Aminiya:
2025-12-09@00:17:25 GMT

Gwamnan Bauchi ya naɗa ɗan uwansa a matsayin sabon Sarkin Duguri

Published: 24th, October 2025 GMT

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya naɗa babban ɗan uwansa, Alhaji Adamu Mohammed, a matsayin sabon Sarkin Masarautar Duguri.

Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Aminu Hammayo ne, ya bai wa sabon Sarkin takardar naɗin a madadin gwamnan, a wani biki da aka gudanar a fadar sarkin Duguri, da ke Ƙaramar Hukumar Alkaleri, a ranar Juma’a.

Ƙungiya ta tallafa wa ɗaliban makarantar masu buƙata ta musamman a Gombe ’Yan sanda sun sake kama Sowore bayan kotu ta bayar da belinsa

A yayin bikin, Sakataren Gwamnatin Jihar, ya shawarci sabon Sarkin da ya ci gaba da mara wa manufofi da shirye-shiryen gwamnati baya, domin samar da ci gaba mai ɗorewa a jihar.

A nasa jawabin, sabon Sarkin Duguri, Alhaji Adamu Mohammed, ya gode wa Gwamna Bala Mohammed bisa wannan karamci.

Ya yi wa ɗan uwan nasa addu’ar Allah Ya saka masa da alheri.

Ya kuma yi alƙawarin yin biyayya ga Gwamnatin Jihar Bauchi da kuma Majalisar Masarautar Bauchi.

Hakazalika, Hammayo, ya miƙa wa sabon Sarkin masarautar Bununu, Alhaji Jibrin D. Hassan, takardar naɗinsa.

Ya shawarce shi da ya yi aiki bisa doka da oda, tare da tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin ƙabilu daban-daban a yankinsa.

A nasa martanin, sabon Sarkin Bununu, ya gode wa gwamnan bisa amincewa da shi, tare da tabbatar da cewa ba zai bai wa gwamnati da al’umma abin kunya ba.

Aminiya ta ruwaito yadda Gwamna Bala Mohammed, ya rattaba hannu kan dokar da ta ƙirƙiro sabbin masarautu 13 a Jihar Bauchi.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: masarauta Sabon Sarki sabon Sarkin

এছাড়াও পড়ুন:

Amurka: Mun Yi Kokarin Kifar Da Gwamnatin JMI Har Sau Biyu Ba Tare Da Samun Nasara Ba

Tom Barrack jakadan Amurka na musamman a kasar Siriya ya bayyana cewa gwamnatin kasar Amurka ta yi kokarinkifar da gwamnatin JMI a baya har sau biyu amma ta kasa yin haka.

Tashar talabijin ta Presstva a nan Tehran ta nakalto Barrack yana fadawa wani kamfanin dillancin labaran UAE a ranar jumma’an da ta gabata, ya kuma kara da cewa daga shekara ta 1946 ya zuwa yau gwamnatin Amurka ta yi kokarin kifar da gwamnatoci 93 biyu daga cikinsu a kasar Iran ba tare da samun nasarara ba. Amma akwai da dama wadanda suka sami nasara.

Ya ce kafin Trump ya hawo kan kujerar shugabancin Amurka mun yi kokar kifar da gwamnatin kasar har sau biyu ba tare da samun nasara ba. Barrack dai har’ila yau shi ne jakadan Amurka a kasar turkiyya.

Wannan bayanin yana zuwa ne watanni 6 da yakin kwanaki 12 wanda Amurka da HKI suka kaiwa kasar wato daga ranar 13 ga watan Yuni zuwa 24 ga watan. Inda sukakashe Iraniyawa 1,064 suka kuma kaiwa fararen hula da dama hare-hare.

A cikin yakin ne gwamnatin Amurka ta kai hgare-hare kan cibiyoyin makamashin nukliya na kasar Iran a fordo Naqtanz da kuma Esfahan.

Iran ta sami nasara a wannan yakin ne bayan ta kai hare-hare masu karfi kan HKI da dama, hare-haren dasuka tabbatar da cewa Iran zata iya shafe HKI da yayin ya ci gaba. Haka ma Iran ta kai hare-haren kan sansanon sojojin Amurka mafi girma a gabas ta tsakiya dake Al-udaita na kasar Qatar.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta Gargadi Kasashen Larabawa Dangane Da Tsibiran Kasar Guda Uku A cikin Tekun Farisa December 7, 2025 Hamas Tace Zata Mikawa Gwamnatin Falasdinawa Makamanta Idan An Kawo Karshen Mamaya December 7, 2025 Venezuela: Ba Mu Tsoron Kaudin Amurka Na Wuce Gona Da Iri December 7, 2025 Iran Ta Zama Zakaran  Duniya A Wasan “Taekwondo” Na Masu Shekaru Kasa Da 21 December 7, 2025 Afirka Ta Kudu: An Kashe Mutane 11 A Wani Bude Wuta Na Kan Mai Uwa Da Wabi December 7, 2025  Dubban Mutane Suna Guduwa Daga  Gabashin DRC Saboda Barkewar Sabon Fada December 7, 2025 Mutane Biyar Ne Suka Mutu A Wata Musayar Wuta Tsakanin Sojojin Afghanistan Da Pakistan December 6, 2025 Iran Da Masar Sun yi Kira Da Kawo Karshen Keta Hurumin Gaza da Labanon da Isra’ila ke yi December 6, 2025   Qatar Tayi Gargardi Game Da Gakiyar Yarjejeniyar Gaza Matukar Isra’ila Bata Janye Ba December 6, 2025 Gwamnatin Najeriya Za ta Karbi Sabon Bashin Dala Miliyan 500 A Bankin Raya Kasashen Afrika December 6, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ‘Yan Bindiga 18 Sun Muta a Wata Arangama da Rundunar Operation Fansan Yamma
  • Sojoji sun kashe ’yan bindiga 13, sun ceto ’yan kasuwa a Sakkwato
  • Najeriya: Gwamnatin Tarayya Ta Bada Sanarwan Kubutar Da Yan Makaranta 100 Da Aka Sace
  • Rashin Tsaro: Gwamnatin Tarayya ta gaza — Kwankwaso
  • Sabon Fada Ya Barke A Tsakanin Thailand Da Cambodia
  • Rasha Ta Yi Maraba Da Cire Sunanta A Matsayin ” Barazanar Da Amurka  Teke Fuskanta
  • Amurka: Mun Yi Kokarin Kifar Da Gwamnatin JMI Har Sau Biyu Ba Tare Da Samun Nasara Ba
  •  Dubban Mutane Suna Guduwa Daga  Gabashin DRC Saboda Barkewar Sabon Fada
  • Gwamnatin Najeriya Za ta Karbi Sabon Bashin Dala Miliyan 500 A Bankin Raya Kasashen Afrika
  • Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Jigawa ta Kare Kasafin Kudin 2026 a Gaban Majalisa