Majalisa ta amince a ƙirƙiro sabbin jihohi 6 a Najeriya
Published: 26th, October 2025 GMT
Kwamitin Haɗin Gwiwa na Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai kan gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya, ya amince da buƙatar ƙirƙiro sabbin jihohi guda shida.
Wannan mataki na cikin abin da aka cimma a ƙarshen taron kwana biyu da aka gudanar a Legas, ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I.
A cewar kwamitin, an tattauna kan buƙatu 69, ciki har da buƙatun ƙirƙirar jihohi 55 da kuma ƙananan hukumomi 278.
Daga cikin buƙatun ƙirƙirar jihohi 55 da aka gabatar, kwamitin ya amince da ƙirƙirar jihohi shida; ɗaya daga kowanne yanki.
“Za mu binciki dukkanin buƙatun ƙirƙirar jihohi 55 da aka gabatar domin gano inda za a fitar da sababbin jihohi shida.
“Za mu yi wa kowa adalc,” in ji ɗaya daga cikin mambobin kwamitin daga yankin Arewa Maso Yamma.
Idan Majalisar Tarayya ta amince da wannan yunƙuri gaba ɗaya, Najeriya za ta koma tana da jihohi 42 maimakon 36 da ake da su yanzu.
Wannan mataki, a cewar wani babban jami’in majalisar, “Yana nuna adalci da daidaito ga dukkanin yankuna,” kuma za a gabatar da rahoton kwamitin ga duka majalisun a farkon makon Nuwamba.
Sanata Barau, ya ce burin majalisar shi ne tabbatar da cewa duk wasu sauye-sauye da za a yi wa kundin tsarin mulki su kasance waɗanda za su amfani al’umma, tare da cika alƙawarin da aka ɗauka na tura sabon ƙudiri zuwa majalisun dokoki na jihohi kafin ƙarshen wannan shekara.
“Mun shafe sama da shekaru biyu muna taro da al’umma, ƙungiyoyi, da masana domin samun ra’ayoyi game da yadda za a inganta tsarin mulkin ƙasar nan,” in ji shi.
Taron na Legas ya kasance dama ga mambobin majalisar domin su nazarci sauye-sauyen da ake son yi, musamman batutuwan da suka shafi ƙirƙirar sabbin jihohi, daidaita iyakoki, da ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gyaran Kundin Tsarin Mulki iyakoki Kwamiti Majalisar Dattawa Majalisar Wakilai Sanata Barau ƙirƙirar jihohi
এছাড়াও পড়ুন:
Najeriya za ta buga wasan sada zumunta da Masar kafin fara gasar AFCON ta 2025
Tawagar Super Eagles ta Najeriya za ta buga wasan sada zumunta da ƙasar Masar kafin fara gasar Kofin Afrika da za a yi a Maroko.
Wasan zai gudana ne a ranar 11 ga wata. Disamba, da misalin ƙarfe 7 na dare, a filin wasa na Cairo da ke Masar.
EFCC ta tsare Malami kan binciken kuɗaɗen Abacha Real Madrid za ta ɓarje gumi da Manchester City a SantiagoZa a yi wasan ne kwana shida kafin a fara gasar da ƙasashe 24 za su fafata a cikinta.
Najeriya za ta fara wasanta na farko a ranar 23 ga watan Disamba da Tanzania.
Ita kuwa Masar za ta buga wasanta na farko da Zimbabwe a ranar 22 ga watan Disamba.
A tarihi, Masar ce tafi lashe Kofin Afrika inda ta lashe gasar sau bakwai, yayin da Najeriya ta lashe sau uku.