Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji
Published: 24th, October 2025 GMT
Ga Dukkan Alamu Kaikayi Zai Koma Kan Mashekiya Gwamna Biodun Ya Amince Da ₦70,000 Mafi Ƙarancin Albashi Ga Ma’aikatan Ekiti
Waɗannan ginshiƙai, an tsara su ne bisa manufofin sanya hannun jari a cikin dukkanin ƙananan hukumomi 16 na jihar. A cikin shekaru uku, manyan ayyuka 577 zuwa 368 aka kammala, sannan kuma 209 da ake kan gudanar da su a halin yanzu, sun shafi garuruwa da ƙauyuka sama da 200, ana kuma ci gaba da haɓaka harkokin ilimi, kiwon lafiya, wutar lantarki, noma da kuma samar da haɗin kai.
Ayyukan Da Suka Game Mutane
Babu ayyukan da Oyebanji ya yi fiye da na abubuwan more rayuwa.
Sabbin hanyoyi kamar Ikere zuwa Igbara zuwa Odo, Ogotun zuwa Ikogosi, Isinbode zuwa Ara zuwa Ikole, shataletalen titin Ado-Ekiti (Phase I), da Omu zuwa Ijelu zuwa Itapa, sun yi matuƙar buɗe sabbin hanyoyin tattalin arziƙi.
Haka nan, ya ƙara inganta hanyoyin birane irin su; aikin titin Otel na Spotless, ‘GRA Third Eɗtension’ da gadar sama ta Okeyinmi, wanda ake kan ginawa a halin yanzu.
Sai kuma filin jirgin saman dakon kaya na Jihar Ekiti, wanda hukumar NCAA ta share kwanan nan, don gudanar da harkokin kasuwanci, kazalika, akwai kuma wata ƙofa da ke sanya Ekiti a matsayin cibiyar dabarun Kudu-maso-Yamma.
Saka hannun jari mai kama da juna, gami da Cibiyar Fasaha da Al’adu ta ƙasa da ƙasa da kuma ɗakin jinya mai gadaje 80 a babban asibitin koyarwa na jihar ta Ekiti (KSUTH), na nuna kyakkyawan nazarin gwamnatin fiye da wa’adin sa. Ya gina ba don yabo ba, sai don ya bar tarihi.
Yin Noma A Matsayin Tanadi
Noma na ɗaya daga cikin tsarin tattalin arziƙin da Oyebanji ya sanya a gaba. Sama da matasa 5,000 ne suka tsunduma cikin harkar noma da hada-hadar kasuwancinsa, ƙarƙashin wasu tsare-tsare irin su kiwon kaji ‘Broilers Scheme’ a gonar Erifun da kuma shirin dawo da matasa harkar noma.
Zuba hannun jarin da gwamnati ta yi a fannin da kuma share filaye kyauta, ɗakunan kwanan ɗalibai, taraktoci da na’urorin gona na zamani a yankin gonar Oke Ako, ya inganta samar da abinci da ayyukan yi a karkara.
Har ila yau, domin kiyaye filayen noma, an ɗauki ma’aikatan Amotekun 400 da kuma masu aikin gona, suna tsaron al’umma kai tsaye tare sauran amfanin na gona.
Yadda Ya Bai Wa Ilimi Muhimmanci
Ga Gwamna Oyebanji, batun ilimi ya wuce a ce ana kashe kudi; illa wani abu ne da ke kama da zuba jari.
Ya ƙara ba da tallafin karatu a duk wata ga manyan makarantu daga Naira miliyan 767.8 zuwa Naira biliyan 1.27, tare da kawar da basussukan albashi da inganta hanyoyin samar da kuɗaɗe.
A duk faɗin ƙananan hukumomi, an sake gina ɗaruruwan ajujuwa da ɗakunan gwaje-gwaje, cibiyar ayyuka ta yara masu nakasa da kuma azuzuwa 16 da aka sanya wa alluna koyo na zamani.
Sai kuma, ɗaukar malaman makaranta 1,600 da wasu ma’aikata 200, ya ƙarfafa ingancin koyarwa, tare da tabbatar da cewa; koɗawane ajujuwa sun ci gaba da kasancewa kamar yadda ya kamata.
Ya kuma ɗauki kowane ajujuwa a matsayin shukar da ya yi, kana kuma zai girbe gobe.
Lafiya Ita Ce Komai
A ɓangaren kiwon lafiya, gwamnati ta bayar da sakamakon da ake buƙata.
Sashin kula da lafiyar jarirai da cibiyoyin diyya na EKSUTH, na kula da dubban mutane a halin yanzu; ana kan gina katafaren asibiti mai gadaje 80 da manyan asibitoci biyar a Oye, Ijan da Ifaki Ekiti, inda ake yin gyaransu baki-ɗaya.
A ɓangaren tsarin Inshorar Lafiya ta Jihar Ekiti, ’yan fansho 19,000 ne ke samun kulawa ta fuskar kiwon lafiya kyauta. Sama da 3,700 an yi musu tiyata kyauta, an yi wa aƙalla mutum 600,000 gwajin zazzaɓin cizon sauro, sannan an rarraba magungunan kimanin 500,000 a dukkanin faɗin jihar.
An kuma ɗauki wasu ƙwararru a ɓangaren na kiwon lafiya su kimanin 250 aiki, domin tabbatar da kulawa ta isa ga waɗanda suka taɓa jin kamar an manta da su.
Gwamnatin Kowa Da Kowa Wadda Ke Ƙoƙarin Kare Lafiyar Jama’a
Haɗuwa da jama’a ya zama alamar jagorancin Oyebanji.
Gwamnatinsa ta gyara gidan kula da mata da ’yan matan da aka yi watsi da su tare da samar da kayayyakin sana’o’i ga nakasassu da kuma gudanar da ayyukan shawo kan ambaliyar ruwa da ta kai sama da Naira miliyan 300 a ƙarƙashin shirin nan ‘WASH’.
Sabbin hanyoyin magudanar ruwa a Ado ta Ekiti, sun yi matuƙar rage haɗarin ambaliya, yayin da ƙarin layukan wutar lantarki na kƁ 33 da na IPP suka inganta samar da wutar lantarki ga manyan cibiyoyin gwamnati.
Dawo Da Martabar Ma’aikata
Ɗaya daga cikin ma’anar mulkin Oyebanji, shi ne tausayawa al’umma. Ya ɓullo da tsarin ɗaukar jama’a a mota kyauta, musamman ma’aikatan gwamnati da ɗalibai, ya kuma kawar da basussukan fansho da aka daɗe ana bin su, ya biya Naira biliyan 4.9 ga ‘yan fansho su kimanin 2,260 kashi na farko, Naira biliyan 1.3 zuwa 348 da suka yi ritaya a Ƙaramar Hukumar Ado da kuma sama da Naira biliyan 40 a faɗin jihar cikin shekaru uku kacal. Yana mulki cikin tausayawa, sannan kuma Jihar Ekiti ta san haka.
Tallafa Wa Matasa Da Kuma Masana’antu
Matasan Jihar Ekiti, sun samu kulawar gaske a ƙarƙashin Oyebanji.
Cibiyar koyar da dabarun sana’o’i da ke Ado Ekiti, Aso-Oke da kuma gyaran rukunin yaɗuwar Oodua, sun sake farfaɗo da masana’antun gargajiya da na ƙere-ƙere.
Ta hanyar haɗin gwiwa da SMEDAN, sama da matasa 5,000 aka horar kan harkokin kasuwanci da na ilimin kuɗi, yayin da masu sana’a 250 suka samu takardun shaida na kasuwanci da kuma matakai na gaske don dogaro da kai na matasa.
Samun Haɗin Kai A Gwamnati
Wataƙila babbar nasarar Oyebanji, ta ta’allaƙa ne kan samun haɗin kai a siyasance. Domin kuwa, ya samu nasarar haɗa kan ‘yan siyasar Jihar Ekiti wanda ba kasafai aka cika samu ba.
Duk tsofaffin gwamnonin da aka yi a baya kamar Niyi Adebayo, Ayo Fayose, Segun Oni da Kayode Fayemi, sun yaba wa ƙasƙantar da kansa ta hanyar rashin girman kai.
Shugaban majalisar dattawa, Opeyemi Bamidele ya bayyana shi a matsayin ‘mutumin da ba kasafai ake samun irinsa wajen tawali’u da sauƙin kai ba.
Wannan yarjejeniya ta haifar da kwanciyar hankali a siyasa, wanda ya ba da damar ci gaba mai ɗorewa da kwanciyar hankali na rayuwar jama’a.
Daga Farkon Rayuwarsa Zuwa Samun Ɗaukakarsa
An haife shi a ranar 21 ga Disambar 1967, a Ikogosi-Ekiti, Oyebanji yana alfahari da zama a gida Nijeriya. Ya yi digirinsa na farko a fannin Kimiyyar Siyasa B.Sc. daga Jami’ar Jihar Ondo (yanzu EKSU) da kuma digirinsa na biyu M.Sc. a fannin hulɗa da ƙasa da ƙasa daga Jami’ar Ibadan.
Tsohon malami ne, ma’aikacin banki, kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka ƙirƙiro Jihar Ekiti a shekarar 1996, ya kwashe sama da shekaru 11 yana aikin gwamnati.
Ya auri Dakta Olayemi Oyebanji, babbar malama a jami’ar Ibadan, Allah ya albarkace su da samun ‘ya’ya uku.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: Naira biliyan kiwon lafiya Jihar Ekiti
এছাড়াও পড়ুন: