Fiye da Gidaje 280 Sun Amfana da Kwandunan Zubar Sharar a Jihar Nasarawa
Published: 23rd, October 2025 GMT
Fiye da gidaje dari biyu da tamanin (280) a Karamar Hukumar Lafia sun samu kwandunan ajiyar shara (trash bins) domin inganta kula da tsaftar muhalli da rage datti a babban birnin jihar.
An gudanar da rabon ne a birnin Lafia, ƙarƙashin jagorancin Kwamishinar Muhalli da Albarkatun Ƙasa ta Jihar Nasarawa, Dr.
Shirin wayar da kai da rabon kwandunan ya shafi wasu kananan hukumomi da suka haɗa da Karu, Keffi, Akwanga, Wamba, Obi, da Keana, inda Lafia ta fi kowa samun masu cin gajiyar wannan shiri.
A yayin taron, Dr. Margaret Elayo ta bayyana damuwarta kan yadda datti ke ƙaruwa a tituna da magudanan ruwa, lamarin da ke haifar da barazana ga lafiya da muhalli.
Kwamishinar ta yi kira da a rungumi sabon tsarin zamani na sarrafa shara zuwa dukiya (waste-to-wealth), inda ta shawarci masu karɓar kwandunan da su yi amfani da su yadda ya dace wajen zubar da kwalabe da robobin ruwan sachet, tana mai bayyana cewa ana ci gaba da haɗin gwiwa da masana’antun da ke sarrafa waɗannan kayan don sake amfani da su.
Masu cin gajiyar shirin sun yaba da wannan ƙuduri na Dr. Elayo, suna jinjinawa hangen nesanta da jajircewarta wajen kare muhalli, tare da yin alkawarin amfani da tankunan cikin gaskiya da aminci domin taimakawa wajen samar da muhalli mai tsafta a Jihar Nasarawa.
Aliyu Muraki, Lafia
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Lafiya Nasarawa
এছাড়াও পড়ুন:
Muna Samun Gagarumin Cigaba Wajen Dawo Da Zaman Lafiya A Zamfara-Gwamna Lawal
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jaddada cewa yaki da matsalar rashin tsaro a jihar nauyi ne na gwamnatinsa da sauran masu ruwa da tsaki, da ma al’umma baki.
Wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a ranar Litinin, ta ce gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake jagorantar taron majalisar zartarwa ta jihar karo na 18 da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Gusau.
Sanarwar ta ce, majalisar ta tattauna kan muhimman batutuwa da suka shafi jihar, ciki har da tsaro, ilimi, kiwon lafiya, da cigaban ayyukan raya kasa.
Dr. Lawal ya tunatar da mambobin majalisar muhimmancin hadin kan su wajen yaki da rashin tsaro a karkashin wannan gwamnati.
“Muna samun gagarumin ci gaba wajen dawo da zaman lafiya a mafi yawan sassan jihar. An raunana karfin ‘yan bindiga fiye da yadda ake gani a baya,” in ji shi.
Ya bukaci mambobin majalisar su kasance masu saurin daukar mataki, tare da kusanci da al’ummarsu da zababbun shugabannin kananan hukumomi, da kuma ci gaba da bayar da rahoton halin tsaro ga Kwamishinan Tsaro na Jihar.
“Haka kuma, mu ci gaba da addu’a domin shahidanmu da suka rasa rayukansu wajen kare jama’a,” in ji gwamnan.
Gwamna Lawal ya kuma shawarci mambobin majalisar da su ci gaba da kyakkyawar dangantaka da sauran jami’an gwamnati da zababbun wakilai domin tabbatar da ingantacciyar gwamnati da samar da ayyuka ga jama’a.
AMINU DALHATU