Aminiya:
2025-10-24@18:20:24 GMT

’Yan sanda sun sake kama Sowore bayan kotu ta bayar da belinsa

Published: 24th, October 2025 GMT

’Yan Sanda sun sake kama dan gwagwarmaya kuma mamallakin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore, bayan wata kotun Majistare da ke Abuja, ta bayar da belinsa. 

An sake kama Sowore bayan kotu ta bayar da belinsa tare da wasu mutum 12 a ranar Juma’a.

Tinubu ya sauke hafsoshin tsaro, ya maye gurbinsu da wasu Gwamnonin PDP na yanzu za su rusa mana jam’iyya — Wike

Alƙalin kotun, Abubakar Sai’id ne, ya bayar da belin Sowore da wasu mutum 12 da aka tuhuma da tayar da hankalin jama’a, sakamakon zanga-zangar #FreeNnamdiKanuNow da aka gudanar a Abuja a ranar Litinin.

Lauyan Sowore, Tope Temokun, ya zargi ’yan sanda da yin amfani da karfi, inda suka yi awin gaba ba tare da wani bayani ba.

Temokun ya bayyana cewa: “Bayan kotu ta bayar da belin Sowore, sai wasu ’yan sanda ƙarƙashin jagorancin CSP Iliyasu daga Sashen CID suka mamaye harabar kotun, inda suka sa masa da sauran jama’ar da ke wajen duka, sannan suka tafi da Sowore a bainar jama’a.

“A kokarin dakatar da su na ji rauni.”

Ya ƙara da cewa ba a kai Sowore gidan yari ba, amma an tafi da shi wani waje daban wanda ba wanda ya sani.

Kotun ta bayar da belin Sowore da sauran waɗanda ake tuhuma; ciki har da Aloy Ejimakor lauyan shugaban IPOB Nnamdi Kanu da kuma ɗan uwan Nnamdi Kanu, Emmanuel Kanu, kan kudi Naira 500,000 kowanne.

Kotu ta kuma umarce su da su miƙa fasfo ɗinsu, tare da katin shaida dan kasarsu da takardun biyan haraji na shekaru uku kafin a sake su.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ’yan sanda ba su fitar da wata sanarwa ba game da sake kama Sowore ba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda ta bayar da

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnonin Arewa sun yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a fashewar tanka a Neja

Ƙungiyar Gwamnonin Arewa (NSGF), ta bayyana hatsarin fashewar tankar mai da ya auku a ƙauyen Essa a Ƙaramar Hukumar Katcha a Jihar Neja, a matsayin abin baƙin ciki da tausayi.

Shugaban ƙungiyar kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ne, ya yi alhinin lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Waɗanda ke son rusa Kano ba za su yi nasara ba — Sanusi II Majalisar Yobe ta nemi a dauki mataki kan yawaitar hadura a hanyar Damaturu–Potiskum

Ya miƙa saƙon ta’aziyyae ga gwamnatin Jihar Neja da al’ummarta da kuma iyalan da abin ya shafa.

“Wannan lamari abin baƙin ciki ne ƙwarai da gaske. Addu’o’inmu suna tare da iyalan mamatan da kuma jama’ar Jihar Neja a wannan lokaci na jimami,” in ji Yahaya.

Ya kuma gargaɗi jama’a da su guji ɗibar man da ya zube a kan hanya saboda guje wa hatsari.

“Wannan mummunan lamari ya sake tunatar da mu buƙatar tabbatar da ingantattun matakan tsaro da kuma ƙara wayar da kan jama’a game da hatsarin dakon mai.

“Gwamnati, hukumomi da jama’a dole su haɗa kai don hana aukuwar irin waɗannan abubuwan da za a iya gujewa,” in ji shi.

Gwamnan, ya yaba da ƙoƙarin ma’aikatan ceto, jami’an tsaro, da ‘yan sa-kai waɗanda suka yi aiki tuƙuru wajen ceto waɗanda abin ya rutsa da su.

Ya yi addu’ar Allah Ya jiƙan waɗanda suka rasu, Ya kuma bai wa waɗanda suka jikkata lafiya.

Gwamnan, ya kuma tabbatar da cewa ƙungiyar za ta ci gaba da aiki tare da hukumomin gwamnati na tarayya da na jihohi domin ƙarfafa tsarin kare rayuka da dukiyoyin al’umma a yankin.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ‘Yan sanda sun kama ɗalibi da ya soki Gwamnan Neja
  • Ƴansanda Sun Sake Kama Sowore Bayan An Bayar Da Belinsa
  • Ƴansanda Sun Sake Kama Sowore Bayan An Bayar Da Shi Beli
  • Nnamdi Kanu Ya Sake Bayyana A Kotu Ba Tare Da Lauya Ba, Zai Kare Kansa Da Kansa
  • Sojoji Sun Kama Fitaccen Ɗan Bindiga Babawo Badoo Da Wasu 37 A Filato 
  • Jami’an tsaro sun kama Sowore saboda shirya zanga-zanga
  • ISWAP: Mun kawar da duk wata barazana — Gwamnatin Ondo
  • Gwamnonin Arewa sun yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a fashewar tanka a Neja
  • Rundunar ‘Yan Sanda A Jihar Zamfara Ta Gargadi Direbobi Game Da Rufe Lambar Mota