Aminiya:
2025-10-26@09:36:24 GMT

Sojoji sun daƙile harin ISWAP a Borno

Published: 26th, October 2025 GMT

Dakarun rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) sun daƙile harin da ’yan ta’addan ISWAP suka kai a garin Gamborun Ngala da ke kan iyakar Najeriya da ƙasar Kamaru.

Rahotanni daga rundunar sun nuna cewa an kai harin ne da misalin ƙarfe 6:15 na yammacin ranar Asabar, inda aka ji ƙarar harbe-harbe masu ƙarfi a sassa daban-daban na garin.

ABU ta musanta zargin ƙera makamin nukiliya a ɓoye An ba da tallafin N2m ga iyalan jami’in NSCDC da aka kashe a Jigawa 

Sai dai a cewar majiyoyi, sojojin sun mayar da martani cikin gaggawa, inda suka shiga fafatawa da ’yan ta’addan, kuma suka fatattake su ba tare da wata asara a ɓangaren dakarun ba.

Wakilinmu ya ruwaito cewa babu wani soja ko farar hula da ya rasa ransa ko ya jikkata, yayin da aka samu cikakken kwanciyar hankali a garin bayan da aka daƙile harin.

A yanzu dai, harkokin yau da kullum sun kankama a Gamborun Ngala, inda mazauna garin ke jinjina wa sojojin bisa jajircewarsu da nasarar da suka samu wajen kare al’umma daga wannan mummunan hari.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: ISWAP jihar Borno Operation Hadin Kai

এছাড়াও পড়ুন:

An kama Sakataren APC na mazaba a Yobe kan zargin aikata kisan kai

Rundunar ’Yan Sandan jihar Yobe ta ce ta cafke wani shugaban mazaba na jam’iyyar APC a karamar hukumar Karasuwa bisa zarginsa da hannu a kisan wata mata.

Rundunar ta ce ta samu nasarar ce a binciken da take yi kan wata gawar da aka gano a kusa da Jami’ar Tarayya da ke Gashuwa a makon da ya gabata.

Gwamnan Neja ya ba dukkan iyalan wadanda suka kone a gobarar tankar mai N1m Tinubu ya bukaci sabon shugaban INEC ya gudanar da zaben gaskiya a 2027

A cewar sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Dungus Abdulkarim, ’yan sanda daga sashin karamar hukumar Bade sun kama wani mutum mai suna Abdulmumini Garba, mai shekaru 60, dangane da mutuwar matar mai suna Falmata Abubakar, ‘yar shekara 45 da haihuwa.

Rahoton ya nuna cewa wanda ake zargin mazaunin Gasma ne a karamar hukumar Karasuwa, kuma yana rike da mukamai biyu: Sakataren APC na Mazava a Karasuwa da Sakataren Kasuwar Gwari a Gashuwa.

‘Yan sanda sun ce an kama Garba ne bayan gudanar da bincike mai zurfi da kuma kokarin leƙen asiri da suka yi a ranar 17 ga watan Oktoba, 2025.

Lokacin da ake masa tambayoyi, Garba ya amsa cewa shi ne ya kashe Falmata Abubakar a cikin motarsa, bayan samun sabani tsakaninsu.

An bayyana cewa rikicin ya samo asali ne daga bukatar marigayiyar na neman taimakon kuɗi don tallafa wa sana’arta, wanda ya rikide zuwa tashin hankali da ya haifar da mutuwarta.

Bayan mutuwar, wanda ake zargin ya ce ya jefar da gawar a daji da ke kusa da wajen da misalin ƙarfe 10 na dare, inda daga bisani aka gano gawar.

Rundunar ’yan sanda ta bayyana wannan ci gaba a matsayin shaida ta ƙwazo da dabarun tattara bayanai da suka taimaka wajen gano wanda ake zargi cikin gaggawa.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Emmanuel Ado, ya jinjina wa jami’an sashin Bade bisa ƙwarewa da jajircewarsu, tare da jaddada aniyar rundunar na ganin an samu adalci.

CP Ado ya tabbatar wa da jama’a cewa za a kammala bincike cikin tsanaki, sannan a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu da zarar an kammala binciken.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka
  • Rear Admiral Sayyari: Sojojin Iran A Shirye Suke Su Fuskanci Kowace Barazana
  • ‘Yan sanda sun kama ɗalibi da ya soki Gwamnan Neja
  • An kama Sakataren APC na mazaba a Yobe kan zargin aikata kisan kai
  • Buƙatar Daƙile Badaƙalar Amfani Da Takardun Karatun Bogi A Nijeriya
  • Rasha ta miƙa wa Ukraine sojoji 1,000 da suka mutu a fagen daga
  • Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 50, Sun Daƙile Hare-Hare A Borno
  • An kashe manoma uku da suke girbin amfanin gona a Filato
  • Boko Haram sun kai sabbin hare-hare a wasu yankunan Borno da Yobe