Matsalar kashe-kashe a Nijeriya ba ta da alaƙa da addini — Femi Kayode
Published: 26th, October 2025 GMT
Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Cif Femi Fani-Kayode, ya bayyana cewa matsalar kashe-kashen da ake fama da su a sassa daban-daban na ƙasar nan ba ta da alaƙa da addini, illa dai ayyukan miyagu da ke kashe Musulmi da Kirista ba tare da la’akari da bambancin addini ba.
Fani-Kayode ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi a matsayin bako mai jawabi a taron cika shekaru 35 da kafuwar Cocin Anglican da ke garin Kafanchan a Jihar Kaduna.
Tsohon Ministan ya ce lokaci ya yi da ‘yan Najeriya za su dawo daga rakiyar mutanen da ke amfani da addini wajen raba kan al’umma, yana mai cewa masu kashe Kiristoci su ne dai ke kashe Musulmi.
Ya buƙaci mabiya addinan biyu da su rungumi zaman lafiya, haɗin kai da fahimtar juna, tare da guje wa duk wani yunƙurin na kawo rarrabuwa ko tashin hankali.
A nasa ɓangaren, Babban Mai Shari’a na Jihar Kaduna, Barista James Kanyip, wanda ya wakilci Gwamnan Jihar, Sanata Uba Sani, ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar na ci gaba da kare ‘yancin addini da tabbatar da haɗin kai da shugabannin addinai, musamman masu wa’azin zaman lafiya da jituwa.
Shi ma Bishop Markus Dogo na Cocin Anglican da ke Kafanchan, ya bayyana irin ayyukan jin ƙai da cocin ya gudanar cikin shekaru 35, ciki har da gina makarantu, asibitoci da cibiyoyin koyon sana’o’i don tallafa wa marasa galihu.
Haka kuma, Sanatan Kaduna ta Kudu, Barista Sunday Marshall Katung, wanda ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Jema’a da Sanga, Hon. Daniel Amos ya wakilta, ya yaba wa Gwamna Uba Sani bisa yadda yake tafiyar da mulki cikin adalci da rashin nuna wariya ga kowane ɓangare na jihar.
Taron ya samu halarci manyan shugabannin addini, na siyasa da na al’umma, inda suka jaddada muhimmancin zaman lafiya da haɗin kai a matsayin ginshiƙai na ci gaban Najeriya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Femi Fani Kayode
এছাড়াও পড়ুন:
Saurayi ya kashe budurwarsa sannan ya soya qwaqwalwarta
Saurayi ya kashe budurwarsa sannan ya soya qwaqwalwarta
Koda a cikin jerin masu kisan gilla, mai cin naman mutane a Rasha Dmitry Luchin ya ci ya kasance matsayin xaya daga cikin mutune mafi munin xabi’a da rashin tausayi da suke rayuwa a duniya.
Xan ina da kisan, yanzu ya kasance sanannen mai laifi a Rasha saboda kashe budurwarsa da ya yi a shekarar 2018. Bayanan da suka fito game da yadda wannan lamari na rashin imani ya auku ya girgiza Gabashin Turai.
Budurwarsa mai suna Budunova, wacce take da shekaru 23 kacal a lokacin, ta ziyarci saurayinta Dmitry Luchin mai shekaru 45 don yin shagalin bikin Ranar Mata ta Duniya, amma shi kuwa mugun, ba ta san cewa, yana da wata muguwar voyayyar manufa ba.
Bayan sun sha giya tare, Luchin ya xauki kwalbar giyar da ya sha ya rusa mata a ka. Inda nan take ya kashe ta. Daga nan kuma ya sa wuqa ya gididdiba ta.
Bincike ya nuna cewa, xan ina da kisan, daga nan sai ya fasa kanta ya kwashe qwaqwalwar Budunova soya ya ci. Bai tsaya a nan ba, sai kuma ya xauki jininta da ke gudana da ya xiba a kofi ya sha. Ya kuma farke cikinta, ya yanke kunnuwanta ya saka mata xaya a bakinta xayan kuma ya ajiye a cikin wani da yake ba wa kyanwarsa abinci.
Luchin, wanda aka ruwaito cewa, matsafi ne mai bautar Shaidan, ya yi tawada da jininta ya rubuta wasu alamomin shaidan a qofar xakinsa, da nufin zai kira Shaixan da kansa ya zo xakin su gana kai tsaye. Bayan ya shiga hannu, a lokacin da ake gudanar da bincike ya gaya wa ‘yan sanda cewa, ya ci qwaqwalwarta da ya soya har sau biyu saboda “yana jin daxin xanxanon.”
Masu gabatar da qara sun ce, Luchin ma’abocin kallon finafinan masu aikata kisan kai ne, sannan yana shafe sa’o’i a shafukan yanar gizo da ake koyar da kisa.
A lokacin da ake gabatar da shari’arsa, Luchin ya fara karanta wata waqa ta surkulle daga inda yake killace a cikin wani kejin qarfe. Inda ya dage yana cewa, “shi ba mahaukaci ba ne, ba xan ina da kisa ba ne kuma shi ba mai cin naman mutane ba ne,” yana bayyana kansa a matsayin, “xalibi, xan wasa kuma mawaqi”.
Alqali Alexey Stanovsky ya katse shi lokacin da ya fara yin soki-burutsun kawo labari game da wani sanannen mai kisan gillar xan qasar Soviet mai suna Andrei Chikatilo. Alqali ya yanke hukuncin cewa, Luchin yana da qoshin lafiya kuma ya yanke masa hukunci kan laifin da ya aikata na kisan gilla.
Zai yi zaman shekaru 19 a gidan yari tare da aiki mai tsanani. Maqwabtan Budunova da suka shiga cikin damuwa sun ce, ba za su tava mantawa da mugun ganin da suka yi ba. Wani daga cikin su, ya qara da cewa, ” idan na tuna abin da na gani, sai in ga kamar ba a duniyar nan abin ya faru ba. Don na ganin babu wani xan adam da zai iya yin abin da ya yi.”