Gwamna Yusuf Ya Gwangwaje Kano Pillars Da Sabbin Motocii
Published: 23rd, October 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ta bai wa ƙungiyar kwallon ƙafa ta Kano Pillars Football Club sabbin motoci uku domin sauƙaƙa musu matsalolin sufuri a yayin gasar Premier ta shekarar 2025/2026 da ke gudana.
Motocin sun haɗa da babbar motar Marcopolo mai kujeru 29 don ɗaukar ’yan wasa, motar samfurin Hummer, da kuma Sharon da za a yi amfani da ita wajen harkokin gudanarwa da sufuri.
A lokacin da yake mika makullai da takardun motocin a madadin Gwamnan, Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Malam Ibrahim Umar Farouk, ya roƙi matasan jihar masu son wasanni da su ci gaba da zama masu bin doka da oda tare da guje wa duk wani abu da zai bata sunan jihar.
Ya bayyana cewa wannan kyauta ta nuna yadda Gwamna Yusuf ke da ƙwarin gwiwa wajen ƙarfafa matasa da bunƙasa harkokin wasanni a jihar.
A nasa jawabin, Kwamishinan Matasa da Wasanni, Mustapha Kwankwaso, ya bayyana godiyarsa ga Gwamna Yusuf bisa wannan babban ci gaba da zai ƙara wa ’yan wasan kwarin gwiwa da jin daɗin aiki.
Ya kuma yi kira ga magoya bayan ƙungiyar Sai Masu Gida da su kasance masu ladabi da biyayya tare da ci gaba da nuna goyon baya cikin lumana.
Da yake mayar da martani, Manajan Janar na Kano Pillars FC kuma kyaftin ɗin Super Eagles, Ahmed Musa (MON, OON), ya yaba wa Gwamna Yusuf bisa goyon baya da ƙaunar da yake nuna wa ƙungiyar.
Ahmed Musa ya kuma roƙi gwamnatin jihar da ta ba da girmamawa ta musamman ga tsohon kyaftin ɗin ƙungiyar, Rabiu Ali, domin tunawa da gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa kwallon ƙafa a Najeriya, yana mai kiran sa da “ɗaya daga cikin fitattun ’yan wasa mafiya tasiri da suka taka leda a tarihin NPFL.”
A halin yanzu, ƙungiyar Kano Pillars za ta karɓi bakuncin Niger Tornadoes ta Minna a wasansu na ranar goma ta gasar NPFL a wannan Asabar, a filin wasa da suka ɗauka a matsayin gida na wucin gadi — Filin Muhammadu Dikko da ke Katsina.
Khadijah Aliyu
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Gwamna Yusuf Kano Pillars
এছাড়াও পড়ুন:
Fyaɗe ga ’yar shekara 12 ya ja wa matashi ɗaurin rai-da-rai a Yobe
Kotu ta yanke wa wani wanda ya yi wa wata yarinya ’yar shekara 12 fyaɗe hukuncin ɗaurin rai-da-rai a Ƙaramar Hukumar Guba ta Jihar Yobe.
Babbar Kotun Jihar Yobe da ke zaune a ƙaramar hukumar Gujba ta yanke wa mutumin mai shekaru 31 mai suna Ali Kwano.
An gurfanar da shi ne a kan zargin ya kai yarinyar cikin aji a ƙaramar makarantar sakandare ta je-ka-ka-dawo da ke garin Bumsa, inda ya yi lalata da ita da ƙarfi.
Ya yaudari yarinyar ce bayan ya gaya mata cewa ta jira shi a cikin aji bisa cewar zai sayi ƙosai.
Bayan da ta shiga ajin sai ya kama hannunta, ya rufe bakinta ya danne ta a ƙasa sannan ya yi lalata da ita da ƙarfi.
Ƙasashen waje na taimaka wa ’yan ta’adda a Najeriya —Sheikh Gumi ’Yan sanda sun kama tsohon shugaban PCACC, Muhuyi Rimin Gado a KanoAlƙaliyar da ke jagorantar shari’a, Mai Shari’a Amina Shehu, ta same shi da laifi, don haka ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai-da-rai bisa ga sashe na 3 na dokar haramta cin zarafin mutane, ta Jihar Yobe ta Shekarar 2020.