashi ya yi. Ina tare da ku ɗari bisa ɗari don murƙushe masu yunƙurin rusa Najeriya. Ku ne ƙarfina, goyon bayana da addu’o’ina.”

Ya gargaɗi cewa barazanar da ake fuskanta ba ƙananan abubuwa ba ne.

“Waɗannan miyagun ba sa bambanta tsakanin coci da masallaci. Suna mayar da yara marayu ba tare da la’akari da ƙabila ko addini ba,” in ji shi.

Tinubu, ya kuma sha alwashin ci gaba da inganta walwalar sojoji da ba su kayan aiki na zamani.

“Za mu ci gaba da zuba jari a makamai, bayanan sirri da horo. Sojojinmu dole su kasance a shirye a koyaushe don kare Najeriya.”

Ya jinjina wa sojojin da suka rasa rayukansu wajen kare ƙasa.

“Jininsu ba zai zube a banza ba. Za mu ci gaba da tunawa da su har abada.”

Shugaban Hafsan Soji, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya yaba wa jarumtar dakarun sojin Najeriya.

“Karfinmu na gaske shi ne jarumta da sadaukarwar sojan Najeriya,” in ji shi.

Bikin ya ƙayatar da dandazon jama’a da manyan baƙi, inda aka nuna kayan aikin dakarun na zamani.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: yan ta adda umarni

এছাড়াও পড়ুন:

NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar Ruwa

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

Ambaliyar ruwa na cigaba da salwantar da dukiyoyi da rayukan al’ummomi da dama a sassa daban-daban na Najeriya.

 

Ko a farkon makon nan, hukumomi sun yi gargadin cewa akwai yiwuwar samun ambaliyar a jihohi akalla 11.

Sai dai wasu alummomin tuni suka dauki matakai don rage barnar da ambaliyar ka iya yi musu.

NAJERIYA A YAU: Masu Nau’in Jinin AS Sun Fi Masu Nau’in AA Lafiya DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau Uku

A kan wadannan matakai shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari.

Domin sauke shirin, latsa nan

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnati ta ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani 20 a Sakkwato
  • Tinubu Ya Janye Dokar Ta-baci A Jihar Rivers
  • Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a Ribas
  • Chadi:  Majalisa ta amince a baiwa shugaban kasa  damar ci gaba da Mulki har karshen rayuwa
  • Sojoji Sun Harbe Wasu ‘Yan Ta’adda 2 A Taraba
  • Sin Ta Daga Zuwa Mataki Na 10 A Jadawalin GII Na Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Kirkire-Kirkire
  • ’Yan sanda sun kama mutum 6 kan satar zinarin N109m a Kebbi
  • NAJERIYA A YAU: Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba
  • Tattalin Arzikin Sin Ya Samu Ci Gaba Ba Tare Da Tangarda Ba A Watan Agusta
  • NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar Ruwa