Aminiya:
2025-10-23@13:55:16 GMT

Nnamdi Kanu ya kori lauyoyinsa, ya ce zai kare kansa a kotu

Published: 23rd, October 2025 GMT

Shugaban Ƙungiyar ’Yan Awaren Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu, ya sallami dukkanin lauyoyinsa.

A zaman kotu da aka gudanar a ranar Alhamis, Kanu ya shaida wa kotu cewa a shirye yake ya kare kansa ba tare da taimakon lauya ba.

DSS ta cafke mutum 3 kan zargin sayar wa ’yan bindiga makamai a Kaduna ’Yan uwana 8 sun rasu a fashewar tanka a Neja — Wani Mutum

Lauyoyin da ke kare shi ƙarƙashin jagorancin Kanu Agabi (SAN), sun yanke hukuncin cire hannunsu daga kare shi kan shari’ar da yake fuskanta.

Daga nan sai Kanu ya fara magana kai-tsaye, inda ya ƙalubalanci ikon kotu na ci gaba da yin shari’arsa.

 

Cikakken bayani zai biyo baya…

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Shari a

এছাড়াও পড়ুন:

EFCC ta ƙwato fiye da naira biliyan 500 a shekara biyu — Shetima

Mataimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, ya bayyana cewa, Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arziki ta’annati ta samu nasarar tara dukiyar da ta haura naira biliyan 500 a tsawon shekaru biyu na gwamnatinsu.

Shettima, wanda ya wakilci Shugaba Bola Tinubu, ya bayyana haka ne a yayin wani taron bita da ƙara wa juna sani na alƙalai da Hukumar EFCC tare da haɗin gwiwar Hukumar Shari’a ta Najeriya (NJC) suka shirya a birnin Abuja.

Red Cross ta kafa cibiyoyin rage haɗurran bala’o’i a makarantun Gombe NLC ta sa zare da gwamnati kan yajin aikin ASUU

Shettima ya buƙaci alƙalai da sauran ma’aikatan ɓangaren shari’a da su ƙara ƙaimi tare da yin aiki bisa gaskiya da adalci, yana mai gargaɗin cewa ana fara samun matsala ne a ƙasa da zarar masu riƙe da amanar hukunci suka fara tauye haƙƙin mai haƙƙi.

Mataimakin shugaban ƙasar ya ce gwamnatinsu ba ta tsoma baki a harkokin shari’a, yana mai cewa “mun ba ɓangaren shari’a da hukumomin yaƙi da cin hanci damar gudanar da ayyukansu ba tare da katsalandan ba,” in ji shi.

Da yake bayyana irin nasarorin da aka samu a fannin yaƙi da cin hanci da rashawa, Shettima ya ce EFCC ta samu nasarar ƙwato fiye da naira biliyan 500 a cikin shekara biyu da suka gabata.

“A cikin shekara biyu na wannan gwamnatin, EFCC ta samu nasarar gurfanar da sama da mutum 7,000 a gaban kotu, sannan ta ƙwato dukiyar da ta haura naira biliyan 500,” in ji Shettima.

Ya ƙara da cewa, kuɗaɗen da aka ƙwato ana amfani da su ne a shirye-shiryen tabbatar da walwalar al’umma, ciki har da shirin bayar da bashi ga ɗalibai da sauran manufofin tallafa wa jama’a.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jami’an tsaro sun kama Sowore saboda shirya zanga-zanga
  • Gwamna Yusuf Ya Gwangwaje Kano Pillars Da Sabbin Motocii
  • Ba A Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla A Arewacin Nijeriya – Sarkin Musulmi
  • Yadda Zanga-zangar Kanu ta ja wa ’yan kasuwa da ma’aikata asara
  • Bidiyoyin baɗala: Kotu ta umarci Hisbah ta daura aure tsakanin ’yan TikTok
  • Najeriya: ‘Yansanda A Abuja Sun Yi Amsani Da Hayakin Mai Sa Hawaye Kan Masu Neman A Saki Nnamdi Kanu
  • EFCC ta ƙwato fiye da naira biliyan 500 a shekara biyu — Shetima
  • An maka mahaifi a kotu kan cefanar da gidan ɗansa a Kano
  • Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Mutane Biyu Da Suka Kashe Malamin Jami’a