Gwamnatin Tarayya Ta Jajantawa Waɗanda Fashewar Tankar Mai Ta Rutsa Da Su A Neja
Published: 23rd, October 2025 GMT
Gwamnatin Tarayya ta koka da cewa, duk da wayar da kan jama’a da kuma gargadin da ake ci gaba da yi, wasu mutane har yanzu suna kasada da rayukansu ta hanyar yunƙurin ɗibar mai yayin da tankunan dakon mai suka faɗi.
Ya jaddada cewa, kowace rai ta ɗan Nijeriya tana da daraja kuma irin wadannan bala’o’in da za a iya rigakafin su, na nuna bukatar kara wayar da kan jama’a game da haɗurran da ke tattare da hakan cikin gaggawa.
Ya ce, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), an umurce ta da ta hada karfi ga kokarin Gwamnatin Jihar ta hanyar samar da kayan agaji da taimakon magunguna ga wadanda abin ya shafa da iyalansu.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
ISWAP: Mun kawar da duk wata barazana — Gwamnatin Ondo
Gwamnatin Jihar Ondo ta roƙi jama’a da su kwantar da hankalinsu bayan gargaɗin da Hukumar Tsaro ta DSS, ta yi na cewar wasu mayaƙan ISWAP na shirin kai hari wasu sassan jihar.
A cikin wata sanarwa, Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Mista Idowu Ajanaku, ya bayyana cewa irin waɗannan rahotanni abu ne na yau da kullum a harkokin tsaro.
NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Haraji Da Zai Fara Aiki A 2026 Idan Tinubu ya gaza zai yi wuya a samu shugaban da zai yi nasara — Shehu SaniYa ce hukumomin tsaro suna yawan musayar bayanai irin waɗannan domin daƙile duk wata barazana.
Ajanaku, ya tabbatar wa jama’a cewa gwamnati tare da hukumomin tsaro sun ɗauki matakai don kare rayuka da dukiyoyin jama’a a faɗin jihar.
“Gwamnati da hukumomin tsaro suna kan lamarin kuma suna ɗaukar duk matakan da suka dace don tabbatar da cewa Jihar Ondo ta kasance cikin aminci,” in ji sanarwar.
Ya kuma roƙi mazauna jihar da su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da ayyukansu na yau da kullum, sannan su riƙa sanar da hukumomin tsaro idan suka ga wani abun zargi.
Kwamishinan ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta mayar da hankali sosai kan yankunan da ke iyakar wasu jihohi don kawar da kowace irin barazana.
“Don Allah kada ku firgita, kada kuma ku ɗauki doka a hannunku. Ku haɗa kai da gwamnati da hukumomin tsaro domin mu ci gaba da tabbatar da tsaron jiharmu,” in ji Ajanaku.