Kwamishinan Ilimi Na Kano Ya Yi Kira Da A Karfafa Shugabancin Makarantu Domin Inganta Karatun Dalibai
Published: 23rd, October 2025 GMT
Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dr. Ali Haruna Abubakar Makoda, ya jaddada muhimmancin samun ƙwararrun shugabannin makarantu wajen inganta koyarwa da haɓaka sakamakon karatu a fadin makarantun jihar.
Wannan bayanin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Wayar da Kai na Ma’aikatar Ilimi, Kwamared Balarabe Abdullahi Kiru, ya sanya wa hannu.
Kwamishinan ya bayyana hakan ne a wajen taron horaswa na kwanaki biyu mai taken “Leading Learning for Gender Equality in Education” wanda British Council ta shirya domin wakilai daga jihohin Kano, Kaduna, Plateau da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT).
Dr. Makoda ya ce, jagoranci mai ƙarfi da tsari a cikin makarantu shi ne ginshiƙin cimma ingantaccen ilimi. Ya kara da cewa, shugabannin makarantu su dinga tsara ayyuka yadda ya kamata, su rika sa ido kan darussa, da kuma gano wuraren da malamai ke buƙatar ƙarin horo ko ƙwarewa.
Ya kuma jaddada buƙatar jagoranci da ba da ƙarfafawa ga malamai a kai a kai, yana mai cewa gwamnatin jihar na da cikakken shirin ci gaba da horas da malamai a matakin firamare da sakandare, tare da tabbatar da cewa ana biyan su albashi kafin ko a ranar 25 ga kowane wata.
Kwamishinan ya gode wa British Council bisa shirya wannan taro, sannan ya shawarci shugabannin makarantu da malamai da su nuna godiya ta hanyar yin aiki tukuru domin ƙara bunƙasa tsarin ilimi a Jihar Kano.
Abdullahi Jalaluddeen, Kano
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Sakandare
এছাড়াও পড়ুন:
Jihohin Jigawa, Katsina Da Kano Za Su Kaddamar Da Asusun Wutar Lantarki Mafi Girma A Najeriya
Jihohin Jigawa, Katsina da Kano sun amince da hadin gwiwa kan kasuwar wutar lantarki ta jihohi uku, tare da samun kaso a kamfanin Future Energies Africa (FEA), wanda shi ne ke da hannun jari mafi girma a Kano Electricity Distribution Company (KEDCO).
Kwamishinan wutar lantarki na jihar Jigawa, Injiniya Surajo Musa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Dutse.
Ya ce gwamnonin jihohin ukun sun cimma wannan matsaya ce a birnin Marrakech, kasar Morocco, yayin taron kolin manyan jami’ai kan samar da wutar lantarki.
Injiniya Surajo Musa ya kara da cewa a yayin taron, jihohin Kano da Katsina sun amince da yin hadin gwiwa da jihar Jigawa wajen samun kaso a Future Energies Africa, domin karfafa tsare-tsaren ci gaban KEDCO.
“Jihohin uku tare da kamfanin Future Energies Africa za su kaddamar da wani asusun samar da wutar lantarki na musamman wanda shi ne irinsa na farko da ake sa ran zai kai Naira Biliyan 50 a matakin farko, domin hanzarta samar da wuta a cikin jihohin uku,” in ji shi.
Sanarwar ta kara da cewa jihohin za su duba hanyoyin da Dokar Wutar Lantarki (Electricity Act) ta tanada, domin yin hadin gwiwa kan kasuwar wutar lantarki ta jihohin uku, inda kowanne zai amfana.
Ya ce FEA tare da gwamnonin jihohin uku za su rika gudanar da taron kasa da kasa sau daya a shekara, sannan su rika ganawa duk bayan watanni uku domin duba ci gaba da karfafa dangantakar kasuwar wutar lantarki ta Arewa maso Yamma.
Usman Mohammed Zaria