Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum
Published: 26th, October 2025 GMT
Matatar Dangote ta sanar da shirin ƙara ƙarfin sarrafa man fetur daga ganga 650,000 zuwa miliyan 1.4 a kowace rana, wanda zai sanya ta zama babbar matatar mai mafi girma a duniya. Shugaban kamfanin, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana hakan a taron manema labarai a Legas, yana mai cewa faɗaɗawar na nuna ƙwarin gwuiwa ga tattalin arziƙin Nijeriya da hangen nesa na Shugaba Bola Ahmed Tinubu na mayar da ƙasar cibiyar sarrafa mai ta duniya.
Dangote ya ce aikin faɗaɗawar “tana nuna amincewa da ƙarfin Afrika wajen tsara makomar makamashinta,” yana mai yabawa gwamnati bisa manufofi irin su Naira-for-Crude Policy da One-Stop Shop Initiative, waɗanda suka ƙarfafa zuba jari a ɓangaren mai. Ya kuma tabbatar da cewa matsalolin da suka shafi ƙungiyoyi da tsayawar aiki an magance su, tare da dawo da zaman lumana a matatar.
ACF Ta Yi Zargin Shiri Na Musamman Don Rusa Matatar Man Dangote Kada Ku Yi Sanadiyar Rugujewar Matatar Mai Ta Dangote – Shettima Ga PENGASSANA cewarsa, aikin faɗaɗawar zai samar da aiyukan yi sama da 65,000 yayin gina sabbin sassa, tare da inganta samar da sinadarai kamar polypropylene, base oils, da linear alkylbenzene, wanda ake amfani da shi a masana’antar kayan tsafta. Dangote ya kuma tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa “ƙarancin man fetur ba zai sake faruwa ba yayin bukukuwan ƙarshen shekara.”
Matatar Dangote, wacce aka ƙaddamar a Mayu 2023 ta hannun tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ta fara aiki a Janairu 2024 bayan ta karɓi gangar mai miliyan 6 na ɗanyen mai. Tun daga wannan lokaci tana taimakawa wajen wadatar da kasuwannin cikin gida da rage dogaro da shigo da man fetur daga ƙasashen waje.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Gombe Ta Ƙulla Yarjejeniya Da Rano Air Don Fara Jigila Tsakanin Abuja Zuwa Gombe
Tawagar kamfanin na Rano Air a wurin ganawa da gwamnan, ta haɗa da Babban Manajan (Ayyuka), Abah O. Godwin; da Accountable Manager Alhaji Lawal Sabo Bakinzuwo; da Shugaban Sashin Ayyuka na ƙasa Bashir Abdullahi Wudilawa; da Shugaban Sashin Bunƙasa Harkokin Kasuwanci na kamfanin, Auwal Sulaiman Ubale.
Jami’an kamfanin sun tabbatarwa gwamnan cewa kamfanin na Rano Air zai samar da nagartacciyar hidima abar dogaro, mai inganci kuma mai haba-haba ga kwastomomi, ta yadda za a samu sauƙin tafiye-tafiyen kasuwanci da bunƙasa harkokin tattalin arziki a faɗin jihar da Arewa Maso Gabas baki ɗaya.
“Gwamna Inuwa Yahaya ya yi maraba da wannan ci gaba, inda ya bayyana hakan a matsayin wata shaida kan yadda Jihar Gombe ke da zaman lafiya da kwanciyar hankali kuma jihar da ke maraba da harkokin kasuwanci,” sanarwar ta naƙalto.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA