NUJ Reshen Kano Ta Taya Ahmed Mu’azu Murna Kan Naɗin Da NAHCON Ta Yi Masa
Published: 23rd, October 2025 GMT
Ƙungiyar ‘yan jaridu ta Nijeriya (NUJ), reshen jihar Kano, ta mika sakon taya murna ga Ahmed Mu’azu bisa naɗin da aka yi masa na mataimaki na musanman a ɓangaren yaɗa labarai ga shugaban hukumar alhazai ta ƙasa (NAHCON), Abdullahi Usman Saleh. A matsayinsa na ɗan asalin jihar Kano, ɗaukaka darajar Malam Ahmad Mu’azu zuwa wannan matsayi abin alfahari ne ga masu aikin jarida a jihar.
কীওয়ার্ড: yaɗa labarai
এছাড়াও পড়ুন:
Fyaɗe ga ’yar shekara 12 ya ja wa matashi ɗaurin rai-da-rai a Yobe
Kotu ta yanke wa wani wanda ya yi wa wata yarinya ’yar shekara 12 fyaɗe hukuncin ɗaurin rai-da-rai a Ƙaramar Hukumar Guba ta Jihar Yobe.
Babbar Kotun Jihar Yobe da ke zaune a ƙaramar hukumar Gujba ta yanke wa mutumin mai shekaru 31 mai suna Ali Kwano.
An gurfanar da shi ne a kan zargin ya kai yarinyar cikin aji a ƙaramar makarantar sakandare ta je-ka-ka-dawo da ke garin Bumsa, inda ya yi lalata da ita da ƙarfi.
Ya yaudari yarinyar ce bayan ya gaya mata cewa ta jira shi a cikin aji bisa cewar zai sayi ƙosai.
Bayan da ta shiga ajin sai ya kama hannunta, ya rufe bakinta ya danne ta a ƙasa sannan ya yi lalata da ita da ƙarfi.
Ƙasashen waje na taimaka wa ’yan ta’adda a Najeriya —Sheikh Gumi ’Yan sanda sun kama tsohon shugaban PCACC, Muhuyi Rimin Gado a KanoAlƙaliyar da ke jagorantar shari’a, Mai Shari’a Amina Shehu, ta same shi da laifi, don haka ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai-da-rai bisa ga sashe na 3 na dokar haramta cin zarafin mutane, ta Jihar Yobe ta Shekarar 2020.