Gwamnatin Jihar Sokoto Ta Amince da Sauya Amfani da Naira Biliyan 526 a Kasafin Kuɗin 2025
Published: 24th, October 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Sokoto ta amince a rika sauya kuɗaɗe da aka ware wasu wurare zuwa swasu idan can ya fi na farko amfani ga al’umma (virement) na naira biliyan 526 a cikin kasafin kuɗin shekarar 2025.
Shugaban taron majalisar zartarwa ta jihar karo na 12 na bana, Gwamna Ahmad Aliyu, ya tabbatar da cewa gwamnatinsa na da cikakken ƙuduri wajen gina Jihar Sokoto mai ingantaccen tattalin arziki ta hanyar aiwatar da muhimman sauye-sauye da shirye-shiryen ci gaban al’umma.
Gwamna Aliyu ya bayyana cewa wannan sauyin kasafi an tsara shi ne domin ƙarfafa zuba jari a fannoni masu muhimmanci kamar gina manyan ayyukan raya kasa, inganta ayyukan jin kai, da haɓaka tasirin gudanar da ayyuka — ba tare da ƙara girman jimillar kasafin kuɗin shekara ba.
Da yake bayani ga manema labarai bayan taron, Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Alhaji Aminu Iya, ya ce canjin kasafin zai mai da hankali kan kuɗaɗen da za a yi amfani da su wajen aiwatar da ayyukan ci gaban jama’a kai tsaye.
A cewarsa, majalisar ta amince da aiwatar da wasu muhimman ayyuka, ciki har da: bita (workshop) na Hukumar Sufurin Jihar Sokoto da ware naira miliyan 75 domin kula da motocin gwamnati, da kuma sayen motocin aiki ga Ma’aikatar Kuɗi ta Jihar Sokoto.
A fannin ilimi kuwa, Kwamishinan Ilimin Firamare da Sakandare, Farfesa Adan Ahmad Ala, ya sanar da cewa majalisar ta amince da naira miliyan 930 domin siyan kujera da tebura 15,000 ga makarantu na firamare da sakandare a fadin jihar.
Nasir Malali
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Sakkwato Kasafi Jihar Sokoto
এছাড়াও পড়ুন:
Shugabannin jam’iyyar PDP Na Arewa Sun Amince Da Turaki A Matsayin Ɗan Takarar Shugabancin Jam’iyyar Na Ƙasa
Sanarwar da aka fitar a karshen taron ta bayyana cewa, matakin na daga cikin kokarin da ake yi na karfafa hadin kan jam’iyyar da tabbatar da daidaiton wakilcin yanki a cikin tsarin shugabancin jam’iyyar PDP.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA