Kwamishinan Gombe ya rasu a hatsarin mota
Published: 25th, October 2025 GMT
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Gombe, Kanal Abdullahi Bello (mai ritaya), ya rasu a hatsarin mota.
Gwamnatin Jihar Gombe ce, ta sanar da rasuwar cikin wata sanarwa da Daraktan Harkokin Watsa Labarai, Ismaila Uba Misilli, ya fitar a ranar Juma’a.
Tinubu ya faɗa wa ’yan Najeriya dalilin sauya hafsoshin tsaro — ADC Gwamnan Bauchi ya naɗa ɗan uwansa a matsayin sabon Sarkin DuguriSanarwar ta ruwaito cewa Bello ya rasu a kan hanyar Malam Sidi zuwa Gombe, bayan aukuwar wani mummunan hatsarin mota.
“Gwamnatin Jihar Gombe na cikin jimamin sanar da rasuwar Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Kanal Abdullahi Bello (mai ritaya), sakamakon a hatsarin mota da ya rutsa da shi a kan hanyar Malam Sidi zuwa Gombe,” in ji Misilli.
Sanarwar, ta bayyana cewa Bello ya rasu tare da wani jami’in ɗan sanda da ke tare da, Sajan Adamu Husaini.
Hatsarin ya rutsa da su yayin da suke dawowa daga Maiduguri, Jihar Borno, inda suka halarci wani taro na yankin Arewa Maso Gabas.
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana labarin rasuwar Kwamishinan a matsayin abun baƙin ciki.
Ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai biyayya, jajircewa da yi wa jama’a hidima, wanda ya nuna ƙwarewa wajen jagoranci da kishin ƙasa a ayyukansa a Gombe.
“Kanal Bello (mai ritaya) zai kasance abin koyi wajen biyayya, hidima ba tare da son kai ba.
“Ya gudanar da aikinsa da himma. Rashinsa babban giɓi ne ba wai ga iyalansa da gwamnatinmu ba, har ma da Jihar Gombe da Najeriya baki ɗaya,” in ji gwamnan.
Gwamnan ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, abokan aikinsa, da al’ummar Ƙaramar Hukumar Balanga.
Hakazalika, ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan jami’in ɗan sandan da ya rasu tare da Kwamishinan.
Ya yi addu’ar Allah Ya gafarta musu tare da sanya su a Aljanna Firdausi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: hatsarin mota Kwamishinan Tsaro rasuwa hatsarin mota Jihar Gombe
এছাড়াও পড়ুন:
Jihar Kwara Ta Ware Naira Biliyan 8 Don Biyan Haƙƙin Ma’aikatan Da Suka Yi Ritaya
Gwamnatin Jihar Kwara ta ware kimanin Naira Biliyan 8 da miliyan dari daya domin biyan haƙƙin fansho da giratuti na ma’aikatan jiha da na kananan hukumomi da suka yi ritaya.
Kwamishinan Kuɗi na Jihar, Dakta Hauwa Nuhu, ce ta bayyana haka a yayin taro da ma’aikatun gwamnati karo na uku, wanda aka gudanar a zauren taro na ma’aikatar kuɗi a Ilori.
A cewarta, za a raba Naira Biliyan biyar da miliyan dari shida ga tsoffin ma’aikatan jiha a matsayin giratuti, yayin da aka ware Naira Biliyan biyu da miliyan dari biyar domin tsoffin ma’aikatan kananan hukumomi.
Dakta Nuhu ta jaddada cewa gwamnatin jiha za ta ci gaba da biyan fansho da giratuti a hankali domin tabbatar da cewa sauran ayyukan ci gaban jama’a ba su tsaya ba.
Ta bayyana cewa adadin giratuti da fansho ya ninka saboda aiwatar da sabon tsarin albashi na Naira Dubu Talatin da Naira Dubu Saba’in, tare da daidaiton da aka yi ga masu ritaya.
Kwamishinar ta kuma tabbatar da cewa babu wani tsohon ma’aikacin karamar hukuma ddake bin gwamnati bashi, sai waɗanda suka ƙi bayyana a lokacin tantancewar da aka gudanar a dukkanin kananan hukumomi 16 na jihar.
Ali Muhammad Rabi’u