Ƴan Bindiga Sun Sace Ma’aikatan INEC Uku Da Wasu
Published: 24th, October 2025 GMT
Wasu jami’an Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) guda uku da ke hanyarsu ta zuwa jihar Anambra domin shirye-shiryen zaben gwamna na ranar 8 ga Nuwamba, sun shiga hannun ‘yan bindiga a jihar Kogi.
Rahotanni daga mazauna yankin sun bayyana cewa an yi garkuwa da jami’an ne a ranar Talata, a ƙauyen Aloma da ke ƙaramar hukumar Ofu ta jihar Kogi.
Sienna da suka ke tafiya da ita ya bayyana a cikin wani kiran waya cewa ƴan bindigar sun tare hanya, suka buɗe musu wuta, har suka lalata gilashin gaban motar, lamarin da ya tilasta musu tsayawa.
A cewar Direban motar, dukkan fasinjojin da ke cikin motar an yi garkuwa da su, ciki har da matarsa, baya ga jami’an INEC uku da kuma wasu fasinjoji uku da ke cikin motar da suke tafiya tare da su.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Tarayya ta yi jimami kan mutuwar mutanen da suka rasu a fashewar motar mai a Jihar Neja
Gwamnatin Tarayya ta bayyana alhinin ta kan mummunar haɗarin fashewar motar mai da ta faru a ƙauyen Essa, cikin Karamar Hukumar Katcha ta Jihar Neja, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu da yawa.
A cikin wata sanarwa da Ministan Yada Labarai da Tsarin Ƙasa, Mohammed Idris, ya sanya wa hannu, Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyya ga Gwamnatin Jihar Neja da al’ummar jihar bisa wannan babban rashi, tana mai bayyana lamarin a matsayin abin tunawa da illar da ke tattare da haɗarin motocin mai a ƙasar.
Sanarwar ta nuna damuwa kan yadda, duk da wayar da kai da gargadin da ake yi a kai a kai, wasu ’yan ƙasa har yanzu ke shiga cikin haɗari ta hanyar kwasar mai daga motoci da suka kife, wanda hakan kan haifar da asarar rayuka da dukiya.
Ministan ya jaddada cewa duk rayuwar ɗan Najeriya tana da muhimmanci, tare da yin kira da a ƙara lura da bin matakan tsaro a lokutan gaggawa.
Ya yaba wa Gwamnatin Jihar Neja, jami’an tsaro, da kuma masu aikin ceto bisa saurin da suka nuna wajen kashe wutar da kuma ceto rayuka.
Haka kuma, Ministan ya bayyana cewa Hukumar Kula da Bala’o’i ta Ƙasa (NEMA) ta samu umarni da ta ci gaba da ba da tallafi da taimakon gaggawa ga waɗanda abin ya shafa, yayin da Hukumar Wayar da Kan Jama’a (NOA) za ta ƙara ƙaimi wajen yaɗa faɗakarwa domin hana irin wannan bala’i a nan gaba.
Gwamnatin Tarayya ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan waɗanda suka mutu, tare da yin addu’a ga Allah Ya jikansu, Ya kuma ba waɗanda suka jikkata lafiya ta ƙwarai.
Bello Wakili