Aminiya:
2025-10-23@12:52:33 GMT

DSS ta cafke mutum 3 kan zargin sayar wa ’yan bindiga makamai a Kaduna

Published: 23rd, October 2025 GMT

Jami’an Hukumar Tsaro ta DSS sun kama wasu mutum uku da ake zargi da sayar da wa ’yan bindiga makamai da harsasai a Jihar Kaduna.

An kama su ne bayan wani samame da jami’an DSS suka kai a ƙananan hukumomin Igabi da Kachia.

’Yan uwana 8 sun rasu a fashewar tanka a Neja — Wani Mutum Tun da PDP ta bar mulkin Najeriya maguɗin zaɓe ya ragu – Akpabio

An kama ɗaya daga cikinsu mai shekaru 30, a kan titin Nnamdi Azikiwe Bypass da ke Igabi.

An gano bindiga ƙirar AK-47 guda biyu, bindigar PKT guda ɗaya, harsasai sama da 200.

Sauran mutum biyu kuma an kama su ne a ƙauyen Doka da ke Ƙaramar Hukumar Kachia, a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

An kama su suna ƙoƙarin yi wa ’yan bindiga safarar AK-47 guda uku a cikin wata mota ƙirar Volkswagen Golf.

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya yaba wa hukumar DSS bisa wannan nasara, inda ya ce gwamnatinsa ba za ta bar wani ɗan ta’adda ko mai aikata laifi ya samu mafaka a jihar ba.

Ta bakin Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Barista Sule Shuaibu, gwamnan ya kuma gode wa Shugaba Bola Tinubu da Darakta-Janar na DSS bisa goyon bayan da suke bai wa tsaro a jihar.

Ya ce tsarin zaman lafiya da gwamnatinsa ta ƙirƙiro wanda ya haɗa da tattaunawa da haɗin kai a tsakanin al’umma ya taimaka wajen rage laifuka a faɗin jihar.

Ya gargaɗi masu aikata laifi da su daina ko kuma su fuskanci hukunci mai tsanani.

Hukumar DSS ta ce tana gudanar da bincike a kan waɗanda ta kama, kuma za ta tabbatar da cewa an hukunta su.

Hakazalika, ta jaddada ƙudirinta na daƙile safarar makamai a Jihar Kaduna.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Safarar Makamai zargi

এছাড়াও পড়ুন:

‘Yansanda Sun Cafke Wani Matashi Ɗan Shekara 15 Da Ake Zargi Da Yin Fashi Da Makami A Gombe

A cewar sanarwar, “A ranar 15 ga Oktoba, 2025, da misalin karfe 11:00 na rana, wata mata da ke zaune a unguwar Federal Low-Cost, Gombe, ta bayyana cewa a daidai wannan ranar da misalin karfe 2:30 na dare, wani wanda ba ta san ko wanene ba, dauke da wuka ya kai mata hari, inda ya sace mata kayanta.

 

“Abubuwan da aka sace, sun haɗa da iphone 13 Pro Max, an kimanta kudinta akan ₦800,000, kwamfutar ‘Apple MacBook’ da darajarta ta kai ₦250,000, da agogon ‘Apple’ da darajarsa ta kai ₦35,000, ‘power bank’ na Oraimo wanda darajarsa ta kai ₦30,000, da jakar makaranta akan darajar ₦25,000.”

 

Abdullahi ya ce, nan take jami’an ‘yansanda na shiyyar suka dauki matakin kama wanda ake zargin tare da kwato dukkan kayayyakin da aka sace.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Tinubu Ya Amince Da Tallafin Naira 250,000 Ga Ƙananan ’Yan Kasuwa A Jihar Katsina October 22, 2025 Labarai Majalisa Ta Buƙaci Gwamnatin Tarayya Ta Kai Agajin Gaggawa Ga Waɗanda Fashewar Tanka Ta Shafa A Neja October 22, 2025 Manyan Labarai Gwamna Uba Sani Ya Rantsar Da Sabon Kwamishinan Yada Labarai Ahmed Maiyaki  October 22, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yadda DSS Suka Kama Masu Safarar Makamai Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kaduna
  • Jami’an tsaro sun kama Sowore saboda shirya zanga-zanga
  • ’Yan uwana 8 sun rasu a fashewar tanka a Neja — Wani Mutum
  • Dangote zai sayar da kaso 10 na hannun jarin matatar man shi
  • ‘Yansanda Sun Cafke Wani Matashi Ɗan Shekara 15 Da Ake Zargi Da Yin Fashi Da Makami A Gombe
  • Hukumar Alhazai Ta Jihar Kaduna Ta Sanar Da Wa’adin Biyan Kafin Alkalami Na Shekarar 2026
  • Uba Sani ya yi wa ma’aikatan manyan makarantu ƙarin kashi 70 a albashi
  • Ma’aikatan Manyan Makarantu Na Kaduna Sun Dakatar Da Yajin Aiki Yayin Da Gwamna Sani Ya Amince Da Sabon Tsarin Albashi
  • Bidiyoyin baɗala: Kotu ta umarci Hisbah ta daura aure tsakanin ’yan TikTok