2025-10-23@08:47:46 GMT
إجمالي نتائج البحث: 10574

«da hukumomin tsaro»:

    Wani mutum mai suna Mallam Surajo Muhammad Shehu ya rasa ’yan uwansa takwas, lokacin da tankar mai ta yi bindiga a garin Essa da ke kan hanyar Agaie zuwa Bida, a Jihar Neja. Lamarin ya auku a ranar Talata, wanda aƙalla mutum 28 ciki har da mata da ƙanana yara, suka rasa rayukansu lokacin da tankar ta kife kuma ta kama da wuta yayin da jama’a ke ƙoƙarin ɗibar mai. Tun da PDP ta bar mulkin Najeriya maguɗin zaɓe ya ragu – Akpabio Dangote zai sayar da kaso 10 na hannun jarin matatar man shi Wasu da dama sun ji rauni kuma an garzaya da su Asibitin Gwamnatin Tarayya (FMC) da ke Bida. Shehu, ya ce mata ne suka fi...
    Gwamnatin Tarayya ta koka da cewa, duk da wayar da kan jama’a da kuma gargadin da ake ci gaba da yi, wasu mutane har yanzu suna kasada da rayukansu ta hanyar yunƙurin ɗibar mai yayin da tankunan dakon mai suka faɗi.   Ya jaddada cewa, kowace rai ta ɗan Nijeriya tana da daraja kuma irin wadannan bala’o’in da za a iya rigakafin su, na nuna bukatar kara wayar da kan jama’a game da haɗurran da ke tattare da hakan cikin gaggawa.   Ya ce, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), an umurce ta da ta hada karfi ga kokarin Gwamnatin Jihar ta hanyar samar da kayan agaji da taimakon magunguna ga wadanda abin ya shafa da iyalansu. ShareTweetSendShare...
    Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce tsarin zabe a Najeriya ya samu gagarumin ci gaba tun bayan da jam’iyyar PDP ta bar mulkin kasar a matakin tarayya. Akpabio, wanda aka zabe shi sau biyu a matsayin gwamna karkashin PDP kuma ya fara shiga majalisar dattawa a karkashin jam’iyyar, ya bayyana hakan ne a lokacin karatu na biyu a kan dokar gyaran tsarin zabe a zaman majalisa da aka yi a ranar Laraba. Dangote zai sayar da kaso 10 na hannun jarin matatar man shi NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Haraji Da Zai Fara Aiki A 2026 “Ina da tabbacin cewa ni da Sanata Abaribe, wanda muka shafe kusan shekaru 25 muna cikin...
    Hon. Musa ya kara da cewa, aikin zai mayar da hankali ne kan nazari da binciken kimiyyar kasa a yankunan da ake tunanin cewa suna dauke da uranium, danyen man fetur, da iskar gas, da nufin tattara dukkan bayanan da ake bukata don ci gaba da aiki.   A cewar kwamishinan, amincewar wani bangare ne na manufofin gwamnatin Gwamna Umar Namadi na binciko albarkatun ma’adanai na jihar don haɓaka tattalin arzikin cikin gida mai ɗorewa. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamna Uba Sani Ya Rantsar Da Sabon Kwamishinan Yada Labarai Ahmed Maiyaki  October 22, 2025 Manyan Labarai Ba A Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla A Arewacin Nijeriya – Sarkin Musulmi October 22, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa ASUU Ta...
    Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ce matatar man shi na shirin sayar da tsakanin kashi 5 zuwa 10 cikin 100 na hannun jarinta a kasuwar hannun jari ta Najeriya. Ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da S&P Global, inda ya ce ana sa ran sayar da hannun jarin a cikin shekara mai zuwa. NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Haraji Da Zai Fara Aiki A 2026 Ko Alassane Ouattara zai samu wa’adi na 4 a mulkin Ivory Coast? Dangote ya ce wannan mataki kwatankwacin irin yadda aka gudanar sayar da hannun jarin kamfanononin siminta da suga na Dangote ne. “Ba ma son mu riƙe fiye da kashi...
    Kotun kasa da kasa ta ICJ ta bayyana cewa Isra’ila ta karya dokokin kasashen duniya lokacin da ta hana shigar da kayan agaji ga Falasdinawa a Zirin Gaza. Kotun na mai bayyana cewa akwai wajabci kan Isra’ila na bayar da damar shigar da taimako cikin sauki zuwa yankin, sannan ya zama wajibi ta guji yin amfani da yunwa a matsayin makamin yaki. Kotun ta kuma bayyana cewa Isra’ila na da wajabcin hada hannu da kungiyoyin agaji na MDD, musamman Unrwa. Babban zauren MDD ne ya bukaci kotun ta bayyana ra’ayinta kan lamarin bayan da Isra’ila ta haramta ayyukan hukumar bayar da agajin jin kai ta falasdinawa cewa da Unrwa, tana mai zargin hukumar da hada kai da kungiyar Hamas. Share...
    Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya yi gargadin cewa amincewar da majalisar dokokin Isra’ila ta yi na samar da kudirorin doka da nufin tsawaita ikon Isra’ila a gabar yammacin kogin Jordan “barazana ne ga yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza. Babban jami’in diflomasiyyar na Amurka ya shaidawa manema labarai a lokacin da yake shirin tafiya Isra’ila cewa, ” wannan ba wani abu ne da za mu iya ba da goyon baya gare shi ba a wannan lokaci.” Furin nasa na zuwa ne bayan da majalisar dokokin Isra’ila ta kada kuri’a kan samar da wani kudirin mallake Gabar Yamma da Kogin Jordan a matsayin yankin Isra’ila. Kudirin wanda wani dan majalisar Isra’ila mai tsattsauran ra’ayi ya gabatar na zuwa ne...
    Tehran ta yi maraba da hukuncin da wata kotun Faransa ta yanke na yi wa ‘yar kasar Mahdieh Esfandiari saki bisa sharadi. ‘yan sandan Faransa sun dai kama ‘yar Iran din ce bisa zarginta da goyan bayan ta’addanci mai nasaba da nuna goyan bayan al’ummar Gaza . Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran,Esmail Baghaei ya ce Tehran za ta ci gaba da bin diddigin shari’ar Esfandiari, ‘yar kasar wacce malamar jami’a ce mai shekaru 39 da ke zaune a Lyon, har sai ta samu cikakken ‘yanci tare da komawa gida,” in ji Baghaei. Esfandiari, wacce ta zauna a Faransa kusan shekaru takwas, an cafke ta ne a asirce a ranar 1 ga Maris, 2025, wanda ya sa danginta sanar da hukumomin...
    Majalisar tsarin mulki a Jamhuriyar Kamaru, ta ce sai zuwa ranar Litini 27 ga watan Oktoban nan ne za ta bayyana wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasar. Majalisar ta sanar da ranar ne bayan ta duba tare da yin watsi da duk wasu kararrakin da suka shafi zaben na ranar 12 ga watan Oktoba. Kafin nan gwamnatin Kamaru ta haramta taron jama’a a birane da dama daga jiya Laraba, gabanin sanar da sakamakon zaben, biyo bayan da madugun ‘yan adawa na kasar Issa Tchiroma Bakary ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar. Tun a makon da ya gabata ne magoya bayan Issa Tchiroma, wanda bisa ga kidayar tasa, ya ce ya samu kashi 54.8%...
    Ƙungiyar ‘yan jaridu ta Nijeriya (NUJ), reshen jihar Kano, ta mika sakon taya murna ga Ahmed Mu’azu bisa naɗin da aka yi masa na mataimaki na musanman a ɓangaren yaɗa labarai ga shugaban hukumar alhazai ta ƙasa (NAHCON),  Abdullahi Usman Saleh. A matsayinsa na ɗan asalin jihar Kano, ɗaukaka darajar Malam Ahmad Mu’azu zuwa wannan matsayi abin alfahari ne ga masu aikin jarida a jihar. ‘Yansanda Sun Cafke Wani Matashi Ɗan Shekara 15 Da Ake Zargi Da Yin Fashi Da Makami A Gombe Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe Naɗin nasa ya nuna irin ƙwarewarsa da sadaukarwarsa a ɓangaren yaɗa labarai da yake da shi. Mu’azu kafin wannan muƙamin ya...
    Gaza : Sabani tsakanin Isra’ila, Amurka da Masar kan mataki na biyu na tsagaita wuta Rahotanni daga Isra’ila ne cewa sabani ya kunno kai tsakanin gwamnatin kasar da Amurka da kuma Masar kan mataki na biyu na aiwtar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da aka cimma. Kafar yada labaran Isra’ila KAN ta bayar da rahoton cewa, an samu rashin jituwa tsakanin bnagarorin dangane da aiwatar da kashi na biyu na shirin shugaban Amurka Donald Trump na kawo karshen yakin Gaza. Kafar yada labaran ta bayyana cewa, sabanin ya samo asali ne yayin wata tattaunawa tsakanin jami’an Isra’ila da babban jami’in leken asirin Masar Hassan Rashad, wanda ya je Isra’ila. Rahotanni sun ce Rashad ya gana da Firaminista Benjamin Netanyahu,...
    Gwamnatin Jihar Ondo ta roƙi jama’a da su kwantar da hankalinsu bayan gargaɗin da Hukumar Tsaro ta DSS, ta yi na cewar wasu mayaƙan ISWAP na shirin kai hari wasu sassan jihar. A cikin wata sanarwa, Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Mista Idowu Ajanaku, ya bayyana cewa irin waɗannan rahotanni abu ne na yau da kullum a harkokin tsaro. NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Haraji Da Zai Fara Aiki A 2026 Idan Tinubu ya gaza zai yi wuya a samu shugaban da zai yi nasara — Shehu Sani Ya ce hukumomin tsaro suna yawan musayar bayanai irin waɗannan domin daƙile duk wata barazana. Ajanaku, ya tabbatar wa jama’a cewa gwamnati tare da hukumomin...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A ranar 26 ga watan Yuni, shekara ta 2025, gwamnatin tarayya ta sanya hannu kan sabon tsarin haraji wanda za a fara aiwatarwa daga ranar 1 ga Janairu, 2026.   Wannan sabon tsarin haraji na daga cikin matakan da gwamnati ke cewa zai taimaka wajen kara samun kudaden shiga da kuma rage dogaro da albarkatun mai. Sai dai, jama’a da dama ba su da cikakken bayani game da irin wadannan sabbin haraji ko menene suke nufi ba. NAJERIYA A YAU: Halin Da Muka Shiga Sakamakon Haihuwar ’Ya Mai Cutar Motsewar Kwakwalwa DAGA LARABA: Shin Ko Jam’iyyar PDP Ta Fara Gushewa Ne? Shin ko ta wadanne hanyoyi ne wannan sabon haraji  zai shafi rayuwar...
    A yau Laraba 22 ga wata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana cewa, huldar diflomasiyya ta shugabanni na matukar taka rawar gani wajen jagorantar dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka, kuma shugabannin kasashen biyu suna ci gaba da cudanya da kuma sadarwa a tsakaninsu. Shugaban Amurka Trump ya ce, yana sa ran kasashen Sin da Amurka za su cimma matsaya kan batutuwan kasuwanci a taron kolin APEC da za a yi a mako mai zuwa, amma ya ce, watakila shugabannin Sin da Amurka ba za su gana ba a lokacin. Guo Jiakun ya yi wadannan bayanai ne a lokacin da yake amsa tambayoyi game da wannan batu, inda ya yi nuni da...
    Ƙungiyar ‘yan jarida ta Nijeriya (NUJ), reshen jihar Kano, ta mika sakon taya murna ga Ahmed Mu’azu bisa nadin da aka yi masa a matsayin mataimakin mai tsara dabara kan harkokin yada labarai a hukumar alhazai ta kasa (NAHCON). A matsayinsa na dan asalin jihar Kano, daukaka darajar Malam Mu’azu zuwa wannan matsayi abin alfahari ne ga masu aikin jarida a jihar. ‘Yansanda Sun Cafke Wani Matashi Ɗan Shekara 15 Da Ake Zargi Da Yin Fashi Da Makami A Gombe Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe Nadin nasa ya nuna aikin ƙwarewa da sadaukarwa a ɓangaren yaɗa labarai da yake da shi. Mu’azu ya taɓa yin aiki a Sashen Hulda...
    Bisa kididdigar da hukumar kula da kudaden kasashen waje ta kasar Sin ta gabatar a yau ranar 22 ga wannan wata, a watan Satumba, yawan kudin da aka yi hada-hadarsu ta fuskar samun kudin shiga da kuma wadanda aka kashe na kamfanoni da daidaikun mutane da sauran hukumomin da ba na banki ba na kasar Sin ya kai dalar Amurka triliyan 1.37, wanda ya karu da kashi 7 cikin dari bisa na watan Agusta. Yawan kudin shiga da na kashewa da ya shafi kudaden kasashen waje na kasar Sin a farkon rabu’i na uku na bana ya kai dalar Amurka triliyan 11.6, wanda ya kai matsayin koli a tarihi, kana ya karu da kashi 10.5 cikin dari bisa na makamancin...
    Shugaban ƙasa mai ci, Alassane Ouattara, shi ne wanda aka fi yi wa hasashen nasara a zaɓen da za a gudanar a Ivory Coast ranar Asabar, sakamakon rashin wasu jiga-jigan ’yan adawa da za a fafata da su a zaɓen. Ouattara, mai shekara 83, yana riƙe da madafun iko tun daga shekarar 2011, lokacin da ƙasar ta fara warwarewa daga rikicin siyasa kuma ta kasance ɗaya daga cikin manyan ƙasashen da ke taka rawa wajen bunƙasar tattalin arzikin yammacin Afirka. Jerin ’yan wasan da ke takarar lashe kyautar gwarzon Afirka na bana Idan Tinubu ya gaza zai yi wuya a samu shugaban da zai yi nasara — Shehu Sani A ƙarƙashin mulkinsa, Ivory Coast — wacce ita ce babbar mai...
    A cewar sanarwar, “A ranar 15 ga Oktoba, 2025, da misalin karfe 11:00 na rana, wata mata da ke zaune a unguwar Federal Low-Cost, Gombe, ta bayyana cewa a daidai wannan ranar da misalin karfe 2:30 na dare, wani wanda ba ta san ko wanene ba, dauke da wuka ya kai mata hari, inda ya sace mata kayanta.   “Abubuwan da aka sace, sun haɗa da iphone 13 Pro Max, an kimanta kudinta akan ₦800,000, kwamfutar ‘Apple MacBook’ da darajarta ta kai ₦250,000, da agogon ‘Apple’ da darajarsa ta kai ₦35,000, ‘power bank’ na Oraimo wanda darajarsa ta kai ₦30,000, da jakar makaranta akan darajar ₦25,000.”   Abdullahi ya ce, nan take jami’an ‘yansanda na shiyyar suka dauki matakin kama...
    Tun daga lokacin da kasar Sin ta fara kera jiragen kasa masu saurin gudu a shekarar 2007 da samfurin CRH1 mai gudun kilomita 250 cikin sa’a guda, ba ta tsaya ba har zuwa yanzu da ta kera wannan sabon na zamani samfurin CR450 wanda shi ma an yi masa tsarin da za a ci gaba da inganta shi. Wannan fasaha wacce ta kara jaddada matsayin kasar Sin na ci gaba da zama jagora a fagen kere-keren jirgin kasa mafi gudu a duniya, ba kasar Sin kawai za ta amfanar ba har ma da sauran sassan duniya musamman a wannan zamani da kasar ta Sin ke kara bude kofarta ga kasashen waje da kuma neman cimma burin samar da al’umma mai...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Babaganaru Ya Zama Sabon Kocin Kano Pillars October 22, 2025 Labarai Morocco Ta Lashe Kofin Duniya Na Ƴan Ƙasa Da Shekara 20 Karo Na Farko A Tarihinta October 20, 2025 Wasanni Kano Pillars Ta Dakatar Da Manyan Masu Horas Da ‘Yan Wasanta Saboda Rashin Nasara October 20, 2025
    Ma’aikatar al’adu da yawon bude ido ta kasar Sin ta fitar da alkaluman kasuwar yawon shakatawa ta kasar tsakanin watan Janairu zuwa na Satumban bana. Kuma sakamakon binciken kididdigar da aka yi ya nuna cewa, daga watan Janairu zuwa na Satumban bana, adadin yawon shakatawa da mutanen kasar Sin suka yi a cikin gida, ya zarce biliyan 4.998, adadin da ya karu da miliyan 761 bisa na makamancin lokacin a bara, karuwar ma ta kai kaso 18 bisa dari. Daga ciki, adadin yawon shakatawa da mazauna birane da garuruwa suka yi ya kai biliyan 3.789, adadin da ya karu da kaso 15.9 bisa dari. Sai kuma adadin yawon shakatawa da mazauna yankunan karkara suka yi ya kai biliyan 1.209, adadin...
    Hukumar Kula da Harkokin Ƙwallon Ƙafa a nahiyyar Afirka (CAF) ta fitar da sunayen ‘yan takarar da za su lashe kyautar CAF ta shekarar 2025 – rukunin maza. Cikin wata sanarwa da CAF ta wallafa a shafinta na intanet, ta ce an yi la’akari da rawar da ’yan wasa da masu horarwa suka taka wajen bunƙasa kwallon ƙafa a nahiyar Afirka da ma duniya baki ɗaya. Hukumar ta ce fitattun masu takarar sun ba da muhimmiyar gudunmawa a fagen tamaula wanda za a yi la’akari da rawar da suka taka a tsakanin ranar 6 ga Janairu zuwa 15 ga Oktoba, 2025. Idan Tinubu ya gaza zai yi wuya a samu shugaban da zai yi nasara — Shehu Sani Waɗanda ke...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Komawar Iran kan teburin tattaunawa da Amurka ya dogara ne kan cimma wasu batutuwa Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta koma kan teburin tattaunawa ba matukar Amurkawa ba za su yi watsi da kwadayinsu na tsarin fadada ayyukansu ba, suna ci gaba da gabatar da bukatun Iran marasa ma’ana. Ministan harkokin wajen na Iran ya bayyana hakan ne ga manema labarai a yau Laraba a filin tashi da saukar jiragen sama na Shahid Hashemi Nejad da ke birnin Mashhad (gabashin kasar Iran), inda zai karbi bakwancin wani taron shiyya mai taken “Diflomasiya na yankin”. Araqchi ya kara da cewa: Tattaunawar da...
    Mai baiwa kasar Iraqi shawara kan harkokin tsaro ya gana da babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Qasim al-Araji, mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasar Iraki ya ci gaba da ziyararsa a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran, inda ya gana da tattaunawa da babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran. Qassem al-Araji mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasar Iraki ya gana da Manjo Janar Seyyed Abdolrahim Mousavi, babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran, inda suka tattauna kan batutuwa da dama da suka shafi moriyar kasashen biyu. A yayin ganawar, babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran ya bayyana cewa: Cikakkiyar aiwatar da yarjejeniyar tsaro tsakanin kasashen biyu na da muhimmanci. Manjo Janar Mousavi ya kara...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kai hari kan wasu muhimman wuraren da hatta kawayen haramtacciyar kasar Isra’ila ba su sani ba Tauraron dan Adam na Noor 3 ana daukarsa a matsayin dabara, soja, tauraron dan adam da Iran ta kera wanda ya samu gagarumin ci gaba na bayanai da leken asiri ga sojojin Iran. Masanin tsaro da dabarun yaki Laftanar Janar Abdul Karim Khalaf ya tabbatar da cewa: Tauraron dan adam Noor 3 na Iran yana wakiltar ingantaccen na’ura akan tauraron dan adam na Noor 2, wanda aka kara masa kilo 7 na karin kayan aiki. Tauraron dan Adam na Noor 2 yana da nauyin kilogiram 25, yayin da tauraron Noor 3 ke daukar nauyin kilogiram 32. Abin lura shi...
    Ya ce tallafin da Shugaba Tinubu ya amince da shi ba rance ba ne, wani bangare ne na yunkurin gwamnati na cire shingen da ke hana ’yan kasuwa ci gaba.   Ya ƙara da cewa gwamnati ta kafa asusun Naira Biliyan 75 da sunan tallafin ga ƙananan masana’antu da yan kasuwa (MSME Intervention Fund), wanda ke bai wa ’yan kasuwa rancen har zuwa Naira miliyan 5 da kaso tara cikin ɗari (9%) a matsayin kudin ruwa, da kuma Naira biliyan 50 a ƙarƙashin shirin Shugaba kasa Bola Tinubu da ke bai wa ƙanana ’yan kasuwa tallafin kuɗi kyauta bisa wasu sharuɗɗa domin bunƙasa kasuwanci (Presidential Conditional Grant Scheme) da ke ba da tallafin Naira 50,000 ga ’yan kasuwa miliyan ɗaya...
    Shugaban kwamitin tsaro na haramtacciyar kasar Isra’ila ya jaddada cewa: Dole ne a gudanar da bincike kan sakacin Isra’ila har Hamas ta kai harin ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023 Tzachi Hanegbi, shugaban kwamitin tsaro na haramtacciyar kasar Isra’ila, ya yi kira da a gudanar da bincike kan bala’in gazawar da aka yi a ranar 7 ga Oktoban shekara ta 2023 har kungiyar Hamas ta yi nasarar aiwatar da gagarumar nasara kan Isra’ila. Wannan ya zo ne a cikin kalaman farko da Hanegbi ya yi tun bayan da Fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya kore shi daga kan mukaminsa. Hanegbi ya ce: “Netanyahu ya sanar da shi yau cewa ya kore shi daga kan mukaminsa.” Ya...
    Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna ta yi kira ga Maniyyata Aikin Hajjin 2026 da su biya kafin alkalami nan da ranar 14 ga watan Nuwamban 2025. Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Ibrahim Datti ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da aka fitar ranar Laraba 22 ga watan Oktoban 2025. Hukumar wacce ta ce kudin kama kujerar kar su gaza Naira Miliyan Biyu, ta ce Hukumar Alhazai ta Kasa NAHCON, na kokarin sama wa Maniyyata rangwame bisa kudin kujera da ta sanar a baya. Ta kara da cewa duk wanda bai biya ba kafin karshen wa’adin da ta bayar, ba zai sami kujerar Aikin Hajjin Bana ba. Har ila yau Hukumar ta ce Maniyyata za su...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Zimbabwe Ta Jinjinawa Jarin Sin A Matsayin Wanda Ya Bunkasa Masana’atun Samar Da Siminti A Kasar October 22, 2025 Daga Birnin Sin Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya  October 21, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Kammala Ginin Cibiyar Adana Bayanai Mai Amfani Da Karfin Iska A Karkashin Ruwa October 21, 2025
    Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya tabbatar da aniyarsa ta inganta daidaito tsakanin maza da mata da kuma karfafa jagorancin mata a fannin ilimi a Jihar Jigawa. Shugabar Ofishin UNICEF na Kano, Rahama Rihood Mohammed, ya bayyana hakan a wani taron da HiLWA ta shirya tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai (EU) a Dakin Taro na Manpower Development Institute. Ya ce bincike ya nuna cewa ko da yake mata su ne mafi rinjaye a aikin koyarwa a Jigawa, suna da kaso 14 bisa 100 ne kacal a mukaman shugabanci, kamar shugabar makaranta ko mataimakiya. Wannan, a cewarsa, yana takaita gudunmawar mata wajen tsara manufofi da ci gaban ilimi. Rahama Ya bayyana cewa matsalolin al’adu, tsarin...
    Ƙungiyar Gwamnonin Arewa (NSGF), ta bayyana hatsarin fashewar tankar mai da ya auku a ƙauyen Essa a Ƙaramar Hukumar Katcha a Jihar Neja, a matsayin abin baƙin ciki da tausayi. Shugaban ƙungiyar kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ne, ya yi alhinin lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama. Waɗanda ke son rusa Kano ba za su yi nasara ba — Sanusi II Majalisar Yobe ta nemi a dauki mataki kan yawaitar hadura a hanyar Damaturu–Potiskum Ya miƙa saƙon ta’aziyyae ga gwamnatin Jihar Neja da al’ummarta da kuma iyalan da abin ya shafa. “Wannan lamari abin baƙin ciki ne ƙwarai da gaske. Addu’o’inmu suna tare da iyalan mamatan da kuma jama’ar Jihar Neja a wannan lokaci na...
      A cewar ministan, shirin sake gina bangaren samar da kayayyaki da samar da ci gaba wanda na wucin gadi ne tsakanin manufar bunkasa ayyukan masana’antu ta kasar da wa’adinta ya kare da kuma sabuwar manufa ta shimfida tubali mai kwari ga ajandar bunkasa masana’antu ta kasar.   Ya kara da cewa, bangaren samar da kayayyaki wanda ya mamaye kaso 15.3 na alkaluman GDP na Zimbabwe a 2024, shi ne kan gaba wajen ingiza ci gaban tattalin arzikin kasar. (Mai fassara: Fa’iza) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya  October 21, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Kammala Ginin Cibiyar Adana Bayanai Mai Amfani Da...
    Ahmed maiyaki, ya dade yana bayar da gudummawa a harkar yada labarai a a fadin kasar nan bayan kasancewarsa tsohon ma’aikaci a sashin hausa na rediyon Faransa ( FRI).   Jihar Kaduna ta kwashe shekaru takwas babu ma’aikatar yada labarai wacce tsohon gwamna Nasir El-Rufai ya rufeta , sai bayan lashe zaben gwamna Uba Sani ya dawo da ma’aikatar wacce aka dorawa alhakin kula da yada manufofin gwamnatin jihar . ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ba A Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla A Arewacin Nijeriya – Sarkin Musulmi October 22, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aiki, Ta Bai Wa Gwamnati Wa’adin Wata Guda Don Biyan Buƙatunta October 22, 2025 Manyan Labarai Majalisa Ta Amince...
    Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Zamfara ta  gargaɗi direbobi da sauran jama’a game da rufe lambobin motoci, musamman a cikin garin Gusau, babban birnin jihar. Gargaɗin ya biyo bayan ƙaruwa da ake samu na rahotanni da kuma lura da direbobi da ke tafiya da lambobin motoci a rufe, wanda rundunar ta bayyana a matsayin karya dokokin hanya da ke kawo barazana ga tsaro da zaman lafiya. A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya fitar, rundunar ta bayyana cewa wannan dabi’a tana nuna ƙoƙarin kaucewa binciken jami’an tsaro tare da yiwuwar taimaka wa aikata laifuka. Sanarwar ta ƙara da cewa, Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, CP Ibrahim Balarabe Maikaba, ya jaddada cewa rundunar...
    Majalisar zartarwa ta jihar Jigawa ta amince da kashe Naira biliyan 2.55 domin gudanar da binciken na musamman, wanda zai mayar da hankali kan albarkatun mai, gas, da sinadarin uranium, tare da cikakken binciken kimiyyar kasa kan ma’adinai a fadin jihar. A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya fitar, ya bayyana cewa wannan muhimmin shiri na gwamnatin yanzu babban mataki ne na gaba wajen cika alkawarin gwamnati na ganowa da kuma amfani da albarkatun kasa masu tarin yawa da ke cikin jihar Jigawa. A cewarsa, wannan bincike zai samar da bayanai masu muhimmanci game da ma’adinai, da mmn fetur da iskar gas da ke karkashin kasa, wanda zai taimaka wajen yanke shawara mai...
    Majalisar dokokin jihar Yobe, ta yi kira ga bangaren zartarwa na gwamnatin jihar da ta dauki matakan gaggawa domin magance yawaitar haduran ababen hawa a garuruwan Ngelzarma, Damagum da Dogon Kuka da ke kan hanyar Damaturu zuwa Potiskum. Majalisar ta yi wannan kiran ne bayan gabatar da kudiri da dan majalisa mai wakiltar mazabar Damagum, Maina Digma Gana, ya yi kan yawaitar hadura a wadannan garuruwa. Waɗanda ke son rusa Kano ba za su yi nasara ba — Sanusi II MTN zai rufe ofisoshi 101 a Kano, Borno da Adamawa saboda gyare-gyare Gana, ya bayyana cewa yawaitar haduran ababen hawa a yankin abun damuwa ne, don haka ya zama wajibi gwamnati ta dauki mataki don kare rayukan jama’a. Ya kara...
    “Da ba sojoji, da ba za mu iya gudanar da wannan taro cikin kwanciyar hankali ba. Don haka dole mu ci gaba da ƙarfafa musu gwiwa,” in ji shi. Sarkin Musulmi ya kuma nuna damuwa kan yadda ake amfani da kafafen sada zumunta na yanar gizo ba tare da tunani ba, inda ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakan da suka dace don tsara amfani da su, inda ya bayyana cewa shi kansa ya taɓa fuskantar matsala bayan yaɗa labaran ƙarya a kansa. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Da ɗumi-ɗuminsa ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aiki, Ta Bai Wa Gwamnati Wa’adin Wata Guda Don Biyan Buƙatunta October 22, 2025 Manyan Labarai Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin...
    Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya ce babu wanda zai yi nasara wajen rusa tarihin Kano da aka kafa tsawon shekaru. Ya bayyana hakan ne a Abuja, a ranar Talata, yayin gabatar da littattafai biyu da Dokta Munzali Dantata, ya rubuta; Behind the City Wall da Aminu Dantata: Life and Times of a Nigerian Entrepreneur. An gano sauro a karon farko na tarihin ƙasar Iceland Gwamnatin Borno rufe makarantun jihar saboda rigakafin ƙyanda da Polio A cewar Sarkin, tarihin Kano ya samo asali ne daga tsohuwar al’ada ta jajircewa, ilimi, kasuwanci, da ƙwarewa. “Mun zo nan ne don murna, amma abin da ya fi muhimmanci shi ne muna taya Kano murna, birni wanda ya samar da iyalan Dantata...
    Wannan tsarin na taimaka wa yara su samu ilimi mai zurfi da zai ba su damar daidaita da tsarin rayuwarsu na yau da kullum. Makarantun suna da ɗakunan kwana, gidajen malamai, wutar lantarki mai amfani da hasken rana, rijiyoyin burtsatse, kujeru, kayan karatu, da cibiyar koyon sana’o’i kamar ɗinki, sassaƙa, kwamfuta, da sauransu. Haka kuma, gwamnan ya gyara Ma’aikatar Harkokin Mata da Ci gaban Jama’a ta Jihar Zamfara da kuma Kwalejin Fasaha da Kimiyya ta Zamfara (ZACAS). A ɓangaren lafiya kuwa, gwamnatinsa ta gyara asibitoci da cibiyoyin lafiya da dama a faɗin jihar. Don rage mace-macen mata da jarirai a yayin haihuwa, ya ɗauki ƙarin ma’aikatan lafiya, tare da samar da magunguna da kayan aiki, tare d harkar kyautata kiwon...
    Gwamnatin Jihar Kwara ta ware kimanin Naira Biliyan 8 da miliyan dari daya domin biyan haƙƙin fansho da giratuti na ma’aikatan jiha da na kananan hukumomi da suka yi ritaya. Kwamishinan Kuɗi na Jihar, Dakta Hauwa Nuhu, ce ta bayyana haka a yayin taro da ma’aikatun gwamnati karo na uku, wanda aka gudanar a zauren taro na ma’aikatar kuɗi a Ilori. A cewarta, za a raba Naira Biliyan biyar da miliyan dari shida ga tsoffin ma’aikatan jiha a matsayin giratuti, yayin da aka ware Naira Biliyan biyu da miliyan dari biyar domin tsoffin ma’aikatan kananan hukumomi. Dakta Nuhu ta jaddada cewa gwamnatin jiha za ta ci gaba da biyan fansho da giratuti a hankali domin tabbatar da cewa sauran ayyukan...
    A karon farko a tarihi, an gano sauro a ƙasar Iceland, tare da gano samfura guda uku a wannan watan a Kjos, wani yanki mai ƙwari a kusa da Hvalfjordur. Wani mai sha’awar ƙwari, Bjorn Hjaltason ne ya fara ba da rahoton ganowar a cikin wani zaure na Facebook mai suna Skordyr a Islandi (wato ƙwari a Iceland), kamar yadda Hukumar Watsa Labarai ta Iceland ta faɗa a ranar Litinin. Gwamnatin Borno rufe makarantun jihar saboda rigakafin ƙyanda da Polio Masu kwacen waya sun kashe ma’aikaciyar lafiya a Zariya An miƙa samfuran ga Cibiyar Tarihin Halittu ta Iceland domin bincike, inda masanin ilimin halitta Matthias Alfredsson ya tabbatar da cewa lalle sauro ne. An bayyana samfurin a matsayin Culiseta annulata,...
    A gefe guda kuma ta roƙi jama’a su yi watsi da rahoton jaridar, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da gudanar da aikinta cikin gaskiya da amana. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Da ɗumi-ɗuminsa ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aiki, Ta Bai Wa Gwamnati Wa’adin Wata Guda Don Biyan Buƙatunta October 22, 2025 Labarai Rashin Abinci Mai Gina Jiki Barazana Ce Ga Lafiyar Al’umma – Gwamna Lawal October 22, 2025 Manyan Labarai Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe October 22, 2025
    Babaganaru, ya taɓa jagorantar ƙungiyar inda ya lashe kofunan gasar NPFL guda biyu a shekarun 2011/12 da 2012/13 a lokacin da ya yi aiki a baya. Ana sa ran zai kawo gogewa da a wannan sabon babi na horar da ƙungiyar. A halin yanzu Pillars tana matsayi na 18 a kan teburin gasar bayan wasanni takwas, inda ta samu nasara biyu kacal, ta yi canjaras biyu da kuma rashin nasara huɗu. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Morocco Ta Lashe Kofin Duniya Na Ƴan Ƙasa Da Shekara 20 Karo Na Farko A Tarihinta October 20, 2025 Wasanni Kano Pillars Ta Dakatar Da Manyan Masu Horas Da ‘Yan Wasanta Saboda Rashin Nasara October 20, 2025 Wasanni Kano Derby: Barau FC...
    Dr Majid Ghayour Mubarhan kwararre kuma farfesa a jami’ar kiwon lafiya ta birnin mashahada ya samu kyautar hukumar WHO na gabashin meditareniya saboda namijin kokarin da yayi na kirkiro abin da zai kula da kuma kare kamuwa da cututtuka da basa yaduwa, kamar cutar kansa ciwon zuciya da kuma ciwon Sugar. Wannan kyautar tana nuna irin ci gaban da Iran ta samu ne a bangaren kimiyyaa yankin duk da takunkumi da kuma takurawar da take fuskanta daga bangaren kasashen turai dake takaita halartar masana kimiyyar kasar  hallara a matakin kasa da kasa. A duk shekata hukumar lafiya ta duniya tana bada kyauta ga duk wani masanin kimiya da yayi kwazo wajen kirkiro wata fasaha a bangaren lafiyar gama gari,  da...
    Majalisar Dattawa ta amince da sabuwar doka da ta tanadi daurin rai da rai ga duk wanda aka samu da laifin lalata da yaro ko yarinya karama. Dokar na son kare hakkokin kananan yara ne, kuma ta shafi maza da mata baki daya, ba tare da wani zabi na biyan tara ba. Sanata Adams Oshiomhole (Edo ta Arewa), ya ce yara ba su da iko ko yardar wajen amincewa da yin jima’i kuma irin wannan abu na jefa su cikin tashin hankali har abada. Da farko ya ba da shawarar a daure mai laifi na tsawon shekaru 20, amma yawancin sanatoci sun nemi hukunci mafi tsauri. Sanata Muhammad Adamu Aliero (Kebbi ta Tsakiya) ya bayar da shawarar daurin rai da...
    Rahotanni su bayyana cewa gwamnatin birtaniya ta sanar a hukumance cire kungiyar tahrirush shams HTS daga cikin jerin kungiyoyin yan ta’adda a wani yunkuri na ganin ta kara kusantar  sabuwar gwamnatin siriya bayan faduwar gwamantin Bashar Al-Asad. Gwamnatin birtaniya ta bayyana cewa wannan mataki zai sanya su kara kusanci da gwamnatin siriya da Abu mohammad Al-Jolani ke jagoranta wanda aka fi sani da Ahmed sharaa wanda shi ne shugaban kungiyar Al-Qaida kuma kwamandan Daesh. Wannan sanarwar ta zo ne bayan ziyarar da sakataren harkokin wajen birtaniya David lammy ya kai kasar siriya  a watan yuli, wanda ya sanya ya zama shi ne babban jami’in diplomasiya da ya kai ziyara kasar a tsawon shekaru. Kuma mataki yazo ne duk da hujjoji...
    Kasar Sin ta kammala ginin wata cibiyar adana bayanai, irinta ta farko dake karkashin teku kuma mai amfani da lantarki daga karfin iska wato (UDC), wanda aka samar a birnin Shanghai na gabashin kasar. Cibiyar ta zama wani maunin inganci ta fuskar samar da kayayyakin sarrafa bayanai. Cibiyar UDC wadda ke da mazauni a yankin Lingang na Shanghai, wanda yanki ne na kulla cinikayya cikin ‘yanci, ta samu jarin yuan biliyan 1.6, kwatankwacin kimanin dala miliyan 226, kuma tana da karfin lantarki da ya kai megawatt 24. A cewar kwamitin gudanar da harkokin yankin Lingang, kammala aikin wata babbar nasara ce ga aikin samar da cibiyar UDC da kuma makamashi mai tsafta dake cikin teku. Ya kuma nuna yadda aka...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Siyasa Babu Rikici A Jam’iyyar APC A Nasarawa — Shugaban Jam’iyya October 21, 2025 Siyasa Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu October 20, 2025 Siyasa Tsohon Ɗan Majalisar Bayelsa Ya Shawarci Jonathan Ya Guji Neman Takara A 2027 October 17, 2025
    Babban jam’in hukumar tsaro ta kasar iran ya bayyana jin dadin kasar iran ga kasar Rasha saboda goyon bayan da ta bata a kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya kan hakkin iran a gaban kasashen turai dake kokarin kakkaba mata sabon takunkumin karya tattalin Arziki, Babban sakataren tsaro na kasar Iran Dr Ali Larijani ya fadi hakan ne a jiya talata A wata ganawa da yayi da jakadan shugaban kasar Rasha Alexander Lavrentiev da ya kawo ziyara nan kasar iran , larijani a matsayinsa na mai bawa jagora shawara ya jinjinawa kasar rasha game da goyon bayan da take bawa kwamitin. LarIjani da sauran jami’an gwamnatin kasar Rasha sun yi bitar matakin hadin guiwa dake tsakanin Tehran da mosko a...
    Ma’aikatar Ilimi, Kimiyya, Fasaha da Kirkire-Kirkire ta Jihar Borno ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun Firamare da Sakandare na gwamnati da masu zaman kansu na tsawon kwanaki biyu domin gudanar da aikin rigakafin cututtukan ƙyanda da shan inna. Sanarwar umarnin rufe makarantun ta fito ne daga ofishin Kwamishinan Ma’aikatar, a ranar Talata, a birnin Maiduguri. Labarin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya ƙarya ne – Sarkin Musulmi Fashewar tankar mai ta yi ajalin mutum 30 a Neja A cewar sanarwar, za a rufe makarantun daga ranar Alhamis, 23 ga Oktoba, zuwa Juma’a, 24 ga watan Oktoba, 2025. An kuma umarci dukkan makarantun da su ci gaba da ayyukansu daga Litinin, 27 ga Oktoba, 2025, kamar yadda aka saba....
    Piwuna, ya ce gwamnati ta gaza cika alƙawurran da ta ɗauka duk da sanarwar kwanaki 14 da ASUU ta bayar tun a ranar 28 ga Satumba, 2025. Ya ce babu wani abin da aka cimma wanda zai hana ƙungiyar aiwatar da shawarar majalisar zartarwarta na fara yajin aikin. “Dukkanin rassan ASUU a faɗin ƙasar nan an umarce su da su janye ayyukansu daga misalin ƙarfe 12 na dare ranar Litinin,” in ji Piwuna Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa idan gwamnati ta kasa magance matsalolin cikin wannan lokaci, za ta ɗauki mataki mafi tsanani bayan kammala yajin aikin gargaɗin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe...
    Piwuna, ya ce gwamnati ta gaza cika alƙawurran da ta ɗauka duk da sanarwar kwanaki 14 da ASUU ta bayar tun a ranar 28 ga Satumba, 2025. Ya ce babu wani abin da aka cimma wanda zai hana ƙungiyar aiwatar da shawarar majalisar zartarwarta na fara yajin aikin. “Dukkanin rassan ASUU a faɗin ƙasar nan an umarce su da su janye ayyukansu daga misalin ƙarfe 12 na dare ranar Litinin,” in ji Piwuna Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa idan gwamnati ta kasa magance matsalolin cikin wannan lokaci, za ta ɗauki mataki mafi tsanani bayan kammala yajin aikin gargaɗi. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe...
    Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), ta dakatar da yajin aikin gargaɗi na makonni biyu da ta fara. Ƙungiyar ta kuma bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin wata ɗaya don biyan buƙatunta. Rashin Abinci Mai Gina Jiki Barazana Ce Ga Lafiyar Al’umma – Gwamna Lawal Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe ASUU ta yi gargaɗin cewa idan gwamnati ta gaza ɗaukar mataki cikin wa’adin da ta bayar, za ta iya komawa yajin aiki. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe October 22, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa Gobara Ta Tashi A Kasuwar Alaba Da Ke Legas October...
    Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya karyata zargin kisan kiyashi ga Kiristoci a Najeriya, yana mai cewa wannan ikirari ƙarya ne kuma bai kamata a ci gaba da yada shi ba. Sarkin ya bayyana hakan ne a taron Babban Majalisar Sarakunan Gargajiya na Arewa na shekarar 2025, wanda aka gudanar a Birnin Kebbi, Jihar Kebbi, a ranar Talata, da taken: “Ƙarfafa Haɗin Gwiwar Al’umma Domin Samun Zaman Lafiya da Tsaro Mai Dorewa a Arewa.” Masu kwacen waya sun kashe ma’aikaciyar lafiya a Zariya Majalisa ta soma binciken yadda aka kashe $4.6bn na tallafin kiwon lafiya Ya ce: “Sun dade suna cewa ana kisan kiyashi ga Kiristoci a Najeriya daga ƙasashen Yamma kamar Amurka, Kanada da sauransu. A ina? Yaushe?...
    Labaran da suke fitowa daga birnin Khartum babban birnin kasar Sudan sun bayyana cewa jirgin yaki na kunan bakin wake ya fada kan wani yanki kusa da tashar jiragen sama na birnin kwana guda kafin gwamnatin kasar ta sake bude ta fiye da shekaru biyu da sufe ta. Shafin yanar gizo na labarai ‘ArabNews’ na kasar Saudiya ya bayyana cewa an rufe tashar jiragen sama na Khurtum ne, jim kadan bayan fara yaki da a cikin watan Afrilun shekara ta 2023.  Yaki tsakanin sojojin Sudan da kuma dakarun  ‘ Rapid Support Forces (RSF), dakarun daukin gaggawa wanda ya lalata muhimman kayakin aiki a tashar, hakan ya sa aka rufe ta.   Wakilin kanfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya...
    Shugaban kungiyar Hizbullah Ta Kasar Lebanon Sheikh Na’em Qasim ya bayyana cewa, ya bayyana cewa Firai ministan HKI Benyamin Natanyahu ya zubar da jinin mutanen yankin yammacin Asia da dama, amma wannan bai bashi lamunin cewa haramtacciyar kasar Isra’ila (HKI) zata zauna lafiya a yankin nan gaba ba. Tashar tal;abijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban kungiyar yana fadar haka a jiya Talata a wani bikin kaddamar da littafi wanda yake bayyana ra’yin Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminaie dangane da wakoki da kidekide. Yace: Duk tare da zubar da jinin mutanen yankin a duk a lokacinda ya ga dama, Netanyahu ba zai ce yana da lamuni na zaman lafiya ga HKI a nan...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya tattauna da babban sakataren MDD Antonio Guterres  ta wayar taron dangane da  sabban al-amura a yankin yammacin Asiya, musamman dangane da Gaza da kuma rikicin kasar Yemen. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya Abbas Aragchi yana fadawa Guterres kan cewa ya zama lazimi kasashen duniya su tabbatar da cewa HKI ta dai keta hurumin yarjenia da ta cimma da Hamas. Ministan ya kara da cewa tare da halin da ake ci a Gaza, yarjeniyar tsagaita wutar ba zata tafi kamar yadda aka tsar aba. Musamman wajen ganin kayakin agaji su shiga Gaza kamar yadda ya dace. Ya ce a halin yanzu HKI tana kawo cikas a shigarda kayakin abinci  da...
      Cikakken bayani na tafe… ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamnoni Sun Yi Ta’aziyyar Mutanen Da Suka Rasu A Fashewar Tankar Mai A Neja October 22, 2025 Manyan Labarai Ma’aikatan Manyan Makarantu Na Kaduna Sun Dakatar Da Yajin Aiki Yayin Da Gwamna Sani Ya Amince Da Sabon Tsarin Albashi October 21, 2025 Manyan Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Fashewar Tankar Man Fetur Ta Yi Ajalin Rayuka 30 A Neja October 21, 2025
    Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) ta bayyana baƙin cikinta game da gobarar tankar mai da ta tashi a ƙaramar hukumar Katcha ta Jihar Neja, inda mutane 38 suka rasa rayukansu. A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na Jihar Kwara, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta jajanta wa jama’a da gwamnatin Jihar Neja, musamman iyalan waɗanda abin ya shafa da kuma Gwamna Mohammed Umar Bago. Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya  Babu Rikici A Jam’iyyar APC A Nasarawa — Shugaban Jam’iyya “Tunaninmu yana tare da iyalan da wannan mummunan lamari ya shafa. Muna godiya ga ma’aikatan agajin gaggawa bisa taimakon da suka bai wa waɗanda abin ya rutsa da su,”...
    Ministan harkokin wajen Habasha Gideon Timotheos ya ce ya tattauna da ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov kan batutuwa daban-daban da suka Shafi dangantaka tsakanin kasashen biyu da kuma yadda za a kara inganta su. Timotheos ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai bayan tattaunawar da ministocin biyu suka yi a ranar jiya  Talata, inda ya ce, “A yau mun tattauna kan yadda za a gaggauta aiwatar da yarjejeniyoyin a fannin nukiliya, da kuma a fannonin zuba jari, binciken kimiyya, da musayar al’adu.” Ya kara da cewa, “Ciniki tsakanin kasashen biyu yana karuwa, amma idan aka kwatanta da damar da kasashen biyu suke da ita,  akwai abubuwa da dama da ya kamata a kara ingantawa da kuma habaka...
    A cikin jawabin da ya gabatar a wannan Talata da aka nuna kai tsaye a taron jana’izar  babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Yemen  Laftanar Janar Mohammed al-Ghamari, Sayyed Abdulmalik al-Houthi ya jaddada cewa, kasar Yemen za ta ci gaba da kasancewa cikin shirin komowa ga ayyukan soji idan Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta koma kisan kare dangi, da kuma ci gaba da killace yankin zirin Gaza. Sayyed al-Houthi ya yi ishara da irin babban gangami na dubban daruruwan mutane da suka taru a wurin jana’izar shahid al-Ghamari a matsayin abin da ke nuni da tsayin daka na al’ummar Yemen a kan manufofinsu. Sayyed al-Houthi ya kuma yi nuni da cewa al’ummar Yemen sun gamsu da matsayi mai Daraja da suke a...
    Wasu da ake zargin masu kwacen waya ne sun kashe ma’aikaciyar jinya a Asibitin Gambo Sawaba da ke Zariya a jihar Kaduna mai suna Hadiza Musa. Bayanai sun ce marigayiyar it ace mataimakiyar shugabar sashen haihuwa a asibitin. Majalisa ta soma binciken yadda aka kashe $4.6bn na tallafin kiwon lafiya Gwamna Bala Mohammed ya ƙirƙiri sabbin masarautu 13 a Bauchi Mijinta, Hamza Ibrahim Idris, wanda ke aiki a Abuja, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an kashe matarsa ne a ranar Asabar yayin da take dawowa daga aiki. “A ranar Asabar, ta kira ni ta ce za ta je wajen gyaran gashi sannan ta ziyarci wani shagon masu magani a Filin Mallawa, Tudun Wada Zariya, kuma na amince.”...
      A ranar 30 ga watan Mayun bana, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya halarci bikin sanya hannu kan yarjejeniyar da ta tabbatar da kafuwar kungiyar IOMed, kuma a madadin kasar Sin, ya sanya hannu kan yarjejeniyar aikinta a yankin musamman na Hong Kong.   Tun daga watan Agustan bana, kasashe 37 sun sanya hannu kan yarjejeniyar kafuwar kungiyar, kana takwas daga cikinsu sun amince da fara aiwatar da ita. A matsayin wadda ta gabatar da shawarar kafa IOMed, kuma mai masaukinta, kasar Sin na kira ga karin kasashe da su gaggauta shiga kungiyar, su kuma shiga a dama da su cikin hadin gwiwar kut-da-kut na ayyukanta, kana su samar da sabuwar gudunmawa ga wanzuwar zaman lafiya da...
    Kasar Sin ta kammala ginin wata cibiyar adana bayanai, irinta ta farko dake karkashin teku kuma mai amfani da lantarki daga karfin iska wato (UDC), wanda aka samar a birnin Shanghai na gabashin kasar. Cibiyar ta zama wani mizanin inganci ta fuskar samar da kayayyakin sarrafa bayanai. Cibiyar UDC wadda ke da mazauni a yankin Lingang na Shanghai, wanda yanki ne na gwajin cinikayya cikin ‘yanci, ta samu jarin yuan biliyan 1.6, kwatankwacin kimanin dala miliyan 226, kuma tana da karfin lantarki da ya kai megawatt 24. A cewar kwamitin gudanar da harkokin yankin Lingang, kammala aikin wata babbar nasara ce ga hadadden aikin samar da cibiyar UDC da kuma makamashi mai tsafta dake cikin teku. Ya kuma nuna yadda...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Me Aka Gano Kan Makomar Tattalin Arzikin Kasar Sin Daga Karuwar 5.2% Na Tattalin Arzikinta? October 21, 2025 Daga Birnin Sin Jirgin Kasa Mafi Saurin Gudu A Duniya Ya Fara Zirga-Zirgar Gwaji A Sin October 21, 2025 Daga Birnin Sin Jami’an Kasashen Afrika Na Koyon Dabarar Yaki Da Talauci Ta Sin A Jihar Ningxia October 21, 2025
    Majalisar Wakilai ta amince a soma binciken yadda aka yi amfani da tallafin ƙetare da ya kai dala biliyan 4.6 da Nijeriya ta karɓa daga shekarar 2021 zuwa 2025, domin yaƙi da cututtukan HIV/AIDS, tarin fuka (TB), da zazzabin cizon sauro (maleriya). Wannan na zuwa ne bayan ƙudirin da Honarabul Philip Agbese daga Jihar Benuwe ya gabatar a yayin zaman majalisar na ranar Talata. Gwamna Bala Mohammed ya ƙirƙiri sabbin masarautu 13 a Bauchi Uba Sani ya yi wa ma’aikatan manyan makarantu ƙarin kashi 70 a albashi Agbese ya bayyana cewa Nijeriya ta karɓi kusan dala biliyan 1.8 daga Global Fund da kuma dala biliyan 2.8 daga Hukumar Raya Kasashe ta Amurka (USAID) a tsakanin 2021–2025, sai kuma sama da dala...
      Gwamna Yusuf ya lura cewa, wasu kafafen yada labarai na yanar gizo suna amfani da manhajojin su wajen yada “labarai masu raba kan addini da siyasa,” wanda a cewarsa, za su iya gurgunta hadin kan al’umma da kwanciyar hankali idan ba a magance su ba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Majalisa Ta Tabbatar Da Yusuf A Matsayin Sabon Shugaban NPC, Wasu 2 A Matsayin Kwamishinoni October 21, 2025 Manyan Labarai Ma’aikatan Manyan Makarantu Na Kaduna Sun Dakatar Da Yajin Aiki Yayin Da Gwamna Sani Ya Amince Da Sabon Tsarin Albashi October 21, 2025 Manyan Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Fashewar Tankar Man Fetur Ta Yi Ajalin Rayuka 30 A Neja October 21, 2025
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da Naira biliyan ɗaya domin gyaran ajujuwan karatu a wasu makarantu na gwamnati. Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Dutse. A cewarsa, majalisar zartarwar jihar ta amince da kashe fiye da Naira miliyan 528 domin gyaran ginin ajujuwa a wasu zababbun makarantu na gwamnati a fadin jihar. Ya bayyana cewa, manufar aikin ita ce inganta yanayin karatu, tabbatar da tsaro, da kuma samar da iingantaccen ilimi karkashin shirin gwamnatin jihar na farfado da ilimin asali. Sagir Musa ya kuma ce, majalisar ta amince da kashe sama da Naira miliyan 512 domin  samar...
      Har ma abun da ba kasafai ake gani ba, tattalin arzikin Sin yana cike da karfin tinkarar duk wani hadari da ka iya kunno kai. Ba sabunta kayayyaki kirar kasar da kara musu inganci kadai aka samu ba, har ma abokan cinikin kasar a ketare suna ta kara yawa.   A jiya Litinin ne aka bude cikakken zama na 4 na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20 a nan Beijing, inda za a tattauna da kuma ba da shawarwari kan shirin shekaru biyar-biyar na 15 na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin. Kasashen duniya na sa ran cewa, kasar Sin za ta ba da sababbin damammarkin neman samun ci gaba ga duniya, bisa ga...
    Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya rattaba hannu kan dokar ƙirƙirar sabbin masarautu 13 wadda za ta ba da damar naɗin hakimai sama 111 a faɗin jihar. Sabbin masarautun da gwamnan ya ƙirƙira sun haɗa da: Burra, Duguri, Dambam, Bununu, Lere, Darazo, Jama’a, Lame, Toro, Ari, Warji, Giade da kuma masarautar Gamawa. Uba Sani ya yi wa ma’aikatan manyan makarantu ƙarin kashi 70 a albashi Fashewar tankar mai ta yi ajalin mutum 30 a Neja Da yake jawabi a gidan gwamnati, Bala Mohammed ya gargadi masu son siyasantar da lamarin ko kawo cikas wajen aiwatar da dokokin, yana mai cewa hukumomin tsaro za su dauki matakin da ya dace. “Ba za mu lamunci duk wanda zai yi ƙoƙarin tayar da...
      “Wadanda aka nada sun bayyana a gaban kwamitin don tantancewa a ranar Talata, 14 ga Oktoba, 2025,” in ji shi. “Kwamitin bai samu koke ko korafe-korafe ba a kansu, sun nuna shiri da cancanta akan ayyukan da aka zabo su”.   Ya bayyana sunayen wadanda aka tantance a matsayin: “Aminu Yusuf (Jihar Neja) – Shugaba, Joseph Haruna Kigbu (Jihar Nasarawa) – Kwamishina, Tonga Betara Bularafa (jihar Yobe) – Kwamishina. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ma’aikatan Manyan Makarantu Na Kaduna Sun Dakatar Da Yajin Aiki Yayin Da Gwamna Sani Ya Amince Da Sabon Tsarin Albashi October 21, 2025 Manyan Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Fashewar Tankar Man Fetur Ta Yi Ajalin Rayuka 30 A Neja October 21, 2025 Manyan...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Jami’an Kasashen Afrika Na Koyon Dabarar Yaki Da Talauci Ta Sin A Jihar Ningxia October 21, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Bayar Da Tallafin Dala Miliyan 3.5 Ga Shirin Samar Da Abinci A Zambia October 21, 2025 Daga Birnin Sin Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka October 20, 2025
    Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani, ya amince da aiwatar da ƙarin kashi 70 a albashin ma’aikatan dukkanin makarantun gaba da sakandare na gwamnati da ke jihar. Sabon tsarin albashin na CONPCASS/CONTEDISS 2024 wanda zai fara aiki daga Oktoban 2025, na daga cikin kokarin gwamnatinsa na inganta walwalar ma’aikata da farfaɗo da harkar ilimi a jihar. Fashewar tankar mai ta yi ajalin mutum 30 a Neja Yadda Kwankwaso ya yi murnar zagayowar ranar haihuwarsa Amincewar na zuwa ne bayan wani muhimmin zama da aka gudanar tsakanin gwamnan da shugabannin ƙungiyoyin ma’aikatan manyan makarantu (JUTIKS), wanda hakan ya kai ga janye yajin aikin da aka shafe wata guda ana yi. Taron wanda Ƙungiyar Ƙwadago ta NLC ta shirya kuma aka gudanar a...
    Tattaunawar wacce aka gudanar a gidan gwamnati dake Kaduna, kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC, da majalisar jihar Kaduna karkashin jagorancin Kwamared Ayuba Suleiman ne ta dauki nauyin gudanar da taron, kuma wakilan kungiyoyin ma’aikatan manyan makarantun ilimi na kwalejin kimiyya da fasaha ta Nuhu Bamalli, Zariya; Kwalejin Ilimi, Gidan Waya; da kwalejin koyon aikin jinya da ungozoma ta jihar Kaduna dake da cibiyoyin karatu a Kaduna, Kafanchan, da Pambegua, duk sun samu halartar taron.   Kungiyoyin sun ayyana daukar wani mataki na yajin aiki ne a ranar 30 ga Satumba, 2025, kan batutuwan da suka shafi aiwatar da tsarin albashi na CONPCASS/CONTEDISS na 2009, fa’idodin ritaya, da jin dadin ma’aikata gaba daya a manyan makarantu mallakar Jihar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA...
    ‘Yan sanda a birnin Abuja sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa Zanga-zangar masu neman a saki jagoran ‘yan awaren Biafar Nnamdi Kanu wanda ake yi wa shari’a bisa tuhumarsa da ayyukan ta’addanci. Shi dai Kanu yana jagorantar kungiyar ‘yan asalin Biarafa ( Ipob) a takaice wacce a hukumance an haramta, saboda kiran da take yin a balle yankin kudu masu gabashin kasar da ‘yan kabilar Igbo suke da rinjaye domin kafa musu kasa mai cin gashin kanta. Jami’an tsaro sun rika yin sintiri a tsakiyar birnin Abuja, da motoci masu silke da kuma masu watsa ruwan zafi. Haka nan kuma sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye akan masu goyon bayan kungiyar da su ka...
    Ofishin da yake tafiyar da hukuma a Gaza, ya sanar da cewa daga tsaaita wutar yaki zuwa yanzu adadin motocin dake dauke da abinci da aka bari su ka shiga yankin ba su wuce 986 ba alhali yawansu ya kai 6600. A bisa yarjejeniyar da aka kulla ta tsagaita wutar yaki, adadin motocin da ya kamata a bari su shiga yankin na Gaza, zuwa jiya Litinin 10/21/2025, shi ne 6,600. Daga cikin kayan agajin da ake son shigar da su cikin Gaza da akwai tukwanen Gas na dafa abinci a cikin manyan motocin dakon kaya 14, da kuma wasu motocin 28 masu dauke da makamashin da gidajen Burodi, asibitoi  za su yi aiki da su. Yankin na Gaza dai yana...
    Da  misalin karfe 9;30 na safiyar ranar Lahadi ne dai wasu mutane masu dauke da makamai su ka kutsa cikin gidan adana kayan tarihi na ” Louvre”  inda su ka yi awon gaba da kayayyaki masu daraja. Ministun harkokin cikin gidan Faransa  da na al’adu sun ce; barayin sun dauki mintuna 4 zuwa 7  kadai su ka yi satar. Da dama daga cikin kafafen watsa labarun kasar ta Faransa sun bayyana abinda ya faru da cewa ya yi kama da abinda ake gani a cikin fina-finai. Satar dai ta jawo cece-kuce a tsakanin ‘yan siyasar kasar, yayin da kafafen watsa labaru suke yi wa lamarin isgili ta hanyar yin zane-zane. Jaridar “La Progress” ta amabci cewa a baya ma an...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Ta Bayar Da Tallafin Dala Miliyan 3.5 Ga Shirin Samar Da Abinci A Zambia October 21, 2025 Daga Birnin Sin Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka October 20, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar October 20, 2025
    Ana fargabar cewa aƙalla mutum 30 sun riga mu gidan gaskiya sakamakon fashewar wata tankar man fetur a ƙauyen Essa da ke hanyar Agaei zuwa Bida a ƙaramar hukumar Katcha ta Jihar Neja. Aminiya ta ruwaito cewa, akwai kuma kimanin mutum 40 da suka jikkata wadanda suka wawason kwalfar man fetur bayan kifewar tankar. Bayanai sun ce da misalin karfe 11 na safiyar wannan Talatar ce tankar ta kife a titin Essan da aka bayyana cewa lalacewar hanyar ce ta haddasa hatsarin.  
    Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya sanar da shirinsa na ɗaga darajar Kwalejin Jinya ta Nafisatu da ke Kwankwaso zuwa cikakkiyar Jami’ar Kiwon Lafiya albarkacin bikin zagayowar ranar haihuwarsa. Taron na wannan Talatar, 21 ga watan Oktoban 2025, ya gudana ne a garinsa na Kwankwaso da ke Karamar Hukumar Madobi, inda aka yaba da ci gaban da makarantar ta samu tun daga kafuwarta a 2019 zuwa yanzu. Tinubu ya naɗa sabon Minista Alƙaluman wucin-gadi na nuna Paul Biya ya lashe zaɓen Kamaru Kwankwaso ya ce an ɗauki wannan mataki ne domin ƙara buɗe damammaki ga mata matasa su sami ilimin kiwon lafiya mai zurfi. Ya jaddada cewa makarantar ita ce ta farko a Najeriya da ke karɓar dalibai...
    Sun ce wadanda suka mutu yawancinsu wadanda suka je kwaso man fetur ne a lokacin da tankar ta yi hatsari kafin fashewar.   Shugabannin Direbobin Tankar Mai na Jihar Neja (PTD) da Kungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Gas ta Nijeriya (NUPENG) ta kasa, Kwamared Farouk Mohammed Kawo, sun tabbatar wa LEADERSHIP faruwar lamarin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai An Ɗage Shari’ar Shugabannin Ƙungiyar Ansaru Zuwa 19 Ga Watan Nuwamba October 21, 2025 Manyan Labarai NLC Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Don Biyan Buƙatun ASUU Da Sauran Ƙungiyoyi  October 21, 2025 Manyan Labarai Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu October 21, 2025
    Kwamitin da Kotun Tsarin Mulki ta Kamaru ta kafa domin sake ƙirga ƙuri’un zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar ranar 12 ga Oktoba, ya miƙa rahotonsa a wannan Talatar. Sakamakon da kwamitin ya gabatar ya nuna cewa shugaban ƙasa mai ci, Paul Biya, ya samu nasara da kashi 53.66 na ƙuri’un da aka kaɗa, yayin da Isa Tchiroma Bakary ya zo na biyu da kashi 35.19. Tinubu ya naɗa sabon Minista Yadda Zanga-zangar Kanu ta ja wa ’yan kasuwa da ma’aikata asara Sai dai ɓangaren jam’iyyar adawa, musamman ta Tchiroma, sun yi watsi da wannan sakamako tun kafin a sanar da shi a hukumance. Alƙaluman kwamitin sun nuna cewa jam’iyyar RDPC ta shugaba Biya ta samu ƙuri’u 2,474,179, yayin da...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka October 20, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar October 20, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan October 20, 2025
    A Yemen Dubban daruruwan mutane ne suka fito titunan birnin Sana’a domin jana’izar babban hafsan hafsan sojin kasar, Laftanar Janar Mohammad Abd al-Karim al-Ghamari, wanda aka ayyana shahadarsa a hare-haren da Isra’ila ta kai a watan Agusta… Taron dai ya nuna matukar hadin kan al’ummar kasar, da suka fito daga sassan babban birnin kasar da larduna daban-daban, tare da manyan jami’an soji da wakilan gwamnati. Jama’a na dauke da hotunan marigayi Janar din, tutocin kasar Yemen, da tutoci masu nuna goyon baya ga gwagwarmayar Falasdinu da kuma yin Allah wadai da harin Amurka da Isra’ila. Tashar Al Mayadeen ta bayar da rahoton cewa, dubun dubatar ‘yan kasar ne suka halarci jana’izar, yana mai nuni da irin yadda jama’a ke girmama...
    Kasashen Iran da Iraki sun bukaci duniya da ta dakatar da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi wa Falasdinawa a Gaza Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da mai baiwa kasar Iraki shawara kan harkokin tsaro Qasim al-Araji sun bukaci kasashen duniya da su dakatar da kisan gillar da gwamnatin Isra’ila ke yi wa Falasdinawa a zirin Gaza. Al-Araji, wanda ke jagorantar wata tawagar jami’an tsaro a kasar Iran, ya gana da Araghchi a yammacin jiya Litinin, inda suka yi musayar ra’ayi da su kan hanyoyin inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, da kuma tattauna halin da ake ciki a Gaza da Lebanon. Dukkan jami’an biyu sun bayyana damuwarsu kan yadda Isra’ila ke ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita bude...
    Kasar Equatorial Guinea, ta zargi Faransa da karan tsaye wa zaman lafiya a kasar. mataimakin shugaban kasar Equatorial Guinea Teodoro Nguema Obiang Mangue ya yi tir da “tsarin Faransa na neman da yunkurin kawo cikas ga zaman lafiya a kasar, . A wani sakon da ya wallafa a shafin X.. Faransa na goyan bayan ‘yan tada zaune tsaye, ta hanyar tunzura su da su kawo cikas ga zaman lafiya, in ji Mataimakin Shugaban kasar a wani lamari da ba a saba gani ba. “Mun yi watsi da manufofin tsattsauran ra’ayi da jamhuriyar Faransa ke bi don tada zaune tsaye a kasarmu, kamar yadda ta yi da sauran kasashen Afirka kamar Mali, Nijar, da Burkina Faso, da dai sauransu. A.” Equatorial...
    Tsohon shugaban kasar Faransa, Nicolas Sarkozy, ya fara zaman gidan yari na shekara biyar a gidan yarin La Santé da ke tsakiyar birnin Paris. An same shi da aikata laifin hada baki wajen samun kudaden yakin neman zabensa na shekarar 2007 daga tsohon shugaban Libiya, Muammar Gaddafi. Sarkozy ya musanta aikata laifin, kuma ya nemi a sake shi daga gidan yari yayin da yake neman daukaka kara. Wannan dai shi ne karo na farko a tarihin jamhuriya ta biyar da wani tsohon shugaban kasar zai kwana a gidan yari. Magoya bayansa sun taru da sanyin safiyar yau a wajen gidansa na Paris. A shafin sa na sada zumunta ya yi wa magoya bayansa alkawarin cewa .gaskiya za ta yi nasara....
    DSS ta gurfanar da su bisa tuhumar laifuka 32 da suka shafi ta’addanci. Usman ya amsa laifi ɗaya kacal na haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, amma ya musanta sauran. Abba kuwa ya ƙi amsa dukkanin laifukan da ake tuhumar sa da su. An zarge su da kai hari sansanin soja na Wawa da ke Jihar Neja, sace mutane, samar da kuɗin ta’addanci, da kuma samun horo a ƙasar Mali daga wata ƙungiyar ta’addanci ta waje. Haka kuma DSS ta ce sun sace jami’in Kwastam da wani jami’in Shige da Fice wanda ya mutu a hannunsu, tare da karɓar kuɗin fansa na miliyoyin Naira daga iyalan waɗanda suka sace kafin a kama su. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai NLC...
      Sinawa kan ce, bisa mataki mataki ake yin tafiya tsawo. Lallai nasarorin da kasar Sin ta cimma, sun faru ne sakamakon yadda al’ummomin kasar suka hada karfi da karfe a karkashin jagorancin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kuma suka yi ta yin kokari ba tare da kasala ba bisa shirye-shiryen raya kasa da gwamnati ta tsara na shekaru biyar biyar. Shirye-shiryen cike suke da burikan da kasar Sin ke neman cimmawa, wadanda kuma suka shaida kokarin da al’ummar kasar suka yi da ma wahalhalun da suka sha. Idan aka fara wani sabon shirin, to, an bude sabon babi na bunkasa kasar ke nan. Ma iya cewa, tarihin shirye-shiryen raya tattalin arziki da zaman al’umma na kasar Sin na shekaru...
    Kwamandan ya ƙara da cewa yayin yaƙin “Operation Zero” na shekarar da ta gabata (Disamban 2024 zuwa Janairun 2025), mutane 432 ne suka mutu, yayin da 2,070 suka jikkata a haɗura 533; adadin ya ragu idan aka kwatanta da na baya. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai NLC Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Don Biyan Buƙatun ASUU Da Sauran Ƙungiyoyi  October 21, 2025 Labarai ’Yansanda Sun Kama Ɗan Fashi Sanye Da Kayan NYSC A Enugu October 21, 2025 Manyan Labarai Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu October 21, 2025
    Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya kaddamar da aikin gina hanyar Babban Sara zuwa Malam Bako zuwa Shabaru zuwa Kirgi zuwa Albasu, mai tsawon kilomita 28.2, a Karamar Hukumar Sule Tankarkar,wanda kudinsa ya kakaNaira Biliyan 4.47, a ci gaba da shirin Gwamnati da Jama’a. Aikin hanyar zai hada fiye da kauyuka 60 tare da karfafa harkokin kasuwanci da zamantakewa a yankin. Haka kuma, gwamnan ya bude sabuwar cibiyar kula da lafiya ta farko, da makarantar Tsangaya ta zamani, da kuma rukunin samar da ruwa a yankin. Gwamna Namadi ya bayyana cewa shirin Gwamnati da Jama’a hanya ce ta karfafa gaskiya, bayyana ayyuka da kuma baiwa jama’a damar fadin  ra’ayoyinsu. “Mun zo ne mu nuna abin da muka...
    Harkokin kasuwanci sun tsaya cik a wasu sassan Abuja sakamakon zanga-zangar neman a saki shugaban ƙungiyar ’yan ta’addan IPOB da ke neman ɓallewa daga Najeriya, Nnamdi Kanu, inda masu ’yan kasuwa da ma’aikata da dama suka yi asarar kuɗaɗen shiga. A yankunan Wuse, Banex da Mararaba, shaguna da kasuwanni da dama sun kasance a rufe saboda fargabar tashin hankali. Wasu ’yan kasuwa da suka gwada buɗe shaguna sun ce babu ciniki. “Na kasa buɗe shagona yau saboda kowa yana tsoron tashin hankali. Ko da ka bude, babu wanda zai fito saye da wannan yanayin tsoro,” in ji Peter Ayuba, mai sayar da na’urorin lantarki a kasuwar Wuse. A Smart Bridge Plaza da Zuma Garden da ke unguwar Utako, yawancin shaguna...
    Wasu direbobi sun bayyana cewa tsarin ya taimaka wajen tabbatar da tsaro, ko da yake  fyana jinkirta tafiya. Wasu kuma sun ce farashin sufuri ya ɗan ƙaru sakamakon sabon tsarin. Mutane da ƙungiyoyin farar hula sun yaba da nasarar, amma sun buƙaci gwamnati ta tabbatar da cewa yaran da aka ceto sun samu kulawa, ilimi, da sake gana su da iyayensu. Dakta Sabo ya ce hukumar sufuri za ta ci gaba da haɗa kai da jami’an tsaro tare da faɗaɗa ayyukanta domin tallafa wa tattalin arziƙin jihar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara October 20, 2025 Manyan Labarai Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Mutane Biyu Da...
    Kakakin fadar Kremlin Dmitry Peskov ya sanar a wannan  Litinin cewa, kasar Rasha a shirye take ta fadada hadin gwiwa da Iran a dukkan bangarori, yana mai cewa, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu tana ci gaba da kara habaka, da kuma  amincewa da juna. Peskov ya yi nuni da cewa, Moscow na goyon bayan ci gaba da shawarwari kan yarjejeniyar shirin nukiliyar Iran, yana mai jaddada cewa, “Matsayar da kasashen turai suka dauka game da batun Shirin ba ta da amfani, kuma hakan  yana kara  dagula lamurra, da kuma kawo cikas ga  duk wani ci gaba na hakika kan wannan batu.” In ji shi. Wannan matsayi na Rasha, na zuwa ne a daidai lokacin da lamurra suke kara rincabewa a...
    Wata kotun majistare da ke Kano ta umarci Hukumar Hisbah ta jihar da ta shirya ɗaura aure tsakanin wasu fitattun ’yan TikTok guda biyu — Idris Mai Wushirya da Basira Yar Guda — cikin kwanaki 60. Kotun ta bayar da wannan umarnin ne bayan yaɗuwar bidiyon Mai Wushirwa da ’Yar Guda a kafafen sada zumunta, da Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano ta bayyana a matsayin “na batsa da rahsin tarbiyya.” Bidiyoyin sun nuna waɗannan ’yan TikTok ɗin suna nuna soyayya a bainar jama’a, abin da hukumomi suka ce ya saɓa da ɗabi’u da koyarwar addini da al’adun mutanen Jihar Kano. A yayin zaman kotun ranar Litinin, Mai Shari’a Halima Wali ta yi gargaɗi cewa idan ba a ɗaura auren...
    Mahdieh Esfandiari, malamar jami’a ba’iraniya tana daga cikin Iraniyawar da za’a yi musayarta a shirin musayar fursinonin tsakanin JMI da Farans a cikin yan kwanaki masu zawa. Tashar talabijib ta Presstv a nan Tehran ta nakalto mataimakin ministan harkokin wajen  kasar Iran Vahid Jalalzadeh yana fadar haka ya kumakara da cewa JMI ta yi amfani da hanyoyin diblomasiyya wandanda sukakai ga musayar fursinonin tsakanin ta da kasar Faransa kuma daga cikin wadanda Faransa zata yi musayar da su har da ita Mahdieh  Esfandiari wacce gwamnatin kasar Faransa ta tsare ta tun watan Maris na wannan shekara saboda ta nuna goyon bayanta a Falasdinawa a shafinta na yanar gizo. Jalalzadeh ya kara da cewa , duk tare da cewa gwamnatin kasar Faransa...
    Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta bada sanarwan cewa a cikin sa’o’ii 24 da suka gabata sojojin HKI sun kai falasdinawa 57 ga shahada, wanda kuma ya kawo adadin wadanda ya kawo yawan wadanda ta kashe tun fara yakin tufanul Aksa zuwa 68,216. Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto majiyar na cewa sojojin yahudawan sun kashe Falasdinawa 45 kai tsaye da makamansu daga sama kasa da kuma ruwa a yankuna daban daban na zirin gaza a yayinda gawaki 12 kuma yana daga cikin wadanda aka zakulo daga burbushin gine-gine. Har’ila yau sun jikata wasu Falasdinawa 158 a cikin wannan lokacin. Ma’aikatar ta kara da cewa har yanzun akwai dubban gawakin Falasdinawa a karkashin gine-ginen da aka rusa...
    Kakakin majalisar dokokin kasar Lebanon Nabih Berri ya bayyana cewa babu kuma wata tattaunawa da HKI, bayan da jakadan Amurka na musamman a kasashen Siriya da Lebanon Thomas Barrach ya isar da sako garesu kan cewa HKI ta ki amincewa da tattaunawa kan ficewarta daga wasu yankunan kasar Leabanon da ta mamaye da kuma shata kan iyakar kasashen biyu. Kakakin majalisar ya fadawa Jaridar Asharqul Awasat a jiya litinin kan cewa ba abinda ya rage a halin yanzu, sai kasashen da suke kula da tsagaita wutan da aka cimma da ita a cikin watan Nuwamban shekara ta 2024 su yi aikinsu. Yace su yi aikinsu na tabbatar da cewa HKI ta mutunta yarjeniyar mai lamba 1107 ta MDD wacce ta...
    A jiya litinin ce masu goyon bayan Nnamdi Kanu shugaban kungiyar neman kafa kasar Biafara (IPOP) daga tarayyar Najeriya, wanda ake tsare da shugaban kungiyar tare da tuhumar ayyukan ta’addan sun fito zanga-zanga suka kuma tushe wata babban titi a Abuja. ‘Yansanda sun jefa masu hayakin teargas don tarwatse su a jiya litinin. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa Kanu wanda yake da Passport na kasar Burtania ya yi kokarin wanke kansa daga tuhumar da ake masa tun 2021 amma ya kasa. Kanu yana jagorantar kungiyar IPOP tun da dadewa, da nufin samar da kasar Biafara a yankin kudu maso gabacin Najeriya. Kafin haka dai yan kabilar Ibo sun yi kokarin bellewa daga tarayyar Najeriya a...
    Wakilin Amurka a kasar Syria Tom Barak ya bayyana a wannan Litinin cewa, shirin shugaban Amurka Donald Trump mai dauke da abubuwa 20 na dakatar da yakin zirin Gaza ya haifar da wani sabon yanayi na siyasa, wanda hakan ya sa batun kulla alaka tsakanin kasashen larabawa da Isra’ila ya kara samun karbuwa fiye da kowane lokaci. Barak ya bayyana a wani sakon da ya wallafa a shafukan sada zumunta cewa, “hanyar samun zaman lafiya a yankin ta bayyana karara duk kuwa da kalubalen da ake fuskanta, musamman dangane da warware matsalar Hamas.” In ji shi. Ya kara da cewa: “Saudiyya na gab da shiga yarjejeniyar kulla alaka da Isra’ila a hukumance, yayin da ta yi hakan, sauran kasashe za...