Gaza : Sabani tsakanin Isra’ila, Amurka da Masar kan mataki na biyu na tsagaita wuta
Rahotanni daga Isra’ila ne cewa sabani ya kunno kai tsakanin gwamnatin kasar da Amurka da kuma Masar kan mataki na biyu na aiwtar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da aka cimma.
Kafar yada labaran Isra’ila KAN ta bayar da rahoton cewa, an samu rashin jituwa tsakanin bnagarorin dangane da aiwatar da kashi na biyu na shirin shugaban Amurka Donald Trump na kawo karshen yakin Gaza.
Kafar yada labaran ta bayyana cewa, sabanin ya samo asali ne yayin wata tattaunawa tsakanin jami’an Isra’ila da babban jami’in leken asirin Masar Hassan Rashad, wanda ya je Isra’ila.
Rahotanni sun ce Rashad ya gana da Firaminista Benjamin Netanyahu, da Daraktan Hukumar Tsaron Cikin Gida (Shin Bet) David Zini, da sauran jami’an tsaron Isra’ila.
Daga cikin batutuwan da suka tattauna sun hada da gaggauta kafa rundunar sojin kasashen Larabawa ta kasa da kasa a Gaza.
Rahoton ya nuna cewa, Washington na son a fara mataki na biyu, yayin da Alkahira, a cikin wannan tsarin, ke son shigar da dakarun kasashen waje a Gaza cikin kwanaki masu zuwa.
Kafar yada labaran ta kara da cewa jerin sunayen kasashen da ke son aikewa da sojoji zuwa Gaza don wanzar da tsagaita bude wuta sun hada da Masar, Azarbaijan, Qatar, Jordan, Indonesia, da Turkiyya, wadanda Isra’ila ta ki amincewa da kasancewarsu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Araqchi: Akwai Sharuddan Da Iran Ta Gindaya Kafin Sake Komawa Kan Teburin Tattaunawa Da Amurka October 22, 2025 Mai Ba Da Shawara Kan Harkokin Tsaron Iraki Ya Gana Da Hafsan Hafsoshin Sojojin Kasar Iran October 22, 2025 Kasar Iran Ta Kai Hare-Hare A Wuraren Da Kawayen Isra’ila Ba Su San Da Su ba A Lokacin Yakin Kwanaki 12 October 22, 2025 Makamin Amurka Ne Ya Janyo Kisan Kiyashi A Gaza Sakamakon Wadata Isra’ila Da Makamai October 22, 2025 Korarren Jami’in Isra’ila Ya Ce: Dole Ne A Yi Bincike Kan Sakacin Da Aka Yi Har Hamas Ta Kai Hari Isra’ila October 22, 2025 Wani Masani Dan kasar Iran Ya Samu Lambar Yabo Ta WHO A Yankin October 22, 2025 Majalisar Najeriya Ta Amince Da Dokar Daurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Kananan Yara Fyade October 22, 2025 Birtaniya Ta Cire Kungiyar Tahrirush -Sham Daga Jerin Yan Ta’adda October 22, 2025 China Ta Kammala Gina Cibiyar Adana Bayanai Masu Amfani Da Karfin Iska October 22, 2025 Iran Ta Godewa Rasha Game Da Goyon Bayan Da Ta Bata A Kwamitin Sulhu Na M D D October 22, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Najeriya Ta Amince Da Dokar Daurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Kananan Yara Fyade
Majalisar Dattawa ta amince da sabuwar doka da ta tanadi daurin rai da rai ga duk wanda aka samu da laifin lalata da yaro ko yarinya karama.
Dokar na son kare hakkokin kananan yara ne, kuma ta shafi maza da mata baki daya, ba tare da wani zabi na biyan tara ba. Sanata Adams Oshiomhole (Edo ta Arewa), ya ce yara ba su da iko ko yardar wajen amincewa da yin jima’i kuma irin wannan abu na jefa su cikin tashin hankali har abada.
Da farko ya ba da shawarar a daure mai laifi na tsawon shekaru 20, amma yawancin sanatoci sun nemi hukunci mafi tsauri.
Sanata Muhammad Adamu Aliero (Kebbi ta Tsakiya) ya bayar da shawarar daurin rai da rai, kuma majalisar ta amince da wannan gyara baki daya.
Zaa tura Dokar zuwa Majalisar Wakilai don amincewa da ita kafin a aike wa Shugaban kasa sanya hannu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Birtaniya Ta Cire Kungiyar Tahrirush -Sham Daga Jerin Yan Ta’adda October 22, 2025 China Ta Kammala Gina Cibiyar Adana Bayanai Masu Amfani Da Karfin Iska October 22, 2025 Iran Ta Godewa Rasha Game Da Goyon Bayan Da Ta Bata A Kwamitin Sulhu Na M D D October 22, 2025 Sudan: Jirgin ‘Drone’ Ya Fada Kan Tashar Jiragen Sama Na Khurtum Kafin A Sake Bude Ta October 22, 2025 Sheikh Qasim: Natanyahu Ya Zubar Da Jini Mai Yawa Amma Babu Lamuni Ga Amincin Isra’ila Nan Gaba October 22, 2025 Aragchi Da Guterres Sun Tattauna Kan Gaza Da Rikicin Yemen Ta Wayar Tarho October 22, 2025 Rasha da Habasha sun tattauna kan karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu a fannin nukiliya October 22, 2025 Sayyed al-Houthi: Mun shirya dawowa fagen daga idan Isra’ila ta ci gaba da kisan kiyashi a Gaza October 22, 2025 Nigeria: “Yan Sanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Neman Sakin Jagoran ‘Yan Awaren Biafara October 21, 2025 HKI Tana Ci Gaba Da Hana Wa Falasdinawa Abinci October 21, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci